MEEMA FAROUK Page 1 to 10

Ƙarisawa tayi taja kujera ta zauna bayan tayi sallama a ciki-ciki
Shi kuma tuni ya mayar da idon sa kanta yana faman doka mata murmushi tare da amsa mata sallaman yana cewa, “My Baby”.
Kallon sa tayi tana ɗan sakin fuska kaɗan tace, “how far?”
“I’m not Fine Baby”.
Ɗan ɗage gira tayi tana kallon sa alamun tambaya
Sai yayi murmushi kana yace, “Have a drinks before we start talking”. Yayi maganar yana nuna mata drinks ɗin wajen
“Laa. shukran”.
“Baby you can not drink?”
Gyaɗa masa kai kawai tayi
Sai yaja numfashi yace, “We should stop talking now. I want to send to your house to have a wedding day,”
Ƙura masa ido tayi har ya dira aya, sai ta fuske tare da kini-kini da fuska tace, “Ishaq now there is no word between us, I can tell you now I will not marry”.
“Why MEEMA? Why do you want to humiliate my life?”
“No. I will not humiliate your life, I will not marry if Abee is in his condition, I will never marry until he is fine”.
“Ok, baby, I agree to marry you, so bring him to my home and take care of him.”
“No Ishaq”. Sai ta tashi tsaye tana kallon shi tace, “please don’t come out to me again, i will never get married now”. Ta juya tayi wuceWar ta
Yana kiran ta amma ko juyo wa bata yi ba.
Sanda ta koma class sai su Ummu Hani duk suka tambaye ta ganin ta dawo da wuri
But bata ce komi ba ta zauna taci gaba da karatun ta
Su ma ganin bata tanka su ba sai duk suka fita harkanta domin sun saba da halin ta yanzu, so hakan ba ya basu haushi tunda sun san ba haka take ba a baya.
Three O’Clock yau suka gama lectures, suka yi sallama da juna
Esha said, “MEEMA dropped her off at home because she didn’t bring her own car today.”
Shiyasa suka tafi tare, dayake duk wajen anguwan su ɗaya ne, sai da ta sauke ta kafin ta ƙarisa gida, tana sauka ta rufe motan ta taka tayi ciki a gajiye, tana shiga da sallama
Me aikin su ta amsa mata tana mata sannu da zuwa
Da kai ta amsa mata kafin ta wuce ɗakin Abee
Shi kaɗai ne a ɗakin idanun shi a lumshe, sallaman ta ne yasa ya buɗe idon yana kallon ta da yalwataccen murmushi a kyakykyawar fuskar sa na asalin bafulatani, wadda ta ƙara zabge wa tayi siriri da ita tsaban zaman jinya
“Abee”. Tafaɗa sanda ta zauna a gefen gadon tana riƙo mishi hannu
“Ummy”. Shima ya faɗa still yana mata murmushi, sai kuma yace, “uridu an ata haddas”. (“ina son muyi magana ne”.)
“Ok Abee, lakin jasadak sahl?” (amma jikin ka da sauƙi ko?”)
“Na’am Ummy alhmadulillah. Al’aàn karajal mahaàmil kassi biî wa natahaddasa ma’ahu”. (“Yanzu Lauya na ya fita mun yi magana dashi”.)
“Abee maàzaà hadasa?” (“Me ya faru?”)
Sai da yaja numfashi daƙyar kafin yace, “Ummy, nothing, but now I have decided to return everything to you.”
“Why?” Tafaɗa da wani irin murya me kama da son kuka
Murmushi yayi yace, “nothing Daughter. I am not comfortable with the arrival of my brothers. That is why I have made this decision. I want everything to return to your name so that you can own it or after my life is yours. I own everything for you.”
Kuka ta fashe da shi tana sake damƙe hannun shi, cikin kukan take cewa, “No Abee, You will be cured by God’s will, nothing will happen to you ok?” Sai ta ɗaura kanta kuma a jikin shi taci gaba da kuka, domin ji take yi kamar wani abu ne zai sami Abee ɗin nata, don me zai mata irin wannan zancen? Me kuma yasa zai yanke wannan hukuncin?
Shafa kanta yake yi cike da rarrashi yana ce mata, “enough”. Daƙyar ya samu tayi shiru sannan yace mata, “She went to rest”.
Tashi tayi ta fita, kai tsaye ɗakin ta ta wuce ta kwanta ta hau faman tunanin da ya zame mata jiki, ga shi yanzu lokaci na ta ƙure mata karatun su ya zo ƙarshe, amma kuma ba ta iya yin karatun sosai sabida hankalin ta ba a kwance yake ba. Lumshe idanuwan ta tayi hawayen ciki na sake zubo mata a kunci, ta jima a haka kafin ta tashi ta shiga tayi wanka ta sauya kaya ta gabatar da sallah, sannan ta wuce downstairs ta zauna a kan dainning ta soma cin abinci, gaba ɗaya a tunani ta gama yi kafin ta wuce ta koma ɗakin Abee ɗin ta
Lokacin yayi barci
Sai ta haye kan gadon ta kwanta a gefen shi tana ta faman kallon shi, babu abinda ke dawo mata sai rayuwar su na baya sanda suke tsananin farin ciki, amma ƙaddara ta zo ta ɗauke musu wannan jin daɗin, sanadiyar haka Ummeen ta ta tafi ta bar su, bata san har yaushe za su kasance a haka ba, duk da ta yarda da ƙaddara kuma ta san komi zai wuce, komi zai koma musu dai-dai kamar baya, tana fatan hakan a koda yaushe, shi ne burin ta Mahaifin ta ya samu lafiya hakan ne kaɗai zai dawo da daidaiton walwala a tsakanin su
Idanun ta ta rufe da suke tsiyayar da hawaye wanda ko kaɗan ba sa gajiya, tana jin zuciyar ta na sake ƙunci a duk sakonnin da zata tuna da mahaifiyar ta.
Ta jima a haka kafin ta buɗe rinannun idanuwan ta a kan fuskar Abee ɗin ta, kallon sa kawai take yi kamar wanda bata taɓa ganin sa ba, ko kaɗan ta kasa ƙifta idanu a kan sa, Every second his sympathy deepened into her heart, numfashi taja kafin ta kai fuskar ta dai-dai nasa she kissed him on the forehead and then pressed him to his lips, sannan ta tashi ta fito. Direct waje ta nufa, a hankali take taka wa hannayen ta soke a ɗan guntun jeans trouser ɗin da ta sanya, while fuskar ta babu alamun walwala a cikin ta, gaba ɗaya damuwa ne ya sake mamaye ɗan kyakykyawar cuty face ɗin nata, duk da hakan be hana fito da zallan kyawun ta ba, domin ta kasance kyakykyawa ce MEEMA, bata da bambanci da mahaifin ta sak shi, a kallon farko idan kayi mata zaka tantance ita ɗin asalin bafulatana ce domin zaka yi tunanin ma tana jin yaren, nan kuwa bata iya komi ba a ciki, daga turanci sai larabci shi ne abinda ta iya, sai kuma kaɗan-kaɗan tana jin yaren talegu kasancewar Zamiya na koya musu, asalin ta ƴar India ce ta zo nan Riyadh karatu shi ne take zaune a Hostel.
Babu inda ta tsaya sai wajen swimming pool ɗin da ke mamaye a bayan gidan, wanda yake cikin ɗan ƙaramin garden me ban sha’awa da birge wa, Everything is green and very beautiful. Tana tsaye ta kafe idanunta waje ɗaya hannayen ta a ƙirji, sosai ta faɗa duniyar tunani, tunanin da ta saba a koda yaushe, bata san cewa hawaye na tsiyaya a kuncin ta ba har sanda taji muryan ƴar aikin su kusa da ita, sai tayi firgigit ta dawo cikin hayyacin ta tana juyo da kallon ta gare ta
“Afwan ya Sayyadaty! Anti gariîb fiî intizaàraki”. “(Kiyi haƙuri Madam! Kin yi baƙo yana jiran ki)”.
Gyaɗa mata kai kawai tayi
Ita kuma ta tafi
Numfashi ta ja tana saka bayan hannun ta ta share hawayen fuskar ta kafin ta taka tabi bayan ta a hankali cikin tafiyan ta na salo.
????????????
*MEEMA FAROUK*
????????????
*NA_NAFISA ISMA’IL*
*WATTPAD_UMMUDAHIRAH*
*PERFECT WRITER’S ASSOCIATION* ????
“`( WE AIN’T PERFECT, BUT WE’RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS????)“`
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._
*NO_7&8*
Da shigan ta cikin parlour’n su ta sauke idanun ta a kan Ishaq dake zaune yana shan drink a cikin Glass Cup. Da kallon mamaki kawai take bin sa tana tako wa a hankali