MEEMA FAROUK 1-END

MEEMA FAROUK Page 1 to 10

           Lumshe idanuwan ta kawai tayi a sanda ta kawo nan a tunanin ta, yayinda hawayen ciki suka zubo a saman dandamalin fuskar ta

Su Esha suka rungume ta suna me taya ta kukan kasancewar sun san lokacin rabuwan su ne yayi, duk da suna gari ɗaya amma kuma rayuwan school daban ne, Zamiya ce kaɗai ta fi shiga tashin hankali tunda ita tazaran su da yawa, sake haɗuwan su zai yi wuya, shiyasa take kuka sosai

Yayinda suka haɗu suka rungume ta suna me sake fashe wa da wani sabon kukan.

              Sanda za su rabu kamar kar su rabu, amma babu hali haka kowa ya wuce tare da ƴan uwan sa, while MEEMA ita kaɗai ta nufi gida, a lokacin kuka sosai take yi tunawa da Ummeen ta da kuma Abee ɗin ta dake kwance a can gida babu halin fito wa. Bata iya fitowa a motan ba sanda tayi parcking a cikin haraban gidan, sai ta kifa kanta a saman sitiyarin ɗin tana ci gaba da tsiyayar da hawaye, ta jima a haka ko motsi ta gaza yi before ta ɗago fuskar ta da yayi jawur idanun suka sake kumbura, handkerchief ta saka ta share fuskar tare da daidaita ta kafin ta buɗe motan ta fito hannun ta rike da wayan ta da keey ɗin mota kaɗai domin baza ta iya ɗauko kyaututtukan ba dole ta bar su a cikin mota tayi cikin gidan.

              Babu kowa a parlour’n sai ta wuce kanta tsaye ɗakin Abee

Yana kwance kamar ko yaushe, sai dai yanzu an rigada an kashe masa t.v’n idanun sa a lumshe suke. Muryan ta da ya ji yasa ya buɗe idanun yana sauke wa a kanta, yalwataccen murmushi ya sakar mata yana mata alama da ido a kan, “tazo gare shi”.

Da sauri ta iso tana me duƙa wa a gaban gadon tare da sanya hannayen ta biyu ta riƙo nashi duka, da raunanniyar fuska take kallon shi kamar wacce zata saki kuka

Sai ya janye hannun sa ɗaya ya shafa kanta still Yana murmushi yace, “Alfu mabruùkin ya Ummy, Baárakil lahu fií hayaátiki, jazaákumul lahu aksara min zaliki watamjudniy”. (“ina taya ki murna Ummy, Allah yayi ma rayuwar ki albarka, Allah yasa ki fi haka ya ɗaukaka min ke”.)

“Amin Abee”. Tafaɗa tana me kwantar da kanta saman ƙirjin sa zuciyar ta na farin cikin addu’ar da yayi mata wanda har sai da hawaye suka watso a saman kuncin ta

Shafa kanta kawai yake yi yana murmushi ba tare da ya sake cewa komi ba. Sun ɗau lokaci a haka kafin ya kira sunan ta, “Ummy”.

“Na’am Abee”. Ta amsa mishi ba tare da ta ɗago ba

“Al’aán ba’ada an tahaƙƙaƙu hilmaki fiì tusbiha suhfiìyan, kana haáza hilmaki daá’iman, al’aàn ba’adi inyihaá’i baƙiìyatiz zawaáj, uriduki an tatazauji hatta yahda’a ƙalbiì fiì kulli marrati azhaba fiìhaá ilal firaásh, uriduki an tahdira khaɗììbaki watatawaƙƙafu anil tahaddas ila waálidihi”. (“Yanzu burin ki ya cika kin zama Ƴar jarida, mafarkin ki kenan a koda yaushe. Yanzu saura aure ya rage zaki yi, ina son inga kin Yi aure domin zuciya ta zata fi kwanciya a duk sanda na tafi na barki, ina son ki fito da wanda zaki aura mu tsayar da magana da iyayen shi”.)

Saurin ɗago da kai tayi tana kallon sa, nan da nan hawayen ta suka ci gaba da kwaranya, cikin amon muryan ta dake fita da rawa tace, “Laá Abee, la astaɗiìu an atazauja wa’azhaba wa’aƙuùla wadaá’an, laá yumkinuniìl zahaábu li’aƙuùla wadaá’an fiì haálatil mardi haázihi, laƙad saámahtu zawaáji Abee, lan atazauja hatta tatahassana”. (“A’a Abee. Bazan aure in tafi in barka ba, bazan iya tafiya in barka a wannan halin na rashin lafiya ba, na yafe aure Abee, bazan yi aure ba har sai sanda ka samu lafiya”.) Sai kuma ta fashe da sabon kuka tana me riƙo hannun sa sosai tace, “Abee Ummee… She’s going.. and…” harshen ta kawai ke motsi ta gaza furta abin da take son furta wa saboda yanda wani abu me ƙunci ya tokare mata maƙogwaro

Shima Abee tuni ya soma zubar da hawaye, ya saka hannu ya kwantar mata da kanta a saman jikin sa yana rarrashin ta, “Aásifa”. Kawai yake iya furta wa shima a laɓɓan sa zuciyar sa na masa ƙuna, shi kaɗai ya san me yake ji a wannan lokacin daure wa kawai yake yi

A haka suka kasance har barci ya ɗauki MEEMA a wurin

Numfashi yaja yana me lumshe idanuwan sa, jikin sa rawa yake masa ga azaban zafi da yake ji, gaba ɗaya yau ba ya jin daɗin jikin sa, daure wa kawai yake yi saboda yau ranan murna ce ga Ɗiyar sa, ba ya son ko kaɗan ya ya ɓata mata wannan ranan me muhimmanci.

            Nurse Zara ce ta shigo tace masa, “time to take his medicine”. Haka ta ba shi maganin ta fice

Dayake akwai na barci sai ya samu barcin ya sure sa.

           Sanda MEEMA ta farka ana kiran magriba ne, ganin Abee na barci sai ta miƙe ta wuce ɗakin ta, sallah ta gabatar kafin tayi wanka ta shirya cikin kayan barcin ta, riga da wando masu ruwan Powder and dressed less, ta sauko ƙasa ta zauna a kan dainning, sosai take jin yunwa shiyasa taci abincin da yawa, ta miƙe ta nufi ɗakin Abee

Har a lokacin be tashi ba domin a time ɗin jikin sa ya yi zafi zau, shiyasa Nurse Zara take gasa mishi jikin a time ɗin domin ta shafa masa magani

Da kallo MEEMA take bin ta dashi tana sake tamke fuska, ko sannun da tayi mata bata amsa ba sai ta jeho mata tambayar, “He hasn’t gotten up yet?”

“Yes, he don’t get up”.

Tsaya wa tayi kawai a wurin tana naɗe hannayen ta a ƙirji ta kafe su da idanu, bata jirga a wajen ba har sanda Nurse Zara ta gama duk abinda zata yi masa kafin ta fice, sai ta taka a hankali ta isa bakin gadon ta zauna, hannu tasa a hankali ta kamo nashi tana tamke wa a cikin nata, shiru tayi tana bin sa da kallo zuciyar ta a raunane, sai kuma ta matsa setting kanshi ta saka hannu tana shafa mishi gashin kanshi, nan taji kamar da zafi jikin sa, taɓa wuyan sa tayi taji da ɗumi sosai, lokaci ɗaya ta lumshe idanu hawaye na saukar mata a fuska, sai ta buɗe tana bin shi da kallo tana tamke bakin ta don hana bayyanuwar kukan da ya taho mata. Kanta ta ɗaura a ƙirjin sa ta ƙanƙame shi. A haka ta kwana a jikin sa ko runtsa wa bata iya yi ba

Ko sanda Nurse Zara ta dawo duba sa a cikin daren, ganin ta yasa ta koma taje tayi barcin ta tunda ta san tana tare da shi.

             Sai asuba MEEMA ta tashi ta koma ɗakin ta, lokacin barci sosai ne a idanun ta sakamakon kwana da tayi bata runtsa ba, sallah tayi ta nema wa Abee ɗin ta sauƙi a wurin Allah, kafin ta haye kan gado barci ya sure ta. 

               Sai 12:30pm. Ta farka, da mafarkin mahaifin ta ta tashi shiyasa duk jikin ta ya mutu, bata iya taɓuka komi ba ta fito ta sauka ƙasa don duba lafiyan sa, tana shirin shiga Likitan sa dake zuwa duba sa ya fito daga ɗakin, hakan yasa gaban ta ya faɗi ta nufe sa da sauri kamar zata faɗa kansa idanun ta ware a kansa tace, “Doctor what’s happened?”.

???????????? 

*MEEMA FAROUK*

                   ????????????

*NA_NAFISA ISMA’IL*

*WATTPAD_UMMUDAHIRAH*

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT*????????‍

*PERFECT WRITER’S ASSOCIATION* ????

“`( WE AIN’T PERFECT, BUT WE’RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS????)“`

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*

              *SADAUKARWA*

_Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._

                 *NO_9 & 10*

               Sai da ya gyara wa eyeglasses ɗin sa zama kafin yace, “calm down please let me explain”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button