MEEMA FAROUK Page 11 to 20

Kafin ya kai har ta fito da sauri tana faɗin, “lafiya Sajjad wannan wani irin kiran mafarauta kake min? Me ya faru ne?”
“Umma wace ce wannan? A ina kuka samo ta?”
Sai da ta bi inda yake nuna mata da kallo ta hangi MEEMA a zaune har ta soma haɗa tea ko kallon inda suke bata yi ba, sai ta ja tsaki don ta manta da ita a gidan sai yanzu da ta ganta, tace dashi, “jiya ta zo ai lokacin kayi barci, yarinyan Uncle ɗin ku ne na Riyadh”.
“What..! You mean Zulaiha ce wannan?” Yafaɗa yana sake nuna inda MEEMAN take a zaune
“Eh ita ce. Ka bari idan Abban ku ya dawo sai yayi maka bayani Ni yanzu ina aiki”. Tafaɗa tana juya wa ciki ta bar sa a wurin
Shi kuma juya wa yayi ya isa inda MEEMAN take
Sai da ya ja kujera ya zauna kafin ta ɗago tana kallon sa da manyan idanuwan ta
Washe baki yayi yana bata hannu yace, “Hi Zulaiha I’m Sajjad your brother”.
Sai ta bi hannun nasa da kallo tana tsayar da taunan bread ɗin da take yi
Murmushi ya sake yi yana tura mata hannun yace, “I’m your brother fa? I was so surprised to see you here, I never thought of that, are you so good. The truth you very beautiful. ”
Miƙe wa kawai tayi ta juya ta bar wurin
Shi kuma sai ya saki baki yana bin ta da kallo kamar zai zubar da yawu, har wani lanɗe baki yake yi. “Wow gaskiya tana da kyau. Wai dama haka take yarinyan? Amma gaskiya an cuce Ni da ba’a nuna min ita ba sai yanzu. Wow.. wow”. Yake ta faɗi yana shafa ƙeyan sa, sai kuma ya tashi ya wuce ɗakin Umman nasa, ya same ta tana gyaran gado sai ya zauna a kan drowan gadon yana cewa, “Umma wlh yarinyan kyakykyawa ce sosai har kama take yi dani, amma a nan gidan zata zauna ko?”
Ɗago wa tayi tana hararan sa kafin tace, “Ni fa Sajjad ka rabu da Ni da wannan halin naka, ka kiyaye Ni wlh”.
“Haba Common Momcy yawa ne, ki share kawai Ni fa yarinyan ta shiga raina ne wlh, I like her so much, kuma kin ga ƙanwa ta ce wani abu ne idan nayi tambaya game da ita?”
“To ka je ka tambaye ta mana ina ruwa na a ciki?”
“To ai Umma ta ƙi kula Ni ne, yarinyan tana da matuƙar class ta haɗu Allah fa ina gaya miki”.
“Hohoho Sajjad baza ka rabu da Ni ba ko?”
“Sorry Momcycy na rabu dake.” Ya faɗa yana tashi tsaye tare da sara mata, sai kuma ya matso kusa da ita yana cewa, “but Umma Ina Murjana sai in tambaye ta?”
“Ta je school”.
Ɓata fuska yayi sai kuma ya juya ya fice. Har ya zauna a kan kujeran Parlour’n yana ta kallon ɗakin Murjanan, sai kuma ya tashi ya wuce ɗakin ya tura ƙofa ya shige
MEEMA dake ƙoƙarin cire rigan jikin ta zata ɗaura tawul ta shiga wanka, sai ganin sa kawai tayi a tsakiyar ɗakin, ƙara ta saka lokaci ɗaya ta ja rigan tayi sama da shi
Shi kuwa daskare wa yayi a wurin tsaban ganin kyakykyawar halittan ta da yayi, idanun sa kawai suke motsi a kanta
A lokacin da gudu Umma ta shigo ɗakin tana tambayar, “lafiya?” Saboda ihun da MEEMAN tayi har ɗakin ta. A kan Sajjad ɗin ta sauke ido sai kuma ta kalli MEEMAN, “ke lafiya mene ne?”
Ita dai tana tsaye ta maƙure a jikin bango tana kallon su don bata san me tace ba
Sai Umman ta ja tsaki tana cewa, “wannan ai shashanci ne kawai ki zo kina cika mana gida da ƙara. Kai kuma uban me kayi mata ne da zata fasa min dodon kunne?”
Daƙyar yake iya sauke numfashi, sai da ya ɗan ja fasali kamar ya dawo a cikin hayyacin sa kafin yace, “Babu Umma. Shigo wa ta kenan nima”.
Dogon tsaki ta ja tana juya wa kawai ta fice
Shi kuma sai ya mayar da idanun sa kan ta kafin ya taka izuwa wurin ta
Hakan yasa tayi saurin haye wa gadon tana sake ware idanuwan ta kamar za su faɗo ƙasa a kansa, hannayen ta kuma suna a kan ƙirjin ta sai sake matse su take yi tana ƙanƙame jikin ta. Ganin da tayi ya ƙi dakata wa daga inda yake yana neman hayo wa gadon cikin ruɗe wa tace, “what are you doing here? Please get out.”
Dariya ya saki yana ci je leɓe, sai kuma ya saka hannu zai riƙo ta yace, “Common Babe nayi zaton ke wayayyiya ce, ki riƙa abu kamar na classics big Girls mana, just I will hugg you because I really Love you”.
????????????
*MEEMA FAROUK*
????????????
*NA_NAFISA ISMA’IL*
*WATTPAD_UMMUDAHIRAH*
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT* ????????
*PERFECT WRITER’S ASSOCIATION* ????
“`( WE AIN’T PERFECT, BUT WE’RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS????)“`
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._
*NO_13*
Da sauri ta sauka daga kan gadon ganin da tayi ya kusa taɓa ta. Fuskar ta babu walwala cikin ruɗu da tashin hankali tace, “what will you do for me? What is my connection with you? Please get rid of Me.”
Tsaya wa yayi yana kallon ta domin yanda ta buɗe baki ala dole tana masifa sosai ta sake burge sa, ji yake yi kamar ya je ya rungume ta ya tsotse mata bakin da ya fi ɗauke masa hankali, sai kawai ya shafa kansa yana killer smile yace, “Babe I love you so much, I am so impressed by everything you do. Please I want us to be friends…”
“No I don’t want to. I said go out”. Ta katse sa a cikin tsawa
“Ok, calm down. I’ll be out.” Sai ya juya yayi bakin ƙofa har yana waigen ta, yana zuwa dai-dai bakin ƙofan ya dakata yana juya wa sosai ya kafe ta da ido yana haɗiyar yawu, har da wani lanɗe baki sai faman shafa kansa yake yi wanda alamu ya nuna ɗabi’an sa ne hakan. Ya ja wani soconni a wurin kafin ya juya ya fice
Wani irin ajiyan zuciya ta sauke har tana dafe ƙirjin ta ta zauna a bakin gadon, sosai zuciyar ta ke gudu kamar zata faso ƙirjin ta tsaban tsoro, a haƙiƙanin gaskiya ta tsorata da shi sosai domin abun da be taɓa faruwa da ita bane. Zumbur ta tashi kamar ta tuna da wani abu ta nufi ƙofa ta murza keey sannan ta dawo ta sake zama. Ta daɗe a wurin tana faman saƙa da warwara a ranta kafin ta tashi jiki a saɓule ta ci gaba da zame kayan nata, sannan ta ɗaura tawol ta shiga Toilet, wanka tayi ta fito ta wuce bakin dressing mirror, tsaya wa tayi kawai tana kallon kanta a mirror har a lokacin fuskar ta babu wani ɗigon walwala, ƙare wa kanta kallo take ta yi har na tsawon lokaci kafin ta ja numfashi tana wuce wa wajen Trolly ɗin ta ta buɗe, kayan da zata saka ta ɗauko, sannan ta ciro cream lotions ɗin ta da take amfani da su ta shafa ta mayar, ta saka kayan riga da skert masu tsananin kyau, rigan me ruwan madara ne me taushi sosai tana da zane-zane a jiki wanda sai ka kula da kyau zaka iya hango wa kasancewar da kalan ruwan madaran aka yi, gajeren hannu ne da ita sai kwalliya da aka yi da zare dack brown color da kuma milk ɗin, sai skert ɗin sa Robber brown color da ta sanya har wajen cikin ta, sai ta ɗaura belt ɗin sa Shima Brown but light, gyara gashin ta tayi ta kama da ribom, bata saka komi a kanta ba ta ɗauki computern Abee da nata ta haye kan gadon, buɗe wa tayi ta soma aiki akai.
Abun da Sajjad yayi mata shiyasa ko kaɗan ba ta sha’awar sake fita, shiyasa tayi zaman ta a nan tana ta faman aiki a computer, sai da aka kira sallan azahar kafin ta tashi ta gabatar sannan ta sake zama ta ci gaba har sanda Murjana ta dawo ta hau buga mata ƙofa. Da sauri ta rufe computern ta mayar a cikin Trolly ɗin ta sannan ta wuce ta buɗe mata. Su biyu ta gani a bakin ƙofan ita da wata sa’ar Murjanan har kayan school ɗin su iri ɗaya ne