MEEMA FAROUK Page 11 to 20

Babu kowa sai Sajjad dake zaune. Yana ganin ta ya tashi tsaye idanuwan sa kamar za su faɗo a kanta, tsaban kyan da tayi masa tamkar ya je ya haɗiye ta haka yake ji, sosai MEEMA take da mugun kyau shiyasa gaba ɗaya ta zauta shi ya koma kamar wani soko a kanta, shiyasa ko barcin kirki ba ya iya samu sabida rashin kula sa da take yi, ba zai iya haƙura da ita ba a rayuwar sa, tabbas idan ya rasa ta mutuwa zai yi domin be taɓa ƙaunar wata mace ba sai ita, duk da yana da tarin ƴan mata domin Sajjad na mata ne but sai dai ya gara su be san cewa akwai ranan da wata mace zata shiga zuciyar sa kamar yanda MEEMA tayi ba… Idanuwan sa ya lumshe sanda ta gifta sa ta wuce ƙamshin daddaɗan turaren ta na Arab ya bugi hancin sa. Ya buɗe su yana bin bayan ta da kallo har ta zauna a saman dainning. Wani irin numfashi ya ja nan da nan idanun sa suka soma kaɗa wa, bazai iya jure wa ba dole ya nufi inda take shima ya ja kujera ya zauna, kamar zai yi kuka tsaban yanda yake kallon ta yace, “Zulaiha”.
Kallon sa tayi sanda ta kai tea Cup bakin ta, ido cikin ido suke kallon juna sai dai fuskar ta a tamke yake tun zaman sa a wurin ta sake haɗe wa
“I love You, why don’t you love me?”
Kawar da kanta tayi bata iya cewa komi ba taci gaba da shan tea ɗin, sosai yake tururi but haka take kaiwa baki tana kurɓa a hankali
Sai shima yayi shirun ya sanya mata idanu zuciyar sa babu daɗi
Wayan ta ta ɗauka ta soma latsa wa still tana kurɓan tea ɗin, Numban Ishaq ta rubuta sannan tayi dealing but switch off, tsaki ta ja tana ajiye Cup ɗin ta tashi tsaye ta wuce
Har ta kusa shiga ɗaki Umma da ta fito a nata ɗakin ta kwaɗa mata kira
Hakan yasa ta tsaya tana kallon ta, sai kuma ta buɗi baki a hankali tace, “Morning Mom”.
“Kar ki koma ɗakin nan ki zo ki gyara mana parlour, sannan ki shiga kichen ki ɗaura mana girki”.
Ita dai MEEMA tsaya wa tayi tana kallon ta bata ce uffan ba tunda bata san me tace ba
Sajjad da ya taho wurin ya kalli Umman yace, “Umma wani girki kuma? Haba Umma daga zuwan nata tana baƙuwa sai ki saka ta aiki? Ni gaskiya baza a saka min mata aiki ba”.
“Sajjad ka fita ido na tun kafin in nuna maka fushi na, idan bata yi aikin ba haka zata zauna mana a gida sai dai muyi mu bata taci tayi kashi kamar wata uwar mu?” Sai kuma ta juya ga MEEMAN tace, “ke ko baki ji abinda nace bane kin tsaya kin wani kafa min idanu kamar wacce zata haɗiye Ni?”
Sajjad yace, “to ai bata san me kike cewa ba ko kin manta ba ta jin Hausa ne?”
“Ohh! To sai ka sanar mata da abun da nace”.
Juya wa MEEMAN tayi kawai zata shige ɗaki
Umman tayi saurin janyo ta tace, “babu inda zaki shiga dan uban ki, na ce ka sanar mata ko?” Ta ƙare maganar da daka wa Sajjad ɗin tsawa
“Umma yawa fa kike yi wlh, haba don Allah baki ga yanda take bane taya zata iya wani aiki? Kema daga gani kin san ƴar hutu ce baza ta iya waɗannan aikin ba Gaskiya, don Allah Umma kiyi hakuri ki barta”.
“Iyeeeee Sajjad Ni kake faɗa wa haka don uban ka? Wato ta zauna sai dai Ni nayi ita tana luƙume a ɗaki saboda ita ƴar hutu? To nan ba gidan uban ta bane wlh idan har tana son zaman ta a gidan nan dole ne sai ta yi min bauta”. Ta ƙare maganar tana jan hannun MEEMAN da cewa, “ai dole ki gane idan na tasa ki gaba”.
Da sauri Sajjad ya riƙe Umman yana cewa, “don Allah Umma ki sake ta wai meye haka ne? Ni zan yi aikin a madadin ta ki sake ta”.
While MEEMA kallon su kawai take yi zuciyar ta kamar ta fito tsaban baƙin ciki, ganin Umman ta ƙi sakar ta sai ta ƙwace hannun ta idanuwan ta har sun soma cika da hawaye, bata ce komi ba ta juya ta shige ɗakin
Nan Umma ta yunƙura zata bi bayan ta tana kiran sunan ta
But Sajjad ƙiri-ƙiri ya tare ta ya hana ta wuce wa, “haba Umma haba Umma ki ƙyale ta”.
A fusace tace, “to bari uban naka ya dawo barin gidan nan zata yi”. Sai ta wuce fuuu ta nufi kichen
Shi kuma ɗakin Murjanan ya wuce zai shiga, sai dai MEEMAN ta garƙame ƙofan da keey, dole ya haƙura ya wuce nasa ɗakin.
MEEMA bata buɗe ɗakin ba har sanda ta ji muryan Murjana kafin ta zo ta buɗe mata ta juya ta koma
Da kallo Murjana ta bi bayan ta tana ƙare wa rigan jikin ta kallo, har ta shiga ciki ta kasa ɗauke ido a kan rigan domin yanda take matuƙar son irin rigan a rayuwar ta, sai dai har yanzu bata mallake sa ba don har kasuwa suka je a lokacin ita da Habiba but basu samu ba, dole suka haƙura tunda a lokacin sun so suyi ankon ta ne sanda za’a yi auren Amina. Cire kayan ta tayi ta sanya riga da skert na atamfa kafin ta fice ɗakin. Can sai ga ta ta shigo a lokacin MEEMA ta buɗe Trolly ɗin ta ta ciro computern ta ta koma ta zauna. Tsaki ta ja tana ɗauke kai daga kallon ta
Ita kuma MEEMAN sai a lokacin ma ta ɗago da idanun ta ta dube ta, kawar da kai tayi ta ci gaba da abin da take yi
While Murjana tuni ta sake fice wa tunda dama wayan ta ta dawo ɗauka
Fitan ta babu daɗe wa Habibah ta shigo tana kiran sunan MEEMAN fuskar ta ɗauke da fara’a
Itama ganin ta yasa ta tsayar da abinda take yi tana murmusawa
“Sister I miss you so much, I can’t bear to say let me come and see you.” Tayi maganar bayan ta zauna a gefen MEEMA ta riƙe hannun ta
Sitll da murmushi a fuskar ta tace, “me too”.
“But your dress looks good on me, and it looks great on you. You are so beautiful.”
Kallon ta kawai tayi bata ce komi ba illa murmusa wa da take yi
“Aren’t you working? Because we’re going to our Part today stay for us there, I’ll be happy with that”.
Jinjina kanta tayi kafin tace, “ok I will go”. Ta ƙare maganar da rufe computern tana ɗauka ta tashi ta mayar a cikin Trolly ɗin ta, sai ta zaro irin rigan dake jikin ta sak sai dai shi blue color ne, ta kalli Habiban dake zaune tace, “take it’s for you”.
“Wow! Thank you so much. Thanks again”. Tafaɗa cikin farin ciki bayan da ta taso ta amsa rigan
“Don’t worry there is no gratitude between us.” Itama MEEMAN tafaɗa cikin murmushi kana ta mayar da Trollyn ta rufe sannan ta tashi tana kallon ta tace, “ok let’s go”.
Suna fita Habibah da ta hangi Murjana zaune a kan dainning, da gudu ta isa wurin ta tana shaida mata kyautar rigan da MEEMA ta bata
Yayinda MEEMAN ke tsaye a wurin da ta barta bata motsa ba tana kallon su, sai dai a yanzu ɗin murmushin fuskar ta ya gushe
Ita Murjana taɓe baki tayi cike da isa tace, “ai yayi miki kyau tunda kin je kin roƙe ta kin zubar mana da mutunci, ke dai wlh Habibah baki yi ba a rayuwa”. Sai ta ja tsaki tana banka mata harara ta mayar da hankalin ta kan abincin ta
Habibah da ta saki baki tana kallon ta sai tace, “to fa! Gaskiya Murjana akwai gyara a lamarin ki, har yanzu baza ki dena wannan ɗabi’an naki ba bayan kin san da cewa ita ƴar uwan ki ce, to Ni meye ma a wuri na don na roƙe ta ai kin san Ni ba irin ki bace domin ba Ni da girman kai”.
“To kar dai ki gaya min magana don Allah ki tashi min akai”.
Tsaki kawai Habiban ta ja tana juya wa ta wuce wurin MEEMAN da har yanzu idanuwan nata a kan su suke, bata iya mata magana ba sai jan hannun ta da tayi suka fice.
Suna fita Murjanan ta tashi da sauri ta nufi ƙofan ta leƙa su, ganin da tayi sun bi hanyar Part ɗin su Habiban sai ta koma ta rufe ƙofan ta wuce ɗakin ta da sauri, tana shiga ta nufi wajen Trollyn MEEMAN ta saka hannu zata buɗe.