MEEMA FAROUK Page 1 to 10

_Manzon Allah ya taɓa ce ma Abu Zarrin, “in Mutum yayi Sallah domin neman yardar Allah, duk zunuban sa za su zube Kamar yadda ganye yake zubewa daga itace,” Abin lura a nan shi ne sallah tana kawar da ƙananan zunubai. Manyan kam sai an tuba. Amma in Allah ya ga dama yana iya yafe sagiran da kaba’iran don sallar da mutum yayi. Amma kuma, ko can ba ayi ma musulmin ƙwarai kallon zai riƙa kuntuka kaba’ir, manyan laifuka. Ban da ma haka duk mai Sallah yakan yi istigfari ne, a ƙarshe ya roƙi Ubangiji ya gafarta masa zunuban sa, manya da ƙanana._
_Abu Sa’id Khudri, Allah ya yarda da shi ya ce, “ya taɓa jin Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi na cewa: “ko wace ɗaya daga cikin sallolin nan biyar tana kankare zunuban da suke tsakanin ta da wadda ta gabace ta.” Bari mu kawo misali da wani wanda aikin sa yake sa yayi butu-butu da ƙura. Akwai ƙoramu guda biyar suna gudana tsakanin gidan sa da inda yake aikin. In ya tashi zuwa gidan yakan yi wanka a kowace ƙorama. To, haka fa sakamakon yin sallolin nan biyar yake. Ana yafe duk wasu kurakurai da zunubai da suke tsakanin salloli biyu saboda istigfari da tuba da ake a kowace sallah._
_Manzon Allah yakan riƙa kawo mana ire-iren misalan nan ne don ya nuna mana irin ƙarfin da sallah take da shi wajen kawar da zunubai. Idan mun yi watsi da jin tausayi na Ubangiji, ba za mu kuka da kowa ba sai kan mu._
_Ba shakka ɗan Adam mai yin kurakurai ne. Muna iya yin ayyuka da dama wa’danda za su saɓa ma Ubangiji, mu kuma gamu da hushin sa da horon sa. Amma kuma mu duba irin jin ƙan da Ubangijin mu yake mamaye mu da shi. Ya nuna mana yadda za mu sadu da rahmar sa da jin ƙan sa. Abin takaici ne ƙwarai a ce mun bari wannan baiwa ta wuce mu, bamu kama ta mun riƙe da hannu bibbiyu ba. Rahmar Allah kusa take ƙwarai ga mai Sallah. Sallah falala ce daga Allah ya zo, ya gusar da abin da yake damun zuciya. Haka aka san Manzon Allah da Sahabban sa suke yi._
_Ɗan Adam yana yin Sallah tun safe har ya zuwa sallar isha’i da fatar dacewa da rahmar Allah. Bayan isha’in mutane sun kasu gida uku. Akwai waɗanda suke su gare su daren hanya ce ta samun lada da tubarraki. Waɗannan su ne masu raba dare suna bautar Allah, lokacin da wasu suke ta shara Barci. Su kam lada suke samu daga Ubangijin su. To, sai kuma mutanen da suke mayar da daren wani kaya mai nauyi da masifa gare su saboda yin ka-ce-na-ce cikin miyagun ayyuka da talatainin dare. Ba abin da daren yake kawo musu sai baƙin ciki. Sai kuma kashi na uku wanda ya ƙunshi masu hayewa gado kawai bayan sun gama isha’i. Su kam ba yabo ba fallasa. Irin su sun kauce wa hadisin Manzon Allah da yake cewa, “ku dimanci yin Sallah a gidajen ku ko baiwar Allah da rahmar Allah su iso gare ku.” Allah yasa mu dace duniya lahira._
*NO_ 5 & 6*
Sanda MEEMA ta farka ta ganta jikin Abee ɗin ta sai ta ɗago kai tana kallon sa
Idanun su ne ya haɗu da juna, ya sakar mata murmushi yana ce mata, “You woke-up?”
Bata iya magana ba illa gyaɗa mishi kai da tayi
Still murmushin ya sake Yi Yana lumshe ido tare da buɗe wa yace da ita, “Okay, go pray and eat. I know you haven’t eaten yet.”
“Ok Abee”. Tayi maganar tana sauka daga kan gadon, sai ta wuce ta shiga Toilet ɗin sa ta ɗauro alwala. Tana fito wa ta duba wardrobe ɗin sa ta cira Hijab, dayake akwai kayan ta a ciki tunda ko yaushe tana ɗakin sa, idan har ba karatu zata yi ba, to, bata cika zuwa ɗakin ta ba, ta fi son zama kusa dashi.
Har ta gama sallan yana kallon ta yana faman murmushi kaɗan
Bayan ta gama dawowa tayi ta zauna gefen gadon tana riƙo hannun sa, “Abee, you are doing to pray?”.
Gyaɗa mata kai yayi makes her smile
“Ok let me Call Nurse”. Tayi maganar tana tashi ta fice.
A Parlour ta tarar da su zaune suna hira, sai ta kalle su fuska ba fara’a tace, “Abee will pray”.
“Ok”. Cewar Nurse Zara tana tashi da sauri tayi ɗakin.
Direct MEEMA Kan dainning ta nufa, sosai take jin yunwa tunda rabon ta da abinci tun wanda suka ci ɗazu da Zamiya ta girka musu, shiyasa sai da ta cika cikin ta sosai kafin ta tashi tayi ɗakin Abee ɗin ta, sai da safe tayi masa sannan ta wuce nata ɗakin
Ta san ko ta kwanta baza ta iya barci ba, shiyasa ta ɗauki school bag ɗin ta ta haye hill chair ɗin da take karatu a kai me haɗe da table, ta soma duba karatun da aka yi musu tana revision, bayan ta gama sai ta ɗauko assignment ɗin da aka basu tun last week, tamkar project ne suna bincike akai, taci gaba da binciken ta cikin ɗan ƙaramin Laptop ɗin ta tana yi tana rubutu. Sai 01:30am da taji barcin yazo mata kafin ta kwanta, babu daɗe wa kuwa ya sure ta cike da mafarkai kala-kala da ta saba yi ko yaushe.
Washe gari zuwa ƙarfe 08:00am. Ta gama shirin ta, kamar yanda ta saba shigan ƙananan kaya sai ta ɗaura Abaya a kai me bottles a gaban, wannan karon Abayan brown color ne sai mayafin shi fari da Flower’s kalan brown, flet shoes ta saka fari sannan ta ɗauki School bag ɗin ta ta rataya a kafaɗa ta fito, a hankali take sauka a kan Steps ɗin har ta dira ƙasa
House girl ɗin su dake gyara parlor’n, ganin ta yasa ta dakata tana gaishe ta
Kallo ɗaya tayi mata ta amsa a taƙaice tana shigewa ɗakin Abee ɗin ta
Nurse Zara da fitowar ta kenan daga Toilet ta gaishe ta cike da fara’a
Kamar kullum ta amsa mata a daƙile tana wuce wa kusa da mahaifin ta, ganin sa yana barci sai ta kalli Nurse Zaran tace, “He still hasn’t woken up?”
“Yes”.
Numfashi taja tana mayar da idanun ta kan shi
While Nurse Zara ita kuma tayi ficewar ta
Sai da ta shafa fuskar sa zuciyar ta na cike da damuwa, kafin kuma ta tashi ta fice, yau bata tsaya breakfast ba tayi ficewar ta, motan ta ta hau ta wuce school.
Lokacin da ta shiga class su Ummu Hani duk sun zo, yau har da Zamiya saboda jikin nata da sauƙi. Suna cikin gaisawa ne Malamin su ya shigo, sai suka nutsu suka mayar da hankalin su kan darasin da yake musu.
Sun sami break lokacin suna duba karatun su sai wayan MEEMA tayi ƙara, ɗauka tayi ta duba sai taga sunan Ishaq ne, tsaki taja ta ajiye tana ci gaba da duba book ɗin dake hannun ta
Esha Sarkin shaƙiyanci dariya ta saki tana kallon ta tare da ɗage mata gira tace, “Is that Ishaq?”
Ɗago kai MEEMA tayi tana hararan ta bata ce komi ba ta sake ɗauke kai daga kallon ta
Sai tace, “Please go if he is, don’t get tired of waiting for you, you know his condition is persistent”.
Sai duk suka saki dariya har Eshan da tayi maganar
While MEEMA ta sake kicin-kicin da fuska still taƙi magana
Sun san halin ta shiyasa suka yi gum da bakin su suka ci gaba da karatun su
A lokacin ne kiran nashi ya sake shigo mata, bata sake bi ta kai ba har sanda yayi mata three Miss calls, ganin ya dame ta sai ta ɗauki wayan a daƙile tana amsa mishi sallaman nashi
Sanar mata yayi, “he came outside where they used to meet”.
Sai ta tashi kawai ta fice
Su kuma sai suka koma hira memakon karatun da suke yi, har wasu daga cikin mate ɗin nasu suka zauna cikin su ana yi da su.
********
MEEMA da fitar ta Direct inda zata ganshi ta nufa, tana zuwa ta hange shi a cikin rumfar da yawancin ɗalibai suke zuwa su zauna don shaƙatawa, babban rumfa ne da kujeru a wajen da aka jera su gunun sha’awa da tables ɗin su