MEEMA FAROUK Page 11 to 20

******
MEEMA dake zaune a ɗaki duk maganar da suke yi a kunnen ta ne tun fitan Habibah, sai dai bata fahimci ko eh ba a ciki, tayi jiran ko Habiba zata dawo amma shiru shiyasa ta kwanta tana ɗaukan wayan ta ta soma latsa wa
Murjana ce ta shigo ɗakin ta ganta a haka, ta ɗauke kai tana wani ciccin magani ta wuce ta shiga Toilet. Bata jima ba ta fito tana kallon MEEMAN tace, “ke dalla tashi ki fita zan gyara ɗaki na tunda baki san ki gyara min ba”.
Idanu ta zuba mata tana mamakin yadda take hararan ta tana mata tsawa a kai. Shiru kawai tayi tana sake ƙare wa Murjanan kallo, ko a girme zata bata good 5years ko fiye da haka..
“Keee! Ko ba kya ji ne ki tashi nace ko gadon uban ki ya siya min ne?” A wannan karon ma Murjanan tayi maganar a fusace tana ɗaga murya
Tashi zaune MEEMA tayi tana kallon ta sosai kafin tace, “what do you say I don’t hear you?”
“Uban ki nace banza kawai. I said get up and go out”.
Ɗauke kai tayi daga kallon ta tana me ɗaukar wayan ta ba tare da ta furta komi ba ta tashi ta fice a ɗakin.. Kai tsaye Parlour ta koma ta zauna tana ɗaura kanta a saman kujeran ta lumshe idanuwan ta
Sajjad ne ya buɗe ƙofan ya shigo yana rera waƙa ear phone a kunnen sa. Idanuwan sa suna sauka a kanta yayi saurin zare ear phone ɗin yana bin ta da kallo kamar zai haɗiye ta tsaban kallo while zuciyar sa cike da farin cikin ganin ta
Ita kuwa tuni ta ɗago tun sanda ta ji muryan nasa itama tana kallon sa, sai dai ta sake haɗe rai kamar bata taɓa dariya ba.
????????????
*MEEMA FAROUK*
????????????
*NA_NAFISA ISMA’IL*
*WATTPAD_UMMUDAHIRAH*
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT* ????????
*PERFECT WRITER’S ASSOCIATION* ????
“`( WE AIN’T PERFECT, BUT WE’RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS????)“`
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._
*NO_14*
Ɗauke kai tayi a kansa ganin ya taho wurin ta. Sosai ƙirjin ta ke luguden buga wa saboda tsoron sa amma ko kaɗan bata nuna a fuska ba
Har ya zo ya zauna gefen ta yana wani faman shafa kai da kafa mata idanu kamar wanda zai cinye ta. Cikin sanyin murya yace, “Babe why don’t you want to take care of Me? I am your brother and I love you so much.”
Ɗago Kai tayi ta kalle sa, sai dai bata ce komi ba ta sake ɗauke kai a kansa
Numfashi ya ja kafin yace, “ok I’m so sorry for what I did to you, I forgot I did not greet your dead father, sorry God bless his grandson”.
Still dai shiru tayi
Sai shima ɗin yayi shiru kawai yana kallon ta
Abba ne ya shigo gidan da sallama a bakin sa
Sajjad ya amsa mishi yana kallon sa, sai kuma ya miƙe ya nufe sa yana hugg ɗin sa tare da cewa, “Oyoyo Dadyyyy”.
“My son ya kake?” Abban yafaɗa yana shafa kansa cikin fara’a
“I’m fine Abba, sai dai i miss You so Much”.
Dariya yayi yana bugan kafaɗan sa da cewa, “Oh my son baza ka dena halin ka ba”.
Cikin shagwaɓa yace, “Allah Dadyyyy da gaske nake yi fa”.
Idanu MEEMA ta zuba musu tana faman kallon su, sai kawai Abee ɗin ta ya faɗo mata a rai, lumshe idanu tayi tana me buɗe su a lokaci ɗaya tare da son komar da hawayen da suka taru mata a cikin ido. Mayar da kallon ta tayi a kansu da har sun ƙariso wurin, sai ta tashi cikin girmamawa tace, “Welcome Dad”.
Yaƙe yayi Kawu Ali yana kallon ta yace, “Ah Zulaiha you are here?”
“Na’am Dad”.
“Okay we have something to talk about, but then your uncle comes and we will discuss”.
“Nima Abba akwai maganar da zamu yi da kai gaskiya”.
“Ok my son, ai ko wani time lokacin ka ne faɗa mu ji”.
Sai da ya bubbuga ƙafafu kafin ya kalli MEEMA da ta saki baki a wannan lokacin tana kallon sa, ya nuna ta da yatsa da cewa, “Abba Gaskiya na kamu da son ta, I really love her Ina son ka aura min ita”.
“Whattt.. Sajjad what are you saying?”
“Ina son in aure ta”. Ya sake maimaita wa yana tura baki
Umma da ta fito daga ɗaki a yanzu ɗin tace, “uban wa zaka aura ba dai wannan yarinyan ba Sajjad? Kana da hankali kuwa?”
“Yes Umma ina da hankali na, Ni dai kawai ita nake so ku aura min ita wlh, idan ba haka ba zan mutu”. Ya ƙare maganar da dafe ƙirjin sa yana wani narke fuska
“Ai kuwa sai dai ka mutu wlh, ka dena tunanin ma maganar ka zai yiwu, koda yake babu wanda be san halin ka ba”.
“Umma wlh da gaske nake yi ina son ta da aure ne”. Yayi maganar yana ƙarisa wa wajen ta da riƙo hannayen ta
“Dalla sake Ni banza kawai, meye abun so a nan?”
“Abba baka ce komi ba kana jin ta ko?” Yayi maganar cikin buga ƙafafu
“Nima me zance Sajjad? Shirmen ka yana da yawa kai kam, Ni yanzu na dawo a gajiye ka bari na huta”. Ya ƙare maganar yana wuce wa ɗakin sa
Itama MEEMA tuni ta koma ta zauna tana ta kallon su kamar ta sami t.v, sai dai ko kaɗan bata fahimci inda zancen nasu ya nufa ba illa mamakin abun da Sajjad ɗin yake yi kamar wani yaro. Tana kallon yanda yake ta bin Umman har cikin kichen yana mata shagwaɓa
Murjana da ta fito yanzu bin bayan su tayi tana cewa, “wai umma wa ya taɓo Yaya ne yake ta mammanne miki?”
“Wai maganar wancan yarinyan yake min auren ta zai yi”.
Dariya Murjana ta kwashe da shi tana cewa, “ai akwai kallon drema kenan a gidan nan, nima haka yace min ɗazu abun da bazai taɓa yiwuwa bane.”
Biyo ta yayi yana faɗin, “ina wasa dake?”
Da sauri ta gudu suka soma zagaye kichen ɗin suna zagaye Umma dake tsaye a tsakiyar kichen ɗin
Sai faɗi take yi, “zaku ka dani fa”.
Amma ba su ji ta ba sai guje-guje suke yi, daga ƙarshe Parlour suka wuce suka ci gaba da yi
Lokacin MEEMA bata a parlour’n ta koma ɗaki
Ƙarshe dai ɗakin Abba suka je a can ya raba su faɗan, domin haka suka saba tunda sun zama kamar yara an sangarta su sai abun da suke so suke yi a gidan, sun tashi babu kwaɓa ko kaɗan, ba ma kamar Sajjad da yake ɗan fari, dayake sanda aka haife shi sai da ya jima domin har sun ɗauke tsammanin sake haihuwa, sai kuma daga baya aka haifi Murjana.
Yanzu haka Kawu Zubairu shi kuma yana da yara uku ne, dayake tare suka yi aure da Kawu Ali, Ɗiyar sa ta farko me sunan mahaifiyar su Jammatu suna kiran ta Ummi tayi aure har da yara uku don ita ce sa’ar Sajjad, sai kuma Amina itama tayi aure da yaron ta ɗaya da cikin na biyu, ko MEEMA ta girmi Amina, sannan sai Habibah sa’ar Murjana, yanzu suna S.S 3 ne zangon ƙarshe.
✳️✳️✳️
Da aka yi sallan isha’i sai Kawu Ali suka shigo sashin shi da Kawu Zubairu. Sajjad na biye da su a baya
Umma ta kawo musu abinci tana cewa, “yau a nan zaka mana hira kenan?”
Dariya Kawu Zubairun yayi yace, “a’a yanzun nan zan tafi ai, maganar dai Zulaiha ce muke so muyi yanzu, ina take? Ki kira mana ita don Allah”.
“To”. Tace tana juya wa ta wuce ɗakin Murjana
Shi kuma Sajjad dake hakimce a saman kujera yana latsa waya da sauri ya ɗago yace, “Abba to nima ayi maganar mu da ita, wlh da gaske nake yi ina son ta ku aura min ita”.
“Wace ce yake so ne?” Kawu Zubairu yake tambaya
“Wai Zulaiha yake so, idan ba shirmen Sajjad ba ina shi ina yarinyan nan bayan ya san yanda muke da uban ta ƴar tsaman dake tsakanin mu, ai bazai yiwu ma ya kawo ta a matsayin surukata ba wlh, yarinyar da ta gama ɓalɓancewan ta kusan sa’ar shi me zai yi da ita?”.