MEEMA FAROUK 1-END

MEEMA FAROUK Page 11 to 20

Ita Murjana tsaki ta banka tana hararan ta ta wuce ciki

While ita kuma ɗayan washe baki tayi tsaban farin ciki kawai ta rungume MEEMA, sai kuma ta sake ta tana faɗin, “Oyoyo sister. Ni ƴar uwan ki ce suna na Habibah, Habibah Zubairu, 

I am your uncle Zubairu’s daughter, I am happy to see you”. Ta ƙare maganar tana bata hannu

MEEMA bata gama fahimtan maganar nata ba sabida kasancewar ta haɗa da Hausa, amma sai ta miƙa mata hannu itama tana ƙirƙirar murmushi tace, “me too”.

Shigowa ɗakin Habiban tayi tana riƙo hannun MEEMAN ta ja ta suka zauna a kan gado tace, “yanzu da zamu dawo school Murjana take sanar min da zuwan ki, shi ne nace bari in zo in ganki”.

MEEMA kallon ta kawai take yi, sai kuma ta murmusa tace, “sorry i don’t understand, what did you say?”

“Oh don’t you understand Hausa?” Habiban tayi magana tana ware idanu da mamaki

Still MEEMA tana murmushi ta gyaɗa mata kai

“Ok sorry I don’t know, but do you want to teach you our language?”

Shiru MEEMAN tayi bata iya ce mata komi ba

Sai ita kuma tayi murmushi tana riƙo hannun ta ta haɗa da nata kafin tace, “I will pass our Part, I will come back to see you later, because even in my soul I like you”.

“I like you too”. Tafaɗa itama sosai a wannan lokacin tana murmusa wa

Tashi tayi Habiban ta ɗaga mata hannu ta fice

Da kallo ta bi bayan ta har ta ɓace wa ganin ta, a ranta sosai ta ji sanyi haɗuwar ta da Habiba zata samu wacce za suna magana ba kamar Murjana da ko kallon ta ba ta yi, ko magana ta ƙi yin mata

Yanzu ma tuni ta fice a ɗakin tunda ta sauya kaya. Tana fita parlor Sajjad ya tare ta da maganar MEEMA, shi ne abin ya bata haushi ta ja tsaki tana cewa, “wai Yaya meye haɗin ka da ita ne da kake son sanin wani abu a kanta? Gaskiya yarinyan bata yi min ba bcoz tana da jijji da kai, ko don ta ga tana da kyau ne?”.

Dungure mata kai yayi yace, “kina dai baƙin ciki ne bayan haka meye a jikin ta da zaki ce bata miki ba? Ni kuma ina son ta”.

Tura baki tayi ta wuce ta zauna a saman dainning ta soma haɗa lunch

Sai ya biyo ta yana cewa, “Common Sister ki sanar dani abun da na tambaye ki kinji? Haba My sister”.

Sai da ta taɓe baki kafin tace, “Wai Mahaifin ta ne ya rasu shi ne ta zo nan”.

“Wow da gaske?” Yafaɗa yana buga tsalle

Da kallo ta bi sa kafin tace, “lafiya Yaya meye na murnan?”

“Uhmm daɗi nake ji sosai a raina, kenan ta dawo nan da zama? Kin ga shikenan zan same ta”.

“Wai kana nufin da gaske son ta kake Yi?”

“Sosai ma. Kuma auren ta zan yi domin dai-dai kala ta ce ita, macen da nake fatan samu kenan, Abba na dawo wa zan sanar mishi ayi-ayi a aura min ita”.

Dariya Murjana tayi tace, “daga ganin Sarkin fawa sai miya tayi zaƙi Yaya? Tab ɗijim zan ga inda draman nan zata ƙare, akwai kallo a gidan nan wlh”. Ta ƙare maganar tana sake fashe wa da dariya

“Ke fa baki da kunya na lura, amma bari in je in dawo kafin Abba ya dawo zaki ga me zan yi”. Ya tashi ya fice

Ita kuma sai dariya take yi, daƙyar ta dakatar da shi ta soma cin abincin.

              A lokacin ne MEEMA ta fito ta nufi wajen dainning ɗin

Da kallo Murjana take bin ta har ta ƙariso ta ja kujera ta zauna. Sai ta ja tsaki tana ɗauke kai ta ci gaba da cin abincin nata

Ita kuma MEEMA kallo ɗaya tayi mata itama ta cire nata idanun a kanta ta soma serving kanta. Duk da tana jin yunwa but daƙyar ta iya yin spoon uku ta ture abincin, hannu ta sanya ta janyo Flaks ɗin dake wurin ta zuba ruwan Lipton ɗin a cikin Cup, ganin babu kayan haɗa tea ɗin a wurin sai ta ɗauka haka nan ta soma sha ko sigar babu a ciki

Murjana dake kallon ta ta ƙasan ido sai ta taɓe baki a fili ta furta, “sanabe gai da uwar miji a kasuwa. Zaki saki ciki ki riƙa cin abinci ne tunda nan ba can bane, ƴar wahala”.

Dayake MEEMAN ba jin ta take yi ba shiyasa ko ɗago wa bata yi ba bare ta kalle ta, har ta kurɓe ruwan lipton ɗin ta tashi zata koma ɗaki

A time ɗin ne Habiba ta shigo ita da Inna Mahaifiyar ta, dayake itama ta shigo domin ta ga MEEMAN ce tunda Kawu Zubairu ya sanar mata

“Yauwa Inna kin ganta”. Cewar Habibah cikin farin ciki tana me ƙarisa wa kusa da MEEMAN ta riƙe mata hannu. Sai kuma ta juya ga MEEMA tana ce mata, “she’s her mother”.

Hakan yasa ta ɗan saki fuska tana gaishe ta

Inna kuwa sai ƙare wa MEEMAN kallo take yi tana faman yamutsa fuska da taɓe baki, domin itama irin waɗannan jarababbun matan nan ne, don har ta fi Umma iya shege

Sai da Habiba tace mata, “Inna gaishe ki fa take Yi?”

“To Ina na sani tunda ba iya Yaren nayi ba?”. Sai kuma ta ja tsaki ta wuce tana tambayar Murjana, “Ina Umman ta?” Hango ta da tayi zaune a saman dainning

“Tana ɗaki”. Ta bata amsa a taƙaice

Hakan yasa ta wuce ciki

Habiba itama tuni ta bi MEEMA cikin ɗaki.

             Inna na shiga ɗakin Umma ta ganta zaune tace, “ashe kina ciki na shigo ban gan ki ba?”

“Eh ina ciki Halima. Aiki na gama kuma na zauna ban fita ba”.

Inna zama tayi a gefen ta kafin suka gaisa kana tace, “Wai Jamila haka zaki zauna da yarinyan nan a gidan ki. Me ya kai ki amsar ta?”

“Wace yarinyar?” Umma ta tambaya tana kallon ta

“Wannan Yarinyan mana na wajen Faruku”.

“Ohh wlh Ni manta wa nake yi da ita a gidan, to ya na iya tunda ba dauwama zata yi ba, su ma su Abban Sajjad ɗin ai suna shirin koran ta ne bayan komi ya dawo hannun su”.

“Ai gwara haka don wlh bata da wurin zama a wannan gidan haka kawai, Ni kinga Habibah ne ma naga tana wani murna da zuwan ta, Ni fa bazan lamun ta hakan ba wlh sai in saɓa mata”.

Umma tace, “ai Ni dayake Murjana babu ruwan ta kinga ko shiga safgarta bata yi ba”.

“Na san maganin Habiban ai, bari in je wanki nake yi na taso”. Cewar Innar tana tashi tsaye

Itama Umman tashi tayi ta bi bayan ta suka fita Parlour suna sake zantawa

Innar ta tambayi Murjana dake zaune a kan sofa a yanzu tana latsa waya, “Ina Habiban?”

“Ta bi wancan yarinyan ciki”. Tayi maganar cikin taɓe baki

“Habiba.. Habiba”. Inna ta ɗaga murya tana kiran ta

Da sauri ta fito tana faɗin, “Inna gani nan fa ba nisa nayi ba”.

Hararan ta tayi tana cewa, “ai na san ba nisan kika yi ba, uban me kike yi a wurin ta?”

“Inna babu komi fa muna hira ne tunda..”

Katse ta tayi tana faɗin, “dalla rufe min baki, idan baki yi wasa ba wlh zan saɓa miki a gidan nan, ina ruwan ki da ita daga zuwan ta zaki fara maƙale mata?”

“Inna ƴar uwa ta ce fa”. Tafaɗa tana zaro idanu

“Eh ƴar uwan taki, ba na son alaƙar ku nace, wuce mu je dalla”.

Habiba cike da rashin jin daɗin abun da uwar nata tayi mata haka ta bi bayan ta suka fice

“Nima fa wlh yarinyan ba burge Ni tayi ba Umma, idan ba ma zubar da kai ba na Habibah daga zuwan ta ta wani fara maƙale mata, da can suna son mu ne da zata zo mana gida?”

“Nima abun da na gani kenan, ki barta ai mu ma ba dauwama zata yi mana a nan ba, can ta wuce dangin uwar ta ba dai nan ba, don bazan riƙe ɗan riƙo ba wlh”.

“To Umma amma fa bazai yiwu ta zauna a haka kullum ki girka ki bata ba babu abinda zata rika yi ƙatuwar budurwa kamar ta, nan ba gidan su bane dole ta riƙa yin aikin gida ko nima zan huta wlh, kinga tunda na fita ke baki gyara parlor’n nan ba ita kuma bata zo tayi miki ba.”

Umma tace, “to dama ai na barta ta ɗan kwana biyu ne kafin ta soma mana aiki, wlh ƴar aiki aka kawo mana don bazai yiwu ta ci ta sha a gidan nan ba ta luƙume a ɗaki, ki bar ta zuwa gobe komi na gidan nan dole tayi shi, wannan sanƙamemiyar budurwan da a yanzu tana gidan miji ina zan iya da ita?”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button