MEEMA FAROUK 1-END

MEEMA FAROUK Page 11 to 20

“Umma kema kin san halin Sajjad, Ni wlh gaba ɗaya na tsani yarinyan nan gaskiya Abba a hana sa auren ta..”

Kafin ta ƙarisa maganar ma Sajjad ya bige mata baki, “ke ki kama kanki Allah zan tattaka ki ina wasa dake ne?” Yayi maganar yana wani zazzare mata idanu

Ita kuma kuka ta saka ta hau shura ƙafafu

Abba yace, “meye kuma na dukan ta My son?”

“Abba baka ji me take cewa bane? Idan ba ta son ta ai Ni ina son ta, Kuma wlh idan ta sake zan fasa bakin ne”. Ya ƙare maganar da tashi ya wuce ɗakin sa

“Ke ma kiyi hakuri da Allah ba fa wani dukan ki yayi ba kina wani ɓare wa mutane baki”. Inji Umma tana kallon ta

Tashi Murjanan tayi tana bubbuga ƙafafu ta wuce ɗaki tana cewa, “ai dama kun fi son shi wlh, kuma bazan yarda ba sai na rama”.

Tana shiga ɗakin MEEMA dake kwance a kan gado tayi saurin ɗago wa saboda a tunanin ta ko Sajjad ne, ganin ba shi bane sai ta mayar da kanta ta ci gaba da waya da Esha da ta kira ta suna gaisa wa

Dogon tsaki Murjanan ta ja tana wuce wa Toilet, tana fito wa ta haye saman gadon tana sake jan tsaki kamar wacce tsaka ta haifa, “dole ne ma a raba mana ɗaki don bazai yiwu in riƙa kwana da ita ba, shegiya kawai da wani fuska sai kace na mage”.

MEEMA na jin ta sai dai dayake bata san me take cewa ba wayan ta kawai take yi, sai da duk ta kira su Ummu Hani da Zamiya suka gaisa kafin ta ajiye wayan tayi addu’a ta shafa ta gyara kwanciyar ta, rufe idanuwan ta tayi zuciyar ta duk babu daɗi, bata jin ko wani irin farin ciki a cikin ta, tana ji baza ta iya zama a gidan nan ba Sajjad na mata abun da ya ga dama, sosai take jin tsoron kar ya zo yayi mata wani abun, shiyasa take ta saƙa da warwaran hanyar da zata ɓullo, ko kaɗan zaman gidan ba ya mata daɗi tunda ta fahimci kamar ba ƙaunar zaman ta suke yi ba, musamman ma Murjana da Umma da suke mata wani kallo, ga kuma Sajjad dake son takurata, tana ga idan babu hali dole zata koma can Riyadh, gwara ta zauna a can zai fi mata, amma kuma abu ɗaya ke hana ta tafiya saboda wasiyyan mahaifin ta, umarni ya bata ta koma wajen mahaifiyar ta ta zauna da ita, but ko kaɗan ba ta ƙaunar sake tozali da Ummeen ta har ta koma ga mahalicci, ta tsane ta sosai a zuciya shiyasa ta ga gwara ta zo wajen dangin Mahaifin nata ta zauna tunda zaman ta a can ne be son tayi ita kaɗai, sai dai a yanzu ɗin tana ganin dole ta nemi layin Ishaq ta ba shi haƙuri ya taho nan ya aure ta ta bi shi, hakan shi ne maslaha a rayuwar ta don baza ta iya zama a cikin Nigeria ba, har yanzu ƙasan be mata daɗi ba, but idan ta auri Ishaq sun koma can hakan ba yana nufin ta ƙi bin umarnin Abee ɗin ta bane. Share hawayen fuskar ta da tun ɗazu suka soma sintiri tayi tana gyara kwanciyar ta, ƙanƙame jikin ta tayi tana sake jin kewar Abee na ratsa mata zuciya, da ace yana da rai da ba haka ba, komi nata na farin ciki ya ruguje, ba ta tunanin akwai ranan da zata sake farin ciki da walwala babu Abee ɗin ta, Abee shi ne farin cikin ta kuma ya tafi ya barta, rayuwar ta gaba ɗaya ta ruguje tun tafiyan Ummee, shiyasa gaba ɗaya laifin alhakin mutuwar Abee take ɗaura shi a kanta, ita ta kashe mata Abee ɗin ta da a yanzu suna tare cikin ƙaunar junan su, baza ta taɓa yafe mata ba. Daƙyar a daren barci ya ɗauki MEEMA tare da mafarkai kala-kala.

???????????? 

*MEEMA FAROUK*

                        ????????????

*NA_NAFISA ISMA’IL*

*WATTPAD_UMMUDAHIRAH*

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT*????????‍

*PERFECT WRITER’S ASSOCIATION* ????

“`( WE AIN’T PERFECT, BUT WE’RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS????)“`

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*

                 *SADAUKARWA*

_Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._

            *TUNATAR WA*

_Kamar yadda sallah take ibada ce ta ruhu, haka nan muka lura cewa wajen yin ta jikin yakan sami babban ƙarsashi saboda motsa shi da ake yi. Ƙwararrun masana wasannin motsa jiki sun yaba da abubuwan da sallah ta ƙunsa, harkokin nan daban-daban waɗanda ake nanata su a cikin raka’o’in Sallah. Wadannan harkoki ba su barin wata gaɓa a jikin mutum mai Sallah sai sun motsa ta. Watau dai, yadda musulmi suke samun ibada ta ruhu a cikin sallah, haka nan ma suna samun amfani babba na motsa jiki._

         _lada da fa’ida da mai yin Sallah zai samu kenan. Ina hukuncin wanda ya yi watsi da ita, ya ƙi bari ta zame masa garkuwa?_

         _Duk wanda ya juya wa sallah baya ya guje wa Musulunci, ya saɓi Ubangijin sa. Ya karya dokokin imanin sa, ya kuma kama hanyar halaka. Duk ayyukan sa na ƙwarai sun ɓalɓalce don kuwa ya kauce wa umarnin Ubangiji game da Sallah – duk wanda ya saɓa ma Allah tamkar ya ce ba shi ne ma, domin kuwa ai da ya amsa cewa akwai Allah ai ba shakka da ya bi umarnin sa, kamar dai yadda yace, a cikin Alƙur’ani mai tsarki:_

        *”Kuma ku tsayar da Sallah. Lalle sallah tana hanawa daga alfasha da abin ƙi”* _Suratul Ankabut, aya ta 45._

Allah yasa mu dace.

                             *NO_16*

             *WASHE GARI*

          MEEMA na cikin barci ta ji ana shafa mata face, tana buɗe idanuwan ta suka faɗa cikin na Sajjad dake durƙushe a gaban gadon ya tsira mata idanu, da sauri ta sake zaro idanun nata don sake gasgata shi ɗin ne a lokaci ɗaya tana me tashi zaune

“Good morning my love.” Yayi maganar yana mata murmushin sa me kyau

Bata iya amsa wa ba kuma bata cire idanun ta a kan sa ba, sai ma tamke kyakykyawar fuskar ta da tayi tana mishi mugun kallo

Tashi yayi ya zauna a gefen ta, kana ya saka hannun sa zai riƙe nata

Tayi saurin daka masa tsawa tana janye hannayen nata, “don’t touch me again”.

“Why dear?” Yayi maganar kamar zai yi kuka

Tashi tayi daga kan gadon tayi hanyar Toilet ta shige

Da kallo ya bi ta kamar zai haɗiye ta tsaban yanda tayi masa kyau a cikin guntun rigan barcin nata, ko kaɗan ya kasa ɗauke ido a ƙofan har sanda ta fito

Ganin sa a zaune har yanzu sai ta ɗauke kai kawai tana sake haɗe fuska, wajen Trolly ɗin ta ta nufa ta ciro towel da abubuwan da zata buƙata ta sake shige wa Toilet ɗin

Sajjad buga tagumi kawai yayi still idanun sa a kan ƙofan ya ƙi ko gezau. A lokacin da ta fito ai sandare wa yayi ganin ta daga ita sai towel, gaba ɗaya santala-santalan cinyoyin ta a waje suke

Ita kanta bata yi tunanin zata sake ganin sa ba kasancewar ta ɓata lokaci a cikin Toilet ɗin, da sauri ta ja ta tsaya tana kallon sa cike da haushi, “I will prepare. Please Get out.”

Numfashi ya sauke sabida jin daddaɗan muryan ta a kunnen sa, yanda yake ji a jikin sa bazai iya magana ba shiyasa a hankali ya taka ya fice a ɗakin har yana sake waigen ta, ji yake yi kamar ya koma ya haɗa jikin su wuri ɗaya tsaban feelings ɗin da yake ji

Ita kuma yana fita ta ja dogon tsaki ta nufi kayan ta, gaba ɗaya zuciyar ta ba ta mata daɗi har ta gama shirin ta cikin wata doguwar riga fara ne wuyan love, rigan Robber ce gaba ɗaya ta bi ta lafe mata duk ta fito mata da shafe ɗin jikin ta, dayake akwai ɗan guntun Hijab ɗin sa maroon color da aka yi design da less a ƙasan, shi ta saka ya tsaya mata a iyakan kafaɗa, da agogon ta da flet shoes ɗin da ta sanya duk na kayan ne white color, tayi kyau sosai duk da fuskar ta babu abun da ta sanya, wayan ta dake ajiye ta ɗauka ta fita Parlour

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button