MEEMA FAROUK 1-END

MEEMA FAROUK Page 11 to 20

                            *NO_15*

            Yana shiga ya hange ta kwance a saman gadon tana latsa waya

Bata san da zuwan nasa ba sai da ya zo har gaban ta yana shirin amshe wayan sai tayi saurin firgita tana shirin ƙwalla ƙara

Shi kuma ya sanya hannu ya kama bakin nata ya rufe ruf yana dariya

Tuni ta yar da wayan tana shirin ƙwace kanta, nan da nan ta ƙwalalo idanu waje domin a tunanin ta wani abun zai mata ta soma Shure-shure zata ƙwace kanta

Saurin matse ta gam yayi a jikin sa yana raɗa mata a kunne, “Shiiiiiii! Calm down! I have nothing to do with you.”

Amma ina bata saurare sa ba sai son ƙwace kanta take Yi tana son buɗe bakin ta da ya ɓame mata ɓam

While Iya ƙarfin sa ya riƙe ta ya ƙi saki, musamman yanda ya ji skin ɗin ta kamar ya tamke mage sabida tsaban taushi da yake dashi, har wani santsi yake yi, hakan ya ja hankalin sa da jin wani irin feelings ya sake manna ta a jikin sa yana shinshina mata fuska

Nan da nan ta soma kokuwa da shi iya ƙarfin ta har hawaye sun soma wanke mata fuska tsaban yanda ta tsorata ainun

To ƙarfin su ba ɗaya ba sosai ya sanya mata ƙarfin sa ya mayar da ita kan gadon ya danne ta yana cewa, “Babe there is nothing I can do for you, I say calm down ok?”

Sai numfashi take sauke wa sabida yanda tagalabaita a ɗan kokawan nan da tayi, because kasancewar ta ƴar hutu bata saba wahala ba shiyasa abu kaɗan a wurin ta aiki ne, idanuwan ta kuwa kamar za su fito waje tsaban zaro su da tayi

Killer smile ya saki yana sake matse ta sosai har ƙirjin su yana haɗe wa, a hankali ya kai fuskar sa saman nata fuskar yana son kissing ɗin ta a forehead still yana liƙe da bakin ta gudun kar tayi masa ihu. Muryan Abban sa ya ji yana kiran sunan sa. Dalilin da ya sanya ya dakata yana me kallon cikin idanun ta in a cool voice yace, “Babe I’m sorry I didn’t do this to spoil you, i love You so Much I will not do it again ok?”

Kallon sa kawai take yi idanuwan ta suna zubar da ƙwalla ko ƙyafta su ta kasa

A hankali ya janye hannun nasa still idanun sa cikin nata

Har ya janye bata sake motsa wa ba illa numfashi da take ta faman sauke wa akai-akai, tana ganin ya sauka daga jikin ta tayi saurin tashi da gudu zata shige Toilet

Hannun ta ya riƙe gam yana cewa, “Where are you going again?”

“Please let me go, I do not want to”. Tafaɗa tana hawaye tana son ɓanɓare hannun nasa

“Ok, I’ll let you go, but let’s go and eat.”

“No I’m not hungry”. Ta sake faɗa tana ƙwaƙule hannun sa da ƙarfi

Be ce komi ba ya riƙe ta ya janyo ta suka fice

Da kallo su Abba suka bi su baki sake

“Kai lafiya me kayi mata Son? Meye haka?”

“Abba babu komi wlh, ta ƙi zuwa ne shi ne na janyo ta”. Yafaɗa yana isa har wajen dainning ɗin ya ja mata kujera yace, “sit please”.

MEEMA dake faman zubar da hawaye zama tayi kawai tana bin sa da kallo kamar zata maƙure sa don baƙin ciki

Umma tace, “Ni ban san irin ka ba Sajjad, wlh zan saɓa maka idan ka cika shiga shirgin yarinyan nan, ina ruwan ka da ita ne?”

“Umma kina so in barta da yunwa ne bayan mata ta ce? Abba kana ji ko?” Yayi maganar kamar zai yi kuka

Abba yace, “kyale ta My son, amma ka dena mata abin da bata so kaji tunda ta nuna ba ta son zuwa ka barta mana. Idan ba haka ba zata tsane ka”.

“To Abba zan dena bazan sake ba”. Sai ya kalli MEEMAN da har yanzu take zubar da hawaye yace, “sorry My Angel I will not do it again, let me serve you”. Ya ƙare maganar yana rawan jiki wajen serving ɗin ta

Murjana dake zaune a kan dainning ɗin tashi tayi tana jan tsaki tace, “amma wlh Yaya kaji kunya na rantse da Allah, ji be yanda kake mata bauta kamar zaka haɗiye ta?”

Be kula ta ba

shiyasa ta sake jan tsaki ta wuce wajen su Abba dake Parlour’n ta zauna tana cewa, “umma akwai matsala fa, dole sai kin shiga tsakanin Yaya da wannan yarinyan, idan ba haka ba wlh kina gani zai zama mijin tace”.

Umma da damuwa ta kalli Abba tana cewa, “ka gani ko abinda nake gudu kenan, don Allah ji be yanda yake ɓarin jiki Abban Sajjad?”

Abba yace, “ke dai Jamila ki bar wannan zancen duk na ɗan lokaci ne, idan muka cika burin mu komi zai ƙare”.

“Ta ya ya? Kana ganin hakan me yiwuwa ne? Ni fa kar azo garin cikan burin ku in rasa ɗana”.

Abban be kai da magana ba Sajjad ya ɗaga murya yana cewa, “Abba ka ga ta ƙi ci”.

“To ka ƙyale ta mana uwar ka ce?” Umma tayi maganar a fusace

“Zulaiha eat the food ok?” Inji Abba cikin kwantar da murya

Girgiza masa kai tayi alamun baza ta ci ba

“I said eat I don’t want to argue.”

Dole a wannan lokacin ta soma ci ba tare da ta sake cewa uffan ba, dama yunwa take ji kuma abincin ba daɗi yake mata ba, shiyasa idan ta Kai spoon ɗaya sai ta ɗau soconni take sake kai wani

Sajjad da ya saka ta a gaba yana kallon ta har da murmushi sai yace, “Babe don’t you enjoy the food? What do you want to bring you now?”

Bata ɗago kai ba bare ta kalle sa gaba ɗaya zuciyar ta tsanar sa take ji a ranta, ko kaɗan ba ta ƙaunar ta kula sa shiyasa tayi masa shiru, tana sake kai wani spoon ɗin baki ta tashi ta ture kujeran zata tafi

Shima biyo bayan ta yayi kamar jela yana tambayar ta, “did you finish?”

Abba ya kira ta yace, “come and sit here, I ask you”.

Zuwa tayi ta zauna tana sake haɗe rai fuska a kumbure

Umma da Murjana sai aikata mata harara suke yi kamar za su make ta

Shi kuma Sajjad tuni ya zo ya zauna kusa da ita yana kallon ta

Abba murmushi yayi yana kallon ta yace, “Daughter I know our country is very happy for you. Are you happy to be here?”

Tura baki tayi gaba bata ce komi ba

“Ok, since you refuse to talk, I want you to say what you need, so that tomorrow it will be brought to you”.

“I don’t want anything”. Tayi maganar tana tashi tsaye zata wuce, sai kuma ta juyo fuska babu walwala tace, “I need Simcard”.

Kafin ma Abba yayi magana Sajjad yayi saurin tsagal ɗin cewa, “Abba ina da sabon Simcard a ɗaki na bari in ɗauko in bata”. Ya ƙare maganar yana tashi da rawan jiki ya wuce ɗakin sa

Shi kansa Abba abubuwan da Sajjad ɗin yake yi ya soma ba shi mamaki da tsoro, sai ya ɗan yi murmushin yaƙe yana kallon MEEMA yace, “Let your brother take it.”

Koma wa tayi ta zauna ba tare da tace uffan ba

Umma tace, “Abban Sajjad wlh abun da Sajjad yake yi ya fara yin yawa”.

“Jamila Ni kaina na ga hakan, amma ki sani wannan yarinyan bilonia ce shiyasa kika ga nima ban ɗauki mataki a kanta ba, dukiyar ta kawai muke so daga nan mu kore ta”.

“To ku amshi kuɗin mana meye na tsaya wa lallaɓa ta?” Umma tafaɗa a fusace

“To ta ya ya zamu amsa bayan kafin mahaifin ta ya rasu sai da ya mallaka mata komi? Yanzu ko mu kan mu bamu da damar amsar gadon mu, kuma kin ga ba nan Nigeria bane idan muka ce zamu amsa ta tsiya ƙarshe kulle Kan mu zamu yi, can suna da doka ba irin nan bane, duk ƙadarorin sa suna can babu damar mu siyar da su a can sai da saka hannun ta da kuma yardan ta”.

Sajjad ɗin ne ya ƙariso wurin da sauri ya miƙa mata Simcard ɗin

Amsa kawai tayi ta tashi ta wuce

Umma tace, “kai Sajjad wai me ka gani a jikin yarinyan nan ne da kake ta rawan ƙafa a kanta?”

“Wlh Umma ban taɓa son wata yarinya a duniya kamar Zulaiha ba, ina son ta sosai, don Allah Abba idan za’a tsayar da ranan auren mu a saka nan kusa kafin in koma karatu na na master’s sai mu tafi tare”.

Riƙe baki Umma tayi da cewa, “Iyeeeee Sajjad”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button