MEEMA FAROUK Page 11 to 20

Kawu Zubairu yace, “Yaya ni ina da shawaran da zan bayar a game da wannan zancen”.
A lokacin Umma da MEEMA suka ƙariso wajen
Sai Kawu Zubairun yace, “to Sajjad bamu wuri zamu tattauna, kuma kar ka damu idan Zulaiha ce zaka aure ta”.
“Da gaske Uncle?” Yafaɗa cike da murna
“Ƙwarai kuwa, bari zamu yi magana da Abban naka”.
“To Uncle. Na gode sosai”. Ya tashi yana murna, idanun sa a kan MEEMA da ta samu wuri ta zauna bata ce komi ba, killer smile ya saki yana faman ci je baki kafin ya wuce.
Ita Umma itama tuni ta wuce cikin nata ɗakin, dama wanka zata yi ta tsaya ajiye musu abinci tunda sun shigo tare
“Wai Zubairu me kake nufi wani shawaran ne zaka bayar? Ba dai a kan auren nasu ba don bazai taɓa yiwuwa ba”.
“Haba Yaya ka kwantar da hankalin ka mana, Ni ina ga wannan ma yana a cikin tsarin mu idan har hanyar da zamu ɓullo be yiwu ba, to kamata yayi ta auri Sajjad idan ya so ko nan gaba sai mu raba ta da komi ya zama mallakin mu, tana ji tana gani kuma bata da yadda zata yi damu tunda a lokacin mun fi ƙarfin ta, tana ƙarƙashin mu dole Sajjad zai san yanda zai yi ya sauya komi da sunan mu. In yaso ma ko ƙara zata kai mu gaba sai mu iya raba ta da duniyar ma”.
Waro ido Kawu Ali yayi
“Ah to abu me sauƙi, kai kana ganin yarinyan nan ba matsala zata zame mana ba?”
Jinjina kai yayi yace, “haka ne kam. Amma yanzu mu fara gwada ta mu gani.” Sai ya juya da kallon sa ga MEEMA dake zaune still tana ta faman kallon su kamar wacce take fahimtar maganar nasu, nan kuwa ko eh bata fahimta ba illa bakunan su da take ta ƙare wa kallo. “Zulaiha, this is what we called you about your father’s assets, you know it is not possible for us as your father’s relatives to leave you with these huge sums of money, even if you say that your father owned everything for you before he died then you must We have a share in the property, but now it is not a matter of what we want to do. You can bring everything so that we can turn it over to you. You feel that we are not advising you. It is an order that you will give us everything to hold in our hands.”
MEEMA da ta tsare sa da idanu tana sauraron sa har ya dire, Bata manta su waye su ba kuma bata manta dalilin da yasa Abee ɗin ta ya mayar da komi nashi da sunan ta ba, dole yanzun ma akwai abin da suke nufi shiyasa ta gyara zaman ta tana cewa, “Uncle’s be patient with what I’m talking about, I’ve already decided what to do with my money, and Abee’s companies are selling them all, and I can keep the documents of his house in my hand. I do not need your help…”
Wani irin fusata Kawu Ali yayi saboda zancen nata
Zai yi magana sai Kawu Zubairu ya dakatar da shi da cewa, “don Allah Yaya ka ƙyale ta, dama nace maka wannan yarinyan shegiya ce mahaifin ta ya rigada ya koya mata yanda zata yi tun kafin ya rasu, kana tunanin bata san manufar mu bane? Ka barta kawai yanzu mu bi ta a sannu idan muka nuna fin ƙarfi zamu iya rasa komi wlh, kuma ka san ba yanda zamu yi mu amshi komi sai da saka hannun ta, takardun filayen kuma ta ce ya mayar da sunan ta ka ga bazai mana amfani ba ko mun ƙwata da ƙarfi”.
“Haka ne. Amma yanzu ya kake so mu yi? Yanzu kana nufin Mu zuba mata ido da zunzurutun kuɗaɗen nan? Wlh bazai yiwu ba”. Kawu Ali yace hakan cikin jin haushi yana sharce zufa
“Lallaɓa ta zamu yi mu jawo ta a jiki hakan zai saka ta saki jiki damu, na san zata bamu komi domin mu riƙa juya mata tunda dai ba ita zata kula da wannan dukiyan ba”. Sai ya kuma juya wa ya kalli inda MEEMAN take cikin turanci yace, “Zulaiha tunda mu a matsayin mu na Iyayen ki kin ƙi aminta damu kin nuna bamu isa dake ba, shikenan ki ci gaba da riƙe kuɗin idan wani abun ya same ki babu ruwan mu, kin yarda?”
Gyaɗa kanta tayi
“Ok get and go”.
Tashi tayi kuwa ta wuce ɗaki
“Gaskiya wannan abun be min daɗi ba, yanzu haka zamu zuba idanu sai kace yarinyan ta fi ƙarfin mu?”
Kawu Zubairu yace, “Kai yaya ka cika saurin hawa ne, to ya zamu yi kuwa wlh baza mu iya amsar komi ba bare kaf ƙadarorin sa suna wani ƙasa ne, ka ga kuwa ba abu bane me sauƙi ya dawo hannun mu ba, idan baka iya kama ɓarawo ba shi sai ya kama ka, shawaran dai da zamu bi mu haɗa su aure da Sajjad ko tana so ko ba ta so”.
“Kana ganin hakan zai fi?”
“Eh mana hakan zamu yi. Idan ta zama matar sa komi zai fi zuwan mana a hannu babu yanda za’a yi ta tafi tunda da auren ta, shima Sajjad ɗin dole mu sanar masa da komi domin ya san shirin mu, in yaso daga ƙarshe mu raba su ko ya ƙi ko ya so idan mun gama da ita, kana gani fa juya mata dukiyar zamu yi amma ta ƙi amincewa, wannan yarinyan halin su ɗaya da uban ta wlh dole sai mun bi a sannu Ni dai Yaya ina faɗa maka, auren su babu fashi zamu tsayar da time a ɗan ƙanƙanin lokaci, sannan baza mu sanar mata ba har sai a ranan bikin idan an ɗaura, ka ga ba yanda zata yi”.
Kawu Ali sosai ya amince da wannan shawaran da ya bayar, sai da suka sake tattauna wa sosai kafin ya tafi
A lokacin su Umma har sun gaji sun fito suna kan dainning suna cin abincin su
“Sajjad kira matar taka mana ku ci abincin, ya naga bata fito ba?”
“Wow Abba ka amince zan aure ta?”
Murmushi yayi yace, “My son kenan, ka taɓa ganin kun nemi abu kun rasa ne? Ai da yardan Allah Zulaiha matar ka ce, sai dai ban ce ka sanar mata ba har sai an ɗaura auren naku, zamu tsayar da lokaci nan ba da jima wa ba don haka sai ka shirya zama ango nan kusa”.
Ihu ya saki tsaban murna ya rungume Umma ya haɗa da Murjana ya matse su yana ci gaba da murna
“Kai wai lafiyan ka ƙalau kuwa? Dalla sake Ni”. Inji Umma tana ɓanɓare shi, sai kuma ta dubi Abban tace, “wai me kake cewa? Ni fa gaskiya ban amince ya auri yarinyan nan ba, haba Abban Sajjad kai ne kuma da faɗan hakan bayan kai zaka fi kowa ƙin auren?”
“Jamila zo ki zauna ki zuba min abincin nan, idan muka gama sai muyi magana in fahimtar da ke.”
Bata ce komi ba dai ta taso ta nufi inda yake ta soma zuba masa abincin
Shi kuma Sajjad tuni ya wuce da sauri ya burma ɗakin Murjana don kiran MEEMA, har wani tsalle yake yi tsaban farin ciki.
_Rashin Comments zai saka baza ku riƙa samu kullum ba, ba sai na riƙa maimaita muku ba duk sanda ku kaga new update shikenan._
????????????
*MEEMA FAROUK*
????????????
*NA_NAFISA ISMA’IL*
*WATTPAD_UMMUDAHIRAH*
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT* ????????
*PERFECT WRITER’S ASSOCIATION* ????
“`( WE AIN’T PERFECT, BUT WE’RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS????)“`
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._
*KAN MATSALAR KASANCEWA A TSAYE ANA SALLAH*
_Rahamar Allah tana isowa, mun samo labarin wani shahararren mai kawo hadisai da ake kira Abu Ishak Subaihi wanda ya rasu yana da shekara ɗari. A kan ji shi yana cewa, “Kash! Wannan rauni na zurfin shekaru ya hana mini more ma doguwar sallah. Yanzu a raka’o’ina biyu Baƙara da Al-imrana kaɗai nake iya karantawa.” Su kuwa surorin nan biyu sun kai kamar ɗaya bisa takwas na Alƙur’anin gaba ɗayan su._
_Shi kuwa Hafiz Ibni Ƙayyam yayi nazarin irin fa’idojin da ake samu daga sallah ne ya jero su da cewa, “sallah tana tabbatar mana da samun abincin yau da kullum, ta kawo lafiya, ta kore cututtuka, ta ƙarfafa zuciya gami da faranta ta, ta kawo haske ga fuska, ta sabunta jiki, ta kawar da lalaci, ta haskaka zuciya, ta daɗaɗa ta, ta rage mata jin nauyi kana ta yiwa mutum albishir da rahmar Allah. Tana kasancewa garkuwa ga azabar Allah, tana tsare mu daga shaiɗan ta kuma kusanta mu da Ubangiji. A taƙaice dai; sallah lamuni ne na duk wani abin so kuma garkuwa ce ga duk wani abin ƙi na zuci ko na jiki a wannan duniya ko lahira.” Allah yasa mu gama da duniya lafiya Amin ya Allah._