MEEMA FAROUK Page 1 to 10

Shi kuma ganin ta yasa ya ajiye Cup ɗin saman Centre table yana me miƙe wa tsaye tare da yalwata fuskar sa da murmushi, ƙyam ya ajiye idanun sa a kanta ya kasa ɗauke wa illa bin ta da yake yi da wani irin kallo me wuyan fassara
Ita kuma ganin haka yasa ta sake tamke fuskar ta bayan ta ƙariso wajen sa idanun ta a kan sa tace, “What are you going to do in our house? What brought you here? ”
Sai da yayi murmushi yana shafa suman kansa kafin yace, “Oh Baby, you know there is no way I can get rid of you so easily. Please, I have come to talk to you.”
Naman goshin ta ta tattare waje ɗaya tana me runtse idanu, sai kuma ta ware su a kansa murya a hassale tace, “What do you want from me?”
“I want to get married MEEMA, I love you so much I can’t divorce you. Please accept my request. I may die if I don’t marry you.” Sai kuma ya duƙa ya saka gwiwowin sa a ƙasa tare da haɗe hannayen sa waje ɗaya yace, “please help Me MEEMA I can’t live without you, I love you so much! I may lose my life for you”.
Sosai a wannan karon ta fusata da kalaman sa, meyasa ba ya gane wa ne yake son takura mata a rayuwa? Lokaci ɗaya ta daka masa tsawa da faɗin, “I also do not love you Ishaq, go out in my life and leave my life alone, I will never marry you and then leave this house Now”. Ta ƙare maganar da nuna masa hanya, “I say Out”.
Tashi yayi tsaye yana bin ta da kallo, har gaban ta ya tako still idanun sa a kanta. Kallon kallo kawai suke yi ido cikin ido na tsawon daƙiƙu ba tare da ko wannen su ya ɗauke ba, sai ya ci je leɓe yana me ɗauke kansa a kanta ya sauke a ƙasa, hannun sa ya saka na dama ya sosa goshin sa kafin ya sake duban ta kana kuma ya taka ya bar parlour’n
Har ya fice tana tsaye a wajen ta kasa motsin kirki, zuciyar ta sosai take tafarfasa wanda ita kanta bata san dalili ba, sai kawai ta juya tayi kan Steps da gudun ta ta shige ɗakin ta tare da faɗa wa kan gadon ta, wani irin kuka me tsuma rai ta saki wanda har jijjiga gadon take yi tsaban kuka, da hannun ta take tattaro zanin gadon tana yamutsa wa still tana ci gaba da kukan ta me tsuma rai wanda ke fito wa daga can ƙasan zuciyan ta. Sai da ta ɗauki like two minutes kafin ta shanye kukan a lokaci ɗaya tana me tashi zaune, hannayen ta ta saka ta soma share hawayen duk da wasu suna sake kwaranyowa, “I will not cry again. From today on, I promise. From today on I will remove you from my life Ishaq. I will never marry.” Sai kuma ta sake fashe wa da wani sabon kukan, cikin kukan take cewa, “I love You Ishaq, i really Love you, you are the only one i ever wanted you are still in my soul, i will never forget you, i love you, i hope one day we will get married, I’m sorry ok?” Sai ta lumshe idanun ta tana me jan numfarfashi, a haka har ta kafar da hawayen ta kafin ta buɗe idanun ta da suka yi jazur suka kumbura, tashi tayi ta wuce Toilet ta wanke fuskar kafin ta fito ta zauna a kan table ɗin karatun ta, School Bag ɗin ta dake saman table ɗin ta janyo tare da buɗe wa ta zaro Text book ta soma karatu, duk da zuciyar ta babu daɗi amma haka ta daure tana ta karatun domin sama ma kanta nutsuwa, ta san idan ta biye wa damuwar ta zata iya rasa chance ɗin ta, dole ne a wannan gaɓar ta mayar da hankalin ta a kan karatun ta.
Shiyasa tun daga ranan ta hana zuciyar ta sukuni bare ta bata damar yin wani tunani me zurfi, kullum tana cikin karatu ko da tana wajen Abee ɗin ta ne da books ɗin ta take zuwa, bata da lokacin kanta a yanzu saboda ganin time ɗin exams ɗin su ya gabato, idan tayi wasa zata iya Field.
Da sannu da sannu ga shi har time yayi sun soma zana jarabawan su, wanda shi ne na ƙarshe sun haɗa degree ɗin su a fannin Mascom.
Gefe ɗaya kuma bata sake ganin Ishaq ya zo wurin ta ba, ko me kama da shi bata sake gani ba, duk da a wani ɓangare na zuciyar ta tana matuƙar kewan sa amma babu yanda zata yi, hakan ma ya fi mata shi zai bata daman nutsuwa ta manta komi, duk da ta san da cewa cire soyayyar sa a zuciyarta gaba ɗaya ba ƙaramin jan aiki bane a gare ta, ada sun so juna matuƙa ita da shi wanda basu yi tunanin ƙaddara zata zo ta raba su ba, First love yana da matuƙar wahala a zuciyar ɗan Adam, haka MEEMA take ji a yanzu, sai dai ƙauna da tausayin Mahaifin ta ya sa ta jure duk wani baƙin ciki da ƙuncin dake zuciyar ta, ta rabu da shi a kan rayuwa da mahaifin ta na har abada, wannan hukuncin ta yanke shi ne ba tare da tunanin me zai je ya dawo ba.
Alhmadulillah komi aka ce yana da farko kuma yana da ƙarshe, kamar yau ne su MEEMA suka soma zana jarabawan su sai ga shi har sun kammala. Inda makarantan tasu ta shirya musu gagarumin waliman yaye ɗalibai
Sun shirya taron ne a ranan Saturday, inda aka gayyato manya-manyan ƙusoshi na ƙasar Riyadh ɗin, kama daga kan ƴan siyasa da masu kuɗi har da ƴan maƙotan ƙasan duk sun hallara, wanda dama an saba yin babban taron nan a duk shekara.
Mahaifin MEEMA na gaban talabijin kamar yanda ya buƙata a kunna masa don ganin taron waliman ɗiyar sa mafi soyuwa a birnin zuciyar sa.
Bazan iya misalta muku tsantsan kyawun da MEEMA tayi a wannan lokacin ba, duk da ko kaɗan fuskar ta babu walwala bare kwalliya, but tayi kyau sosai kasancewar ta me kwarjini ga duk wanda ya kalle ta, kyawun ta shi ke hana a gane tayi murmushi ko bata yi ba, domin ko ya tayi a hakan kyau take ma Mutane, tana zaune ne a sahun gaba-gaba kasancewar tana ɗaya daga cikin manya-manyan Ɗalibai, tayi shiga irin na larabawa babu abun da ake gani nata sai kyakykyawar fuskarta da tafukan hannayen ta. Inda a lokacin aka sanar ana buƙatar *MEEMA FAROUK* ta fito tayi jawabin buɗe taro. A cikin sanyin ta da tafiyan ta me matuƙar birge wa wanda kamar ba taka ƙasan take yi ba ta isa ga mumbarin tare da amsan speakern ta soma buɗe taro da addu’a cikin harshen larabci, wanda tsaban ƙwarewan ta da iya Yaren zaka yi tunanin ita ɗin asalin Balarabiya ce. Bayan ta ida addu’an ne ta juya harshe zuwa Turanci domin kowa ya ji, kasancewar ba kowa ne ke iya jin larabcin ba, godiya da ban girma tayi ma malaman makarantan tare da baƙin wajen, kana ta koma ta zauna
While mutanen wajen sai tafi suke mata.
Daga nan aka soma gudanar da abubuwan da ya tara su har zuwa kan kyaututtuka da ɗalibai haziƙai suka samu. MEEMA na ɗaya daga cikin waɗanda suke amsar kyaututtuka masu yawan gaske, kowa sai jinjina mata yake yi sabida yanda aka nuna hazaƙan ta
Yayinda Abee na kwance a ɗakin sa yana kallon komi yana hawaye, da ace lafiyan sa lau da ya fi kowa nuna murnan sa ga ɗiyan sa a wannan ranan, tabbas da a yanzu ya kasance a wurin tare da ɗiyar sa yana Alfaharin kasancewan sa uba a wajen ta, sai dai babu hali, but duk da haka babu wanda ya kai sa murna ɗin, tsaban murna har kuka yayi
Itama tana can tana share nata hawayen tuna mahaifin ta da tayi, tabbas da yanzu yana tare da ita suna farin ciki tare, tuna hakan ne ya saka ta zubar da hawaye, ko babu komi tana matuƙar kewan mahaifin ta a irin wannan yanayin, ta tuna sanda ta gama secondary School ɗin ta irin farin cikin da ya nuna sakamakon kasancewar ta gwarzuwa a shekaran, Allah ya yi MEEMA me ƙaunar karatu ne sosai shiyasa zai yi wuya ace ba ita ce ta wuce ko wani ɗalibi a class ɗin su ba, idan kuwa bata zo na farko ba dole a na biyu zata zo. Ta tuna sanda ta gama karatun ta before ta ɗaura Degree ɗin ta, irin Big partyn da ya shirya mata da irin celebrate ɗin da suka yi, amma kuma wannan karon babu ko ɗaya, babu damar da zai shirya mata partyn da zai kasance abinda baza ta taɓa manta wa da shi ba.