Bata iya magana ba sai kallon sa da take yi"What happened to bring you here? Where is your father?" Ya sake jero mata waɗannan tambayoyin Wannan karon ma bata ba shi amsa ba Dole ya kalli Me gadin yace da shi, "ya ɗauko mata kayan nata ya shigo da su," sannan yace mata, "she follow him". Shiga suka yi gidan suka wuce Part ɗin Kawu Ali. Sai da yayi Nocking kafin ɗiyar sa Murjana da suke zaune da Umma a parlour'n suna kallo ta zo ta buɗe masa jin muryan Kawu Zubairun "Lafiya me ke faruwa? Wace ce wannan kuma?" Inji Umma domin itama ta taso ta biyo Murjanan a baya a tunanin ta ko babu lafiya ne Shi kuma yace mata, "baki gane ta bane? Zulaiha ce ƴar wurin Faruk". "Faruk.. Faruk dai ɗan uwan ku na Riyadh?" Ta ambata tana sake ƙare wa MEEMAN kallo "Eh shi. Kira min Yayan nawa sai ki sanar masa do Allah". "To shikenan bari in shiga in Kira sa". "Ke kuma ki zo ki zauna kin wani tsaya a tsaye". Inji kawu Zubairun yana kallon MEEMAN dake tsaye har yanzu a bakin ƙofa. Ganin bata motsa ba sai ya tuna ai ba ta jin Hausa sai ya kuma maimaita mata da turanci Hakan yasa ta tako a hankali tana bin ko ina da kallo ta zo ta ɗofana mazaunan ta a kujeran Itama Murjana zama tayi tana ƙare mata kallo kafin kuma ta kalli Kawu Zubairun tace, "wai Kawu wannan ɗin ita ce yarinyan Uncle Faruk ɗin?" "Eh ita ce mana baki ga sun yi kama da uban nata bane?" Taɓe baki tayi tana sake ƙare wa MEEMAN kallo don bata taɓa sanin ta ba, a kaf gidan ma babu wanda ya san ta illa labarin ta da suke ji, sai kuma su Kawu Ali da suke zuwa can ɗin shi ne suka santa. "Ina Zulaihan take?" Inji Kawu Ali da ya fito da sauri daga ɗaki Umma na take masa baya. Ganin ta yasa yace, "ashe dai ba ƙarya Jamila take min ba itan ce da gaske, ikon Allah". Yafaɗa yana zama gefen Kawu Zubairu idanuwan sa a kan MEEMAN, kafin kuma ya juya yana tambayar Kawu Zubairu, "a ina ya samo ta?" "Nima wlh Ina tsaye a bakin ƙofan sashi na na hangi Gali Yana taho wa, shi ne nake tambayar sa lafiya ina zai je? Yake sanar min wai baƙuwa ce ta zo kuma wurin ka ta zo shi ne zai zo ya sanar maka, Ni kuma nace mu je in ganta". Kawu Ali yace, "to ke wa ya nuna miki gidan namu? Waye ma ya kawo ki ƙasar? Ina uban naki?" "Kaima ka san ba ta jin ka tunda ba iya Hausa tayi ba". Cewar Kawu Zubairun Shi shaf ya ma manta sai ya juya harshen yana sake tambayar ta "My Abee is Dead". "He died?" Suka faɗa a tare cikin wani irin farin ciki da ya kasa ɓoyuwa a fuskar su Ita kuwa bata ma fahimci yanayin nasu ba sai gyaɗa kanta da tayi cikin muryan kuka take cewa, "yes he died and left Me". A nan take sanar musu da komi da mutuwar nasa da kuma wasiyyar da ya bata ta dawo Nigeria ta zauna "Ka gani ko Zubairu ai Allah ba azzalumin bawan sa bane, tunda Ni na gansa a haka dama na san zai wula nan ba da jima wa ba, muka so mu taimake shi mu tafi da ita amma ya ƙi furr har shegiyar yarinyan nan tana mana rashin kunya, sai ga shi dai mu ne dolen ta ga shi ta dawo wurin mu, to uban wa yace mishi muna da wurin ajiye ta? Ai a daren nan zamu kaɗa shegiya ta tafi.." Kawu Zubairu yayi saurin taran numfashin sa da cewa, "to gadon mu fa? Haka zata tafi da dukiyan nasa bayan shi muke wa sintiri tun ba yanzu ba?" "Gaskiya nima abun da na gani kenan?" Inji Umma da ta saka musu baki Kawu Ali yace, "to ai dole sai mun amsa kason mu kafin ta bar mana gida". Sai ya juya yana kallon MEEMA da kanta ke saman cinyoyin ta tana ci gaba da kuka yace, "so since he died now where is our inheritance? Where is your father's property then we will share?" Ɗago kai tayi tana kallon su, sai kuma tace, "Abee owned everything for me before he died, and now he has returned all his property to my name." Wani ashar Kawu Ali ya fesar ya buɗe jajayen idanuwan sa zai yi mata magana sai Kawu Zubairu ya dakatar da shi "Ka ga Yaya bar ta don Allah, na nemo mana mafita, ai maganar ma gado bata taso ba, kaf dukiyar sa ya zama namu wlh kuma dole sai mun amshe sa, amma yanzu idan kace zaka nuna mata halin da muke ciki zata iya tafiya wajen uwar ta ta bar mu, yanzu samun hanyar da zamu yi mu mallaki komi ya zama namu shi ne mafita, in yaso daga baya sai mu kore ta ta tafi, ka san tayi karatu tana da ilmi dole sai mun nuna mata siyasa komi ya dawo hannun mu". Shiru Kawu Ali yayi yana tunani Umma tace, "Abban Sajjad maganar Zubairu fa a kan gaskiya take, yanzu ai ko kace zaka amshi komi bazai yiwu ba, ta yiwu ma babu komi a hannun ta dole zata zauna damu har sai kun mallaki komi ya zama naku kafin ku kore ta". Sai da Kawu Alin ya kalli Murjana yace, "ke ja ta ɗakin ki ku tafi ki nuna mata komi don a can zata zauna". Tashi tayi tana kallon MEEMAN cikin yatsina tace mata, "she got up and they went". Hakan yasa ta kalli su Kawu Alin ta ƙi ta tashi Shi kuma yace, "she get up and followed her to her room." Sannan ne ta tashi ta ja kayan ta tabi bayan ta suka wuce ɗakin Murjanan "Yauwa to na yarda da shawaran ku hakan za'a yi, yanzu dai dole zamu ja ta a jiki domin mu mayar da duk ƙadarorin ta ya zama namu". "Eh Yaya hakan za'a yi". Inji Kawu Zubairu "To shikenan mu bar maganar yanzu sai zuwa gobe sai mu ci gaba da tattaunawa ko zamu ɓullo hanyar da ya kamata". Da haka suka rufe maganar Kawu Zubairu yayi musu sallama ya tafi. Su kuma suka wuce ɗakin su. *WASHE GARI* Sai tara da rabi MEEMA ta farka daga barcin da ya ɗauke ta tun sallan asuba da tayi ta koma. Ta jima a zaune a saman gadon bata iya tashi ba tana ta faman tunanin da ya zame mata jiki, da kuma yadda Rayuwar ta zata koma a nan gaba a inda bata saba ba. Sai daga baya ta miƙe sabida yunwan dake ƙwaƙulan ta don babu wanda ya zo ya tashe ta, daga ita sai farar riga me tsantsi da guntun wandon sa ta shiga bayi tayi brush sannan ta fita parlour'n ko ɗan kwali, sai dai ta kama gashin nata ta tufke shi a tsakiyar kan. Babu kowa a parlour'n sai wani kyakykyawar saurayi bafulatani fari sol, don da gani kaf gidan ya fi su kyawu domin shi zak Fulani ne babu silƙi, tamkar dai Mahaifin MEEMA ya haife sa saboda kamanceceniyar da suke yi, don shi ya fi kama dashi a kan su Kawu Ali. Yana zaune ne a kan sofa ya saka ear phone a kunnen sa, daga shi sai gajeren wando ko riga babu, kan nan nasa ya sha askin zamani wanda ƴan iska suke yi, ya bar tulin gashi sosai a tsakiyar kan wanda ko kitso za'a iya yi tsaban tsawon sa, wata macen ma baza ta nuna masa yawan gashi ba. Waƙa yake bi na Turanci duk ya kure parlour'n da muryan sa MEEMA dake tsaye a bakin ƙofan tunda ta fito ta hange shi sai ta tsaya cak tana bin sa da kallo, tayi five minutes a tsaye a wurin tana faman kallon sa kafin kuma a hankali ta tako ta soma dosan cikin parlour'n zata wuce zuwa kan dainning table da ta hango Gab ta iso kusa da wajen nasa ne ya ankare da ita, da sauri ya ɗaga idanu yana kallon ta, be san sanda ya miƙe tsaye a kan ƙafafuwan sa ba yana sake ware ido a kanta Itama idanun ta na a cikin nasa ta kasa ɗauke nata a kanshi, sai dai ko kaɗan fuskar ta babu alamun walwala haka take kallon sa. Sai da ta kusa wuce wa kafin ta janye nata idanun ta nufi saman dainning Har sai da ta zauna before ya kawar da kansa ya nufi ɗakin Umman sa yana kwaɗa mata kira kamar zai tsaga gidan Kafin ya kai har ta fito da sauri tana faɗin, "lafiya Sajjad wannan wani irin kiran mafarauta kake min? Me ya faru ne?" "Umma wace ce wannan? A ina kuka samo ta?" Sai da ta bi inda yake nuna mata da kallo ta hangi MEEMA a zaune har ta soma haɗa tea ko kallon inda suke bata yi ba, sai ta ja tsaki don ta manta da ita a gidan sai yanzu da ta ganta, tace dashi, "jiya ta zo ai lokacin kayi barci, yarinyan Uncle ɗin ku ne na Riyadh". "What..! You mean Zulaiha ce wannan?" Yafaɗa yana sake nuna inda MEEMAN take a zaune "Eh ita ce. Ka bari idan Abban ku ya dawo sai yayi maka bayani Ni yanzu ina aiki". Tafaɗa tana juya wa ciki ta bar sa a wurin Shi kuma juya wa yayi ya isa inda MEEMAN take Sai da ya ja kujera ya zauna kafin ta ɗago tana kallon sa da manyan idanuwan ta Washe baki yayi yana bata hannu yace, "Hi Zulaiha I'm Sajjad your brother". Sai ta bi hannun nasa da kallo tana tsayar da taunan bread ɗin da take yi Murmushi ya sake yi yana tura mata hannun yace, "I'm your brother fa? I was so surprised to see you here, I never thought of that, are you so good. The truth you very beautiful. " Miƙe wa kawai tayi ta juya ta bar wurin Shi kuma sai ya saki baki yana bin ta da kallo kamar zai zubar da yawu, har wani lanɗe baki yake yi. "Wow gaskiya tana da kyau. Wai dama haka take yarinyan? Amma gaskiya an cuce Ni da ba'a nuna min ita ba sai yanzu. Wow.. wow". Yake ta faɗi yana shafa ƙeyan sa, sai kuma ya tashi ya wuce ɗakin Umman nasa, ya same ta tana gyaran gado sai ya zauna a kan drowan gadon yana cewa, "Umma wlh yarinyan kyakykyawa ce sosai har kama take yi dani, amma a nan gidan zata zauna ko?" Ɗago wa tayi tana hararan sa kafin tace, "Ni fa Sajjad ka rabu da Ni da wannan halin naka, ka kiyaye Ni wlh". "Haba Common Momcy yawa ne, ki share kawai Ni fa yarinyan ta shiga raina ne wlh, I like her so much, kuma kin ga ƙanwa ta ce wani abu ne idan nayi tambaya game da ita?" "To ka je ka tambaye ta mana ina ruwa na a ciki?" "To ai Umma ta ƙi kula Ni ne, yarinyan tana da matuƙar class ta haɗu Allah fa ina gaya miki". "Hohoho Sajjad baza ka rabu da Ni ba ko?" "Sorry Momcycy na rabu dake." Ya faɗa yana tashi tsaye tare da sara mata, sai kuma ya matso kusa da ita yana cewa, "but Umma Ina Murjana sai in tambaye ta?" "Ta je school". Ɓata fuska yayi sai kuma ya juya ya fice. Har ya zauna a kan kujeran Parlour'n yana ta kallon ɗakin Murjanan, sai kuma ya tashi ya wuce ɗakin ya tura ƙofa ya shige MEEMA dake ƙoƙarin cire rigan jikin ta zata ɗaura tawul ta shiga wanka, sai ganin sa kawai tayi a tsakiyar ɗakin, ƙara ta saka lokaci ɗaya ta ja rigan tayi sama da shi Shi kuwa daskare wa yayi a wurin tsaban ganin kyakykyawar halittan ta da yayi, idanun sa kawai suke motsi a kanta A lokacin da gudu Umma ta shigo ɗakin tana tambayar, "lafiya?" Saboda ihun da MEEMAN tayi har ɗakin ta. A kan Sajjad ɗin ta sauke ido sai kuma ta kalli MEEMAN, "ke lafiya mene ne?" Ita dai tana tsaye ta maƙure a jikin bango tana kallon su don bata san me tace ba Sai Umman ta ja tsaki tana cewa, "wannan ai shashanci ne kawai ki zo kina cika mana gida da ƙara. Kai kuma uban me kayi mata ne da zata fasa min dodon kunne?" Daƙyar yake iya sauke numfashi, sai da ya ɗan ja fasali kamar ya dawo a cikin hayyacin sa kafin yace, "Babu Umma. Shigo wa ta kenan nima". Dogon tsaki ta ja tana juya wa kawai ta fice Shi kuma sai ya mayar da idanun sa kan ta kafin ya taka izuwa wurin ta Hakan yasa tayi saurin haye wa gadon tana sake ware idanuwan ta kamar za su faɗo ƙasa a kansa, hannayen ta kuma suna a kan ƙirjin ta sai sake matse su take yi tana ƙanƙame jikin ta. Ganin da tayi ya ƙi dakata wa daga inda yake yana neman hayo wa gadon cikin ruɗe wa tace, "what are you doing here? Please get out." Dariya ya saki yana ci je leɓe, sai kuma ya saka hannu zai riƙo ta yace, "Common Babe nayi zaton ke wayayyiya ce, ki riƙa abu kamar na classics big Girls mana, just I will hugg you because I really Love you". ???????????? *MEEMA FAROUK* ???????????? *NA_NAFISA ISMA'IL* *WATTPAD_UMMUDAHIRAH* *SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT* ???????? *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* ???? ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS????)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ *P.W.A✍️* *SADAUKARWA* _Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._ *NO_13* Da sauri ta sauka daga kan gadon ganin da tayi ya kusa taɓa ta. Fuskar ta babu walwala cikin ruɗu da tashin hankali tace, "what will you do for me? What is my connection with you? Please get rid of Me." Tsaya wa yayi yana kallon ta domin yanda ta buɗe baki ala dole tana masifa sosai ta sake burge sa, ji yake yi kamar ya je ya rungume ta ya tsotse mata bakin da ya fi ɗauke masa hankali, sai kawai ya shafa kansa yana killer smile yace, "Babe I love you so much, I am so impressed by everything you do. Please I want us to be friends..." "No I don't want to. I said go out". Ta katse sa a cikin tsawa "Ok, calm down. I'll be out." Sai ya juya yayi bakin ƙofa har yana waigen ta, yana zuwa dai-dai bakin ƙofan ya dakata yana juya wa sosai ya kafe ta da ido yana haɗiyar yawu, har da wani lanɗe baki sai faman shafa kansa yake yi wanda alamu ya nuna ɗabi'an sa ne hakan. Ya ja wani soconni a wurin kafin ya juya ya fice Wani irin ajiyan zuciya ta sauke har tana dafe ƙirjin ta ta zauna a bakin gadon, sosai zuciyar ta ke gudu kamar zata faso ƙirjin ta tsaban tsoro, a haƙiƙanin gaskiya ta tsorata da shi sosai domin abun da be taɓa faruwa da ita bane. Zumbur ta tashi kamar ta tuna da wani abu ta nufi ƙofa ta murza keey sannan ta dawo ta sake zama. Ta daɗe a wurin tana faman saƙa da warwara a ranta kafin ta tashi jiki a saɓule ta ci gaba da zame kayan nata, sannan ta ɗaura tawol ta shiga Toilet, wanka tayi ta fito ta wuce bakin dressing mirror, tsaya wa tayi kawai tana kallon kanta a mirror har a lokacin fuskar ta babu wani ɗigon walwala, ƙare wa kanta kallo take ta yi har na tsawon lokaci kafin ta ja numfashi tana wuce wa wajen Trolly ɗin ta ta buɗe, kayan da zata saka ta ɗauko, sannan ta ciro cream lotions ɗin ta da take amfani da su ta shafa ta mayar, ta saka kayan riga da skert masu tsananin kyau, rigan me ruwan madara ne me taushi sosai tana da zane-zane a jiki wanda sai ka kula da kyau zaka iya hango wa kasancewar da kalan ruwan madaran aka yi, gajeren hannu ne da ita sai kwalliya da aka yi da zare dack brown color da kuma milk ɗin, sai skert ɗin sa Robber brown color da ta sanya har wajen cikin ta, sai ta ɗaura belt ɗin sa Shima Brown but light, gyara gashin ta tayi ta kama da ribom, bata saka komi a kanta ba ta ɗauki computern Abee da nata ta haye kan gadon, buɗe wa tayi ta soma aiki akai. Abun da Sajjad yayi mata shiyasa ko kaɗan ba ta sha'awar sake fita, shiyasa tayi zaman ta a nan tana ta faman aiki a computer, sai da aka kira sallan azahar kafin ta tashi ta gabatar sannan ta sake zama ta ci gaba har sanda Murjana ta dawo ta hau buga mata ƙofa. Da sauri ta rufe computern ta mayar a cikin Trolly ɗin ta sannan ta wuce ta buɗe mata. Su biyu ta gani a bakin ƙofan ita da wata sa'ar Murjanan har kayan school ɗin su iri ɗaya ne Ita Murjana tsaki ta banka tana hararan ta ta wuce ciki While ita kuma ɗayan washe baki tayi tsaban farin ciki kawai ta rungume MEEMA, sai kuma ta sake ta tana faɗin, "Oyoyo sister. Ni ƴar uwan ki ce suna na Habibah, Habibah Zubairu, I am your uncle Zubairu's daughter, I am happy to see you". Ta ƙare maganar tana bata hannu MEEMA bata gama fahimtan maganar nata ba sabida kasancewar ta haɗa da Hausa, amma sai ta miƙa mata hannu itama tana ƙirƙirar murmushi tace, "me too". Shigowa ɗakin Habiban tayi tana riƙo hannun MEEMAN ta ja ta suka zauna a kan gado tace, "yanzu da zamu dawo school Murjana take sanar min da zuwan ki, shi ne nace bari in zo in ganki". MEEMA kallon ta kawai take yi, sai kuma ta murmusa tace, "sorry i don't understand, what did you say?" "Oh don't you understand Hausa?" Habiban tayi magana tana ware idanu da mamaki Still MEEMA tana murmushi ta gyaɗa mata kai "Ok sorry I don't know, but do you want to teach you our language?" Shiru MEEMAN tayi bata iya ce mata komi ba Sai ita kuma tayi murmushi tana riƙo hannun ta ta haɗa da nata kafin tace, "I will pass our Part, I will come back to see you later, because even in my soul I like you". "I like you too". Tafaɗa itama sosai a wannan lokacin tana murmusa wa Tashi tayi Habiban ta ɗaga mata hannu ta fice Da kallo ta bi bayan ta har ta ɓace wa ganin ta, a ranta sosai ta ji sanyi haɗuwar ta da Habiba zata samu wacce za suna magana ba kamar Murjana da ko kallon ta ba ta yi, ko magana ta ƙi yin mata Yanzu ma tuni ta fice a ɗakin tunda ta sauya kaya. Tana fita parlor Sajjad ya tare ta da maganar MEEMA, shi ne abin ya bata haushi ta ja tsaki tana cewa, "wai Yaya meye haɗin ka da ita ne da kake son sanin wani abu a kanta? Gaskiya yarinyan bata yi min ba bcoz tana da jijji da kai, ko don ta ga tana da kyau ne?". Dungure mata kai yayi yace, "kina dai baƙin ciki ne bayan haka meye a jikin ta da zaki ce bata miki ba? Ni kuma ina son ta". Tura baki tayi ta wuce ta zauna a saman dainning ta soma haɗa lunch Sai ya biyo ta yana cewa, "Common Sister ki sanar dani abun da na tambaye ki kinji? Haba My sister". Sai da ta taɓe baki kafin tace, "Wai Mahaifin ta ne ya rasu shi ne ta zo nan". "Wow da gaske?" Yafaɗa yana buga tsalle Da kallo ta bi sa kafin tace, "lafiya Yaya meye na murnan?" "Uhmm daɗi nake ji sosai a raina, kenan ta dawo nan da zama? Kin ga shikenan zan same ta". "Wai kana nufin da gaske son ta kake Yi?" "Sosai ma. Kuma auren ta zan yi domin dai-dai kala ta ce ita, macen da nake fatan samu kenan, Abba na dawo wa zan sanar mishi ayi-ayi a aura min ita". Dariya Murjana tayi tace, "daga ganin Sarkin fawa sai miya tayi zaƙi Yaya? Tab ɗijim zan ga inda draman nan zata ƙare, akwai kallo a gidan nan wlh". Ta ƙare maganar tana sake fashe wa da dariya "Ke fa baki da kunya na lura, amma bari in je in dawo kafin Abba ya dawo zaki ga me zan yi". Ya tashi ya fice Ita kuma sai dariya take yi, daƙyar ta dakatar da shi ta soma cin abincin. A lokacin ne MEEMA ta fito ta nufi wajen dainning ɗin Da kallo Murjana take bin ta har ta ƙariso ta ja kujera ta zauna. Sai ta ja tsaki tana ɗauke kai ta ci gaba da cin abincin nata Ita kuma MEEMA kallo ɗaya tayi mata itama ta cire nata idanun a kanta ta soma serving kanta. Duk da tana jin yunwa but daƙyar ta iya yin spoon uku ta ture abincin, hannu ta sanya ta janyo Flaks ɗin dake wurin ta zuba ruwan Lipton ɗin a cikin Cup, ganin babu kayan haɗa tea ɗin a wurin sai ta ɗauka haka nan ta soma sha ko sigar babu a ciki Murjana dake kallon ta ta ƙasan ido sai ta taɓe baki a fili ta furta, "sanabe gai da uwar miji a kasuwa. Zaki saki ciki ki riƙa cin abinci ne tunda nan ba can bane, ƴar wahala". Dayake MEEMAN ba jin ta take yi ba shiyasa ko ɗago wa bata yi ba bare ta kalle ta, har ta kurɓe ruwan lipton ɗin ta tashi zata koma ɗaki A time ɗin ne Habiba ta shigo ita da Inna Mahaifiyar ta, dayake itama ta shigo domin ta ga MEEMAN ce tunda Kawu Zubairu ya sanar mata "Yauwa Inna kin ganta". Cewar Habibah cikin farin ciki tana me ƙarisa wa kusa da MEEMAN ta riƙe mata hannu. Sai kuma ta juya ga MEEMA tana ce mata, "she's her mother". Hakan yasa ta ɗan saki fuska tana gaishe ta Inna kuwa sai ƙare wa MEEMAN kallo take yi tana faman yamutsa fuska da taɓe baki, domin itama irin waɗannan jarababbun matan nan ne, don har ta fi Umma iya shege Sai da Habiba tace mata, "Inna gaishe ki fa take Yi?" "To Ina na sani tunda ba iya Yaren nayi ba?". Sai kuma ta ja tsaki ta wuce tana tambayar Murjana, "Ina Umman ta?" Hango ta da tayi zaune a saman dainning "Tana ɗaki". Ta bata amsa a taƙaice Hakan yasa ta wuce ciki Habiba itama tuni ta bi MEEMA cikin ɗaki. Inna na shiga ɗakin Umma ta ganta zaune tace, "ashe kina ciki na shigo ban gan ki ba?" "Eh ina ciki Halima. Aiki na gama kuma na zauna ban fita ba". Inna zama tayi a gefen ta kafin suka gaisa kana tace, "Wai Jamila haka zaki zauna da yarinyan nan a gidan ki. Me ya kai ki amsar ta?" "Wace yarinyar?" Umma ta tambaya tana kallon ta "Wannan Yarinyan mana na wajen Faruku". "Ohh wlh Ni manta wa nake yi da ita a gidan, to ya na iya tunda ba dauwama zata yi ba, su ma su Abban Sajjad ɗin ai suna shirin koran ta ne bayan komi ya dawo hannun su". "Ai gwara haka don wlh bata da wurin zama a wannan gidan haka kawai, Ni kinga Habibah ne ma naga tana wani murna da zuwan ta, Ni fa bazan lamun ta hakan ba wlh sai in saɓa mata". Umma tace, "ai Ni dayake Murjana babu ruwan ta kinga ko shiga safgarta bata yi ba". "Na san maganin Habiban ai, bari in je wanki nake yi na taso". Cewar Innar tana tashi tsaye Itama Umman tashi tayi ta bi bayan ta suka fita Parlour suna sake zantawa Innar ta tambayi Murjana dake zaune a kan sofa a yanzu tana latsa waya, "Ina Habiban?" "Ta bi wancan yarinyan ciki". Tayi maganar cikin taɓe baki "Habiba.. Habiba". Inna ta ɗaga murya tana kiran ta Da sauri ta fito tana faɗin, "Inna gani nan fa ba nisa nayi ba". Hararan ta tayi tana cewa, "ai na san ba nisan kika yi ba, uban me kike yi a wurin ta?" "Inna babu komi fa muna hira ne tunda.." Katse ta tayi tana faɗin, "dalla rufe min baki, idan baki yi wasa ba wlh zan saɓa miki a gidan nan, ina ruwan ki da ita daga zuwan ta zaki fara maƙale mata?" "Inna ƴar uwa ta ce fa". Tafaɗa tana zaro idanu "Eh ƴar uwan taki, ba na son alaƙar ku nace, wuce mu je dalla". Habiba cike da rashin jin daɗin abun da uwar nata tayi mata haka ta bi bayan ta suka fice "Nima fa wlh yarinyan ba burge Ni tayi ba Umma, idan ba ma zubar da kai ba na Habibah daga zuwan ta ta wani fara maƙale mata, da can suna son mu ne da zata zo mana gida?" "Nima abun da na gani kenan, ki barta ai mu ma ba dauwama zata yi mana a nan ba, can ta wuce dangin uwar ta ba dai nan ba, don bazan riƙe ɗan riƙo ba wlh". "To Umma amma fa bazai yiwu ta zauna a haka kullum ki girka ki bata ba babu abinda zata rika yi ƙatuwar budurwa kamar ta, nan ba gidan su bane dole ta riƙa yin aikin gida ko nima zan huta wlh, kinga tunda na fita ke baki gyara parlor'n nan ba ita kuma bata zo tayi miki ba." Umma tace, "to dama ai na barta ta ɗan kwana biyu ne kafin ta soma mana aiki, wlh ƴar aiki aka kawo mana don bazai yiwu ta ci ta sha a gidan nan ba ta luƙume a ɗaki, ki bar ta zuwa gobe komi na gidan nan dole tayi shi, wannan sanƙamemiyar budurwan da a yanzu tana gidan miji ina zan iya da ita?". ****** MEEMA dake zaune a ɗaki duk maganar da suke yi a kunnen ta ne tun fitan Habibah, sai dai bata fahimci ko eh ba a ciki, tayi jiran ko Habiba zata dawo amma shiru shiyasa ta kwanta tana ɗaukan wayan ta ta soma latsa wa Murjana ce ta shigo ɗakin ta ganta a haka, ta ɗauke kai tana wani ciccin magani ta wuce ta shiga Toilet. Bata jima ba ta fito tana kallon MEEMAN tace, "ke dalla tashi ki fita zan gyara ɗaki na tunda baki san ki gyara min ba". Idanu ta zuba mata tana mamakin yadda take hararan ta tana mata tsawa a kai. Shiru kawai tayi tana sake ƙare wa Murjanan kallo, ko a girme zata bata good 5years ko fiye da haka.. "Keee! Ko ba kya ji ne ki tashi nace ko gadon uban ki ya siya min ne?" A wannan karon ma Murjanan tayi maganar a fusace tana ɗaga murya Tashi zaune MEEMA tayi tana kallon ta sosai kafin tace, "what do you say I don't hear you?" "Uban ki nace banza kawai. I said get up and go out". Ɗauke kai tayi daga kallon ta tana me ɗaukar wayan ta ba tare da ta furta komi ba ta tashi ta fice a ɗakin.. Kai tsaye Parlour ta koma ta zauna tana ɗaura kanta a saman kujeran ta lumshe idanuwan ta Sajjad ne ya buɗe ƙofan ya shigo yana rera waƙa ear phone a kunnen sa. Idanuwan sa suna sauka a kanta yayi saurin zare ear phone ɗin yana bin ta da kallo kamar zai haɗiye ta tsaban kallo while zuciyar sa cike da farin cikin ganin ta Ita kuwa tuni ta ɗago tun sanda ta ji muryan nasa itama tana kallon sa, sai dai ta sake haɗe rai kamar bata taɓa dariya ba. ???????????? *MEEMA FAROUK* ???????????? *NA_NAFISA ISMA'IL* *WATTPAD_UMMUDAHIRAH* *SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT* ???????? *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* ???? ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS????)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ *P.W.A✍️* *SADAUKARWA* _Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._ *NO_14* Ɗauke kai tayi a kansa ganin ya taho wurin ta. Sosai ƙirjin ta ke luguden buga wa saboda tsoron sa amma ko kaɗan bata nuna a fuska ba Har ya zo ya zauna gefen ta yana wani faman shafa kai da kafa mata idanu kamar wanda zai cinye ta. Cikin sanyin murya yace, "Babe why don't you want to take care of Me? I am your brother and I love you so much." Ɗago Kai tayi ta kalle sa, sai dai bata ce komi ba ta sake ɗauke kai a kansa Numfashi ya ja kafin yace, "ok I'm so sorry for what I did to you, I forgot I did not greet your dead father, sorry God bless his grandson". Still dai shiru tayi Sai shima ɗin yayi shiru kawai yana kallon ta Abba ne ya shigo gidan da sallama a bakin sa Sajjad ya amsa mishi yana kallon sa, sai kuma ya miƙe ya nufe sa yana hugg ɗin sa tare da cewa, "Oyoyo Dadyyyy". "My son ya kake?" Abban yafaɗa yana shafa kansa cikin fara'a "I'm fine Abba, sai dai i miss You so Much". Dariya yayi yana bugan kafaɗan sa da cewa, "Oh my son baza ka dena halin ka ba". Cikin shagwaɓa yace, "Allah Dadyyyy da gaske nake yi fa". Idanu MEEMA ta zuba musu tana faman kallon su, sai kawai Abee ɗin ta ya faɗo mata a rai, lumshe idanu tayi tana me buɗe su a lokaci ɗaya tare da son komar da hawayen da suka taru mata a cikin ido. Mayar da kallon ta tayi a kansu da har sun ƙariso wurin, sai ta tashi cikin girmamawa tace, "Welcome Dad". Yaƙe yayi Kawu Ali yana kallon ta yace, "Ah Zulaiha you are here?" "Na'am Dad". "Okay we have something to talk about, but then your uncle comes and we will discuss". "Nima Abba akwai maganar da zamu yi da kai gaskiya". "Ok my son, ai ko wani time lokacin ka ne faɗa mu ji". Sai da ya bubbuga ƙafafu kafin ya kalli MEEMA da ta saki baki a wannan lokacin tana kallon sa, ya nuna ta da yatsa da cewa, "Abba Gaskiya na kamu da son ta, I really love her Ina son ka aura min ita". "Whattt.. Sajjad what are you saying?" "Ina son in aure ta". Ya sake maimaita wa yana tura baki Umma da ta fito daga ɗaki a yanzu ɗin tace, "uban wa zaka aura ba dai wannan yarinyan ba Sajjad? Kana da hankali kuwa?" "Yes Umma ina da hankali na, Ni dai kawai ita nake so ku aura min ita wlh, idan ba haka ba zan mutu". Ya ƙare maganar da dafe ƙirjin sa yana wani narke fuska "Ai kuwa sai dai ka mutu wlh, ka dena tunanin ma maganar ka zai yiwu, koda yake babu wanda be san halin ka ba". "Umma wlh da gaske nake yi ina son ta da aure ne". Yayi maganar yana ƙarisa wa wajen ta da riƙo hannayen ta "Dalla sake Ni banza kawai, meye abun so a nan?" "Abba baka ce komi ba kana jin ta ko?" Yayi maganar cikin buga ƙafafu "Nima me zance Sajjad? Shirmen ka yana da yawa kai kam, Ni yanzu na dawo a gajiye ka bari na huta". Ya ƙare maganar yana wuce wa ɗakin sa Itama MEEMA tuni ta koma ta zauna tana ta kallon su kamar ta sami t.v, sai dai ko kaɗan bata fahimci inda zancen nasu ya nufa ba illa mamakin abun da Sajjad ɗin yake yi kamar wani yaro. Tana kallon yanda yake ta bin Umman har cikin kichen yana mata shagwaɓa Murjana da ta fito yanzu bin bayan su tayi tana cewa, "wai umma wa ya taɓo Yaya ne yake ta mammanne miki?" "Wai maganar wancan yarinyan yake min auren ta zai yi". Dariya Murjana ta kwashe da shi tana cewa, "ai akwai kallon drema kenan a gidan nan, nima haka yace min ɗazu abun da bazai taɓa yiwuwa bane." Biyo ta yayi yana faɗin, "ina wasa dake?" Da sauri ta gudu suka soma zagaye kichen ɗin suna zagaye Umma dake tsaye a tsakiyar kichen ɗin Sai faɗi take yi, "zaku ka dani fa". Amma ba su ji ta ba sai guje-guje suke yi, daga ƙarshe Parlour suka wuce suka ci gaba da yi Lokacin MEEMA bata a parlour'n ta koma ɗaki Ƙarshe dai ɗakin Abba suka je a can ya raba su faɗan, domin haka suka saba tunda sun zama kamar yara an sangarta su sai abun da suke so suke yi a gidan, sun tashi babu kwaɓa ko kaɗan, ba ma kamar Sajjad da yake ɗan fari, dayake sanda aka haife shi sai da ya jima domin har sun ɗauke tsammanin sake haihuwa, sai kuma daga baya aka haifi Murjana. Yanzu haka Kawu Zubairu shi kuma yana da yara uku ne, dayake tare suka yi aure da Kawu Ali, Ɗiyar sa ta farko me sunan mahaifiyar su Jammatu suna kiran ta Ummi tayi aure har da yara uku don ita ce sa'ar Sajjad, sai kuma Amina itama tayi aure da yaron ta ɗaya da cikin na biyu, ko MEEMA ta girmi Amina, sannan sai Habibah sa'ar Murjana, yanzu suna S.S 3 ne zangon ƙarshe. ✳️✳️✳️ Da aka yi sallan isha'i sai Kawu Ali suka shigo sashin shi da Kawu Zubairu. Sajjad na biye da su a baya Umma ta kawo musu abinci tana cewa, "yau a nan zaka mana hira kenan?" Dariya Kawu Zubairun yayi yace, "a'a yanzun nan zan tafi ai, maganar dai Zulaiha ce muke so muyi yanzu, ina take? Ki kira mana ita don Allah". "To". Tace tana juya wa ta wuce ɗakin Murjana Shi kuma Sajjad dake hakimce a saman kujera yana latsa waya da sauri ya ɗago yace, "Abba to nima ayi maganar mu da ita, wlh da gaske nake yi ina son ta ku aura min ita". "Wace ce yake so ne?" Kawu Zubairu yake tambaya "Wai Zulaiha yake so, idan ba shirmen Sajjad ba ina shi ina yarinyan nan bayan ya san yanda muke da uban ta ƴar tsaman dake tsakanin mu, ai bazai yiwu ma ya kawo ta a matsayin surukata ba wlh, yarinyar da ta gama ɓalɓancewan ta kusan sa'ar shi me zai yi da ita?". Kawu Zubairu yace, "Yaya ni ina da shawaran da zan bayar a game da wannan zancen". A lokacin Umma da MEEMA suka ƙariso wajen Sai Kawu Zubairun yace, "to Sajjad bamu wuri zamu tattauna, kuma kar ka damu idan Zulaiha ce zaka aure ta". "Da gaske Uncle?" Yafaɗa cike da murna "Ƙwarai kuwa, bari zamu yi magana da Abban naka". "To Uncle. Na gode sosai". Ya tashi yana murna, idanun sa a kan MEEMA da ta samu wuri ta zauna bata ce komi ba, killer smile ya saki yana faman ci je baki kafin ya wuce. Ita Umma itama tuni ta wuce cikin nata ɗakin, dama wanka zata yi ta tsaya ajiye musu abinci tunda sun shigo tare "Wai Zubairu me kake nufi wani shawaran ne zaka bayar? Ba dai a kan auren nasu ba don bazai taɓa yiwuwa ba". "Haba Yaya ka kwantar da hankalin ka mana, Ni ina ga wannan ma yana a cikin tsarin mu idan har hanyar da zamu ɓullo be yiwu ba, to kamata yayi ta auri Sajjad idan ya so ko nan gaba sai mu raba ta da komi ya zama mallakin mu, tana ji tana gani kuma bata da yadda zata yi damu tunda a lokacin mun fi ƙarfin ta, tana ƙarƙashin mu dole Sajjad zai san yanda zai yi ya sauya komi da sunan mu. In yaso ma ko ƙara zata kai mu gaba sai mu iya raba ta da duniyar ma". Waro ido Kawu Ali yayi "Ah to abu me sauƙi, kai kana ganin yarinyan nan ba matsala zata zame mana ba?" Jinjina kai yayi yace, "haka ne kam. Amma yanzu mu fara gwada ta mu gani." Sai ya juya da kallon sa ga MEEMA dake zaune still tana ta faman kallon su kamar wacce take fahimtar maganar nasu, nan kuwa ko eh bata fahimta ba illa bakunan su da take ta ƙare wa kallo. "Zulaiha, this is what we called you about your father's assets, you know it is not possible for us as your father's relatives to leave you with these huge sums of money, even if you say that your father owned everything for you before he died then you must We have a share in the property, but now it is not a matter of what we want to do. You can bring everything so that we can turn it over to you. You feel that we are not advising you. It is an order that you will give us everything to hold in our hands." MEEMA da ta tsare sa da idanu tana sauraron sa har ya dire, Bata manta su waye su ba kuma bata manta dalilin da yasa Abee ɗin ta ya mayar da komi nashi da sunan ta ba, dole yanzun ma akwai abin da suke nufi shiyasa ta gyara zaman ta tana cewa, "Uncle's be patient with what I'm talking about, I've already decided what to do with my money, and Abee's companies are selling them all, and I can keep the documents of his house in my hand. I do not need your help..." Wani irin fusata Kawu Ali yayi saboda zancen nata Zai yi magana sai Kawu Zubairu ya dakatar da shi da cewa, "don Allah Yaya ka ƙyale ta, dama nace maka wannan yarinyan shegiya ce mahaifin ta ya rigada ya koya mata yanda zata yi tun kafin ya rasu, kana tunanin bata san manufar mu bane? Ka barta kawai yanzu mu bi ta a sannu idan muka nuna fin ƙarfi zamu iya rasa komi wlh, kuma ka san ba yanda zamu yi mu amshi komi sai da saka hannun ta, takardun filayen kuma ta ce ya mayar da sunan ta ka ga bazai mana amfani ba ko mun ƙwata da ƙarfi". "Haka ne. Amma yanzu ya kake so mu yi? Yanzu kana nufin Mu zuba mata ido da zunzurutun kuɗaɗen nan? Wlh bazai yiwu ba". Kawu Ali yace hakan cikin jin haushi yana sharce zufa "Lallaɓa ta zamu yi mu jawo ta a jiki hakan zai saka ta saki jiki damu, na san zata bamu komi domin mu riƙa juya mata tunda dai ba ita zata kula da wannan dukiyan ba". Sai ya kuma juya wa ya kalli inda MEEMAN take cikin turanci yace, "Zulaiha tunda mu a matsayin mu na Iyayen ki kin ƙi aminta damu kin nuna bamu isa dake ba, shikenan ki ci gaba da riƙe kuɗin idan wani abun ya same ki babu ruwan mu, kin yarda?" Gyaɗa kanta tayi "Ok get and go". Tashi tayi kuwa ta wuce ɗaki "Gaskiya wannan abun be min daɗi ba, yanzu haka zamu zuba idanu sai kace yarinyan ta fi ƙarfin mu?" Kawu Zubairu yace, "Kai yaya ka cika saurin hawa ne, to ya zamu yi kuwa wlh baza mu iya amsar komi ba bare kaf ƙadarorin sa suna wani ƙasa ne, ka ga kuwa ba abu bane me sauƙi ya dawo hannun mu ba, idan baka iya kama ɓarawo ba shi sai ya kama ka, shawaran dai da zamu bi mu haɗa su aure da Sajjad ko tana so ko ba ta so". "Kana ganin hakan zai fi?" "Eh mana hakan zamu yi. Idan ta zama matar sa komi zai fi zuwan mana a hannu babu yanda za'a yi ta tafi tunda da auren ta, shima Sajjad ɗin dole mu sanar masa da komi domin ya san shirin mu, in yaso daga ƙarshe mu raba su ko ya ƙi ko ya so idan mun gama da ita, kana gani fa juya mata dukiyar zamu yi amma ta ƙi amincewa, wannan yarinyan halin su ɗaya da uban ta wlh dole sai mun bi a sannu Ni dai Yaya ina faɗa maka, auren su babu fashi zamu tsayar da time a ɗan ƙanƙanin lokaci, sannan baza mu sanar mata ba har sai a ranan bikin idan an ɗaura, ka ga ba yanda zata yi". Kawu Ali sosai ya amince da wannan shawaran da ya bayar, sai da suka sake tattauna wa sosai kafin ya tafi A lokacin su Umma har sun gaji sun fito suna kan dainning suna cin abincin su "Sajjad kira matar taka mana ku ci abincin, ya naga bata fito ba?" "Wow Abba ka amince zan aure ta?" Murmushi yayi yace, "My son kenan, ka taɓa ganin kun nemi abu kun rasa ne? Ai da yardan Allah Zulaiha matar ka ce, sai dai ban ce ka sanar mata ba har sai an ɗaura auren naku, zamu tsayar da lokaci nan ba da jima wa ba don haka sai ka shirya zama ango nan kusa". Ihu ya saki tsaban murna ya rungume Umma ya haɗa da Murjana ya matse su yana ci gaba da murna "Kai wai lafiyan ka ƙalau kuwa? Dalla sake Ni". Inji Umma tana ɓanɓare shi, sai kuma ta dubi Abban tace, "wai me kake cewa? Ni fa gaskiya ban amince ya auri yarinyan nan ba, haba Abban Sajjad kai ne kuma da faɗan hakan bayan kai zaka fi kowa ƙin auren?" "Jamila zo ki zauna ki zuba min abincin nan, idan muka gama sai muyi magana in fahimtar da ke." Bata ce komi ba dai ta taso ta nufi inda yake ta soma zuba masa abincin Shi kuma Sajjad tuni ya wuce da sauri ya burma ɗakin Murjana don kiran MEEMA, har wani tsalle yake yi tsaban farin ciki. _Rashin Comments zai saka baza ku riƙa samu kullum ba, ba sai na riƙa maimaita muku ba duk sanda ku kaga new update shikenan._ ???????????? *MEEMA FAROUK* ???????????? *NA_NAFISA ISMA'IL* *WATTPAD_UMMUDAHIRAH* *SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT* ???????? *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* ???? ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS????)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ *P.W.A✍️* *SADAUKARWA* _Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._ *KAN MATSALAR KASANCEWA A TSAYE ANA SALLAH* _Rahamar Allah tana isowa, mun samo labarin wani shahararren mai kawo hadisai da ake kira Abu Ishak Subaihi wanda ya rasu yana da shekara ɗari. A kan ji shi yana cewa, "Kash! Wannan rauni na zurfin shekaru ya hana mini more ma doguwar sallah. Yanzu a raka'o'ina biyu Baƙara da Al-imrana kaɗai nake iya karantawa." Su kuwa surorin nan biyu sun kai kamar ɗaya bisa takwas na Alƙur'anin gaba ɗayan su._ _Shi kuwa Hafiz Ibni Ƙayyam yayi nazarin irin fa'idojin da ake samu daga sallah ne ya jero su da cewa, "sallah tana tabbatar mana da samun abincin yau da kullum, ta kawo lafiya, ta kore cututtuka, ta ƙarfafa zuciya gami da faranta ta, ta kawo haske ga fuska, ta sabunta jiki, ta kawar da lalaci, ta haskaka zuciya, ta daɗaɗa ta, ta rage mata jin nauyi kana ta yiwa mutum albishir da rahmar Allah. Tana kasancewa garkuwa ga azabar Allah, tana tsare mu daga shaiɗan ta kuma kusanta mu da Ubangiji. A taƙaice dai; sallah lamuni ne na duk wani abin so kuma garkuwa ce ga duk wani abin ƙi na zuci ko na jiki a wannan duniya ko lahira." Allah yasa mu gama da duniya lafiya Amin ya Allah._ *NO_15* Yana shiga ya hange ta kwance a saman gadon tana latsa waya Bata san da zuwan nasa ba sai da ya zo har gaban ta yana shirin amshe wayan sai tayi saurin firgita tana shirin ƙwalla ƙara Shi kuma ya sanya hannu ya kama bakin nata ya rufe ruf yana dariya Tuni ta yar da wayan tana shirin ƙwace kanta, nan da nan ta ƙwalalo idanu waje domin a tunanin ta wani abun zai mata ta soma Shure-shure zata ƙwace kanta Saurin matse ta gam yayi a jikin sa yana raɗa mata a kunne, "Shiiiiiii! Calm down! I have nothing to do with you." Amma ina bata saurare sa ba sai son ƙwace kanta take Yi tana son buɗe bakin ta da ya ɓame mata ɓam While Iya ƙarfin sa ya riƙe ta ya ƙi saki, musamman yanda ya ji skin ɗin ta kamar ya tamke mage sabida tsaban taushi da yake dashi, har wani santsi yake yi, hakan ya ja hankalin sa da jin wani irin feelings ya sake manna ta a jikin sa yana shinshina mata fuska Nan da nan ta soma kokuwa da shi iya ƙarfin ta har hawaye sun soma wanke mata fuska tsaban yanda ta tsorata ainun To ƙarfin su ba ɗaya ba sosai ya sanya mata ƙarfin sa ya mayar da ita kan gadon ya danne ta yana cewa, "Babe there is nothing I can do for you, I say calm down ok?" Sai numfashi take sauke wa sabida yanda tagalabaita a ɗan kokawan nan da tayi, because kasancewar ta ƴar hutu bata saba wahala ba shiyasa abu kaɗan a wurin ta aiki ne, idanuwan ta kuwa kamar za su fito waje tsaban zaro su da tayi Killer smile ya saki yana sake matse ta sosai har ƙirjin su yana haɗe wa, a hankali ya kai fuskar sa saman nata fuskar yana son kissing ɗin ta a forehead still yana liƙe da bakin ta gudun kar tayi masa ihu. Muryan Abban sa ya ji yana kiran sunan sa. Dalilin da ya sanya ya dakata yana me kallon cikin idanun ta in a cool voice yace, "Babe I'm sorry I didn't do this to spoil you, i love You so Much I will not do it again ok?" Kallon sa kawai take yi idanuwan ta suna zubar da ƙwalla ko ƙyafta su ta kasa A hankali ya janye hannun nasa still idanun sa cikin nata Har ya janye bata sake motsa wa ba illa numfashi da take ta faman sauke wa akai-akai, tana ganin ya sauka daga jikin ta tayi saurin tashi da gudu zata shige Toilet Hannun ta ya riƙe gam yana cewa, "Where are you going again?" "Please let me go, I do not want to". Tafaɗa tana hawaye tana son ɓanɓare hannun nasa "Ok, I'll let you go, but let's go and eat." "No I'm not hungry". Ta sake faɗa tana ƙwaƙule hannun sa da ƙarfi Be ce komi ba ya riƙe ta ya janyo ta suka fice Da kallo su Abba suka bi su baki sake "Kai lafiya me kayi mata Son? Meye haka?" "Abba babu komi wlh, ta ƙi zuwa ne shi ne na janyo ta". Yafaɗa yana isa har wajen dainning ɗin ya ja mata kujera yace, "sit please". MEEMA dake faman zubar da hawaye zama tayi kawai tana bin sa da kallo kamar zata maƙure sa don baƙin ciki Umma tace, "Ni ban san irin ka ba Sajjad, wlh zan saɓa maka idan ka cika shiga shirgin yarinyan nan, ina ruwan ka da ita ne?" "Umma kina so in barta da yunwa ne bayan mata ta ce? Abba kana ji ko?" Yayi maganar kamar zai yi kuka Abba yace, "kyale ta My son, amma ka dena mata abin da bata so kaji tunda ta nuna ba ta son zuwa ka barta mana. Idan ba haka ba zata tsane ka". "To Abba zan dena bazan sake ba". Sai ya kalli MEEMAN da har yanzu take zubar da hawaye yace, "sorry My Angel I will not do it again, let me serve you". Ya ƙare maganar yana rawan jiki wajen serving ɗin ta Murjana dake zaune a kan dainning ɗin tashi tayi tana jan tsaki tace, "amma wlh Yaya kaji kunya na rantse da Allah, ji be yanda kake mata bauta kamar zaka haɗiye ta?" Be kula ta ba shiyasa ta sake jan tsaki ta wuce wajen su Abba dake Parlour'n ta zauna tana cewa, "umma akwai matsala fa, dole sai kin shiga tsakanin Yaya da wannan yarinyan, idan ba haka ba wlh kina gani zai zama mijin tace". Umma da damuwa ta kalli Abba tana cewa, "ka gani ko abinda nake gudu kenan, don Allah ji be yanda yake ɓarin jiki Abban Sajjad?" Abba yace, "ke dai Jamila ki bar wannan zancen duk na ɗan lokaci ne, idan muka cika burin mu komi zai ƙare". "Ta ya ya? Kana ganin hakan me yiwuwa ne? Ni fa kar azo garin cikan burin ku in rasa ɗana". Abban be kai da magana ba Sajjad ya ɗaga murya yana cewa, "Abba ka ga ta ƙi ci". "To ka ƙyale ta mana uwar ka ce?" Umma tayi maganar a fusace "Zulaiha eat the food ok?" Inji Abba cikin kwantar da murya Girgiza masa kai tayi alamun baza ta ci ba "I said eat I don't want to argue." Dole a wannan lokacin ta soma ci ba tare da ta sake cewa uffan ba, dama yunwa take ji kuma abincin ba daɗi yake mata ba, shiyasa idan ta Kai spoon ɗaya sai ta ɗau soconni take sake kai wani Sajjad da ya saka ta a gaba yana kallon ta har da murmushi sai yace, "Babe don't you enjoy the food? What do you want to bring you now?" Bata ɗago kai ba bare ta kalle sa gaba ɗaya zuciyar ta tsanar sa take ji a ranta, ko kaɗan ba ta ƙaunar ta kula sa shiyasa tayi masa shiru, tana sake kai wani spoon ɗin baki ta tashi ta ture kujeran zata tafi Shima biyo bayan ta yayi kamar jela yana tambayar ta, "did you finish?" Abba ya kira ta yace, "come and sit here, I ask you". Zuwa tayi ta zauna tana sake haɗe rai fuska a kumbure Umma da Murjana sai aikata mata harara suke yi kamar za su make ta Shi kuma Sajjad tuni ya zo ya zauna kusa da ita yana kallon ta Abba murmushi yayi yana kallon ta yace, "Daughter I know our country is very happy for you. Are you happy to be here?" Tura baki tayi gaba bata ce komi ba "Ok, since you refuse to talk, I want you to say what you need, so that tomorrow it will be brought to you". "I don't want anything". Tayi maganar tana tashi tsaye zata wuce, sai kuma ta juyo fuska babu walwala tace, "I need Simcard". Kafin ma Abba yayi magana Sajjad yayi saurin tsagal ɗin cewa, "Abba ina da sabon Simcard a ɗaki na bari in ɗauko in bata". Ya ƙare maganar yana tashi da rawan jiki ya wuce ɗakin sa Shi kansa Abba abubuwan da Sajjad ɗin yake yi ya soma ba shi mamaki da tsoro, sai ya ɗan yi murmushin yaƙe yana kallon MEEMA yace, "Let your brother take it." Koma wa tayi ta zauna ba tare da tace uffan ba Umma tace, "Abban Sajjad wlh abun da Sajjad yake yi ya fara yin yawa". "Jamila Ni kaina na ga hakan, amma ki sani wannan yarinyan bilonia ce shiyasa kika ga nima ban ɗauki mataki a kanta ba, dukiyar ta kawai muke so daga nan mu kore ta". "To ku amshi kuɗin mana meye na tsaya wa lallaɓa ta?" Umma tafaɗa a fusace "To ta ya ya zamu amsa bayan kafin mahaifin ta ya rasu sai da ya mallaka mata komi? Yanzu ko mu kan mu bamu da damar amsar gadon mu, kuma kin ga ba nan Nigeria bane idan muka ce zamu amsa ta tsiya ƙarshe kulle Kan mu zamu yi, can suna da doka ba irin nan bane, duk ƙadarorin sa suna can babu damar mu siyar da su a can sai da saka hannun ta da kuma yardan ta". Sajjad ɗin ne ya ƙariso wurin da sauri ya miƙa mata Simcard ɗin Amsa kawai tayi ta tashi ta wuce Umma tace, "kai Sajjad wai me ka gani a jikin yarinyan nan ne da kake ta rawan ƙafa a kanta?" "Wlh Umma ban taɓa son wata yarinya a duniya kamar Zulaiha ba, ina son ta sosai, don Allah Abba idan za'a tsayar da ranan auren mu a saka nan kusa kafin in koma karatu na na master's sai mu tafi tare". Riƙe baki Umma tayi da cewa, "Iyeeeee Sajjad". "Umma kema kin san halin Sajjad, Ni wlh gaba ɗaya na tsani yarinyan nan gaskiya Abba a hana sa auren ta.." Kafin ta ƙarisa maganar ma Sajjad ya bige mata baki, "ke ki kama kanki Allah zan tattaka ki ina wasa dake ne?" Yayi maganar yana wani zazzare mata idanu Ita kuma kuka ta saka ta hau shura ƙafafu Abba yace, "meye kuma na dukan ta My son?" "Abba baka ji me take cewa bane? Idan ba ta son ta ai Ni ina son ta, Kuma wlh idan ta sake zan fasa bakin ne". Ya ƙare maganar da tashi ya wuce ɗakin sa "Ke ma kiyi hakuri da Allah ba fa wani dukan ki yayi ba kina wani ɓare wa mutane baki". Inji Umma tana kallon ta Tashi Murjanan tayi tana bubbuga ƙafafu ta wuce ɗaki tana cewa, "ai dama kun fi son shi wlh, kuma bazan yarda ba sai na rama". Tana shiga ɗakin MEEMA dake kwance a kan gado tayi saurin ɗago wa saboda a tunanin ta ko Sajjad ne, ganin ba shi bane sai ta mayar da kanta ta ci gaba da waya da Esha da ta kira ta suna gaisa wa Dogon tsaki Murjanan ta ja tana wuce wa Toilet, tana fito wa ta haye saman gadon tana sake jan tsaki kamar wacce tsaka ta haifa, "dole ne ma a raba mana ɗaki don bazai yiwu in riƙa kwana da ita ba, shegiya kawai da wani fuska sai kace na mage". MEEMA na jin ta sai dai dayake bata san me take cewa ba wayan ta kawai take yi, sai da duk ta kira su Ummu Hani da Zamiya suka gaisa kafin ta ajiye wayan tayi addu'a ta shafa ta gyara kwanciyar ta, rufe idanuwan ta tayi zuciyar ta duk babu daɗi, bata jin ko wani irin farin ciki a cikin ta, tana ji baza ta iya zama a gidan nan ba Sajjad na mata abun da ya ga dama, sosai take jin tsoron kar ya zo yayi mata wani abun, shiyasa take ta saƙa da warwaran hanyar da zata ɓullo, ko kaɗan zaman gidan ba ya mata daɗi tunda ta fahimci kamar ba ƙaunar zaman ta suke yi ba, musamman ma Murjana da Umma da suke mata wani kallo, ga kuma Sajjad dake son takurata, tana ga idan babu hali dole zata koma can Riyadh, gwara ta zauna a can zai fi mata, amma kuma abu ɗaya ke hana ta tafiya saboda wasiyyan mahaifin ta, umarni ya bata ta koma wajen mahaifiyar ta ta zauna da ita, but ko kaɗan ba ta ƙaunar sake tozali da Ummeen ta har ta koma ga mahalicci, ta tsane ta sosai a zuciya shiyasa ta ga gwara ta zo wajen dangin Mahaifin nata ta zauna tunda zaman ta a can ne be son tayi ita kaɗai, sai dai a yanzu ɗin tana ganin dole ta nemi layin Ishaq ta ba shi haƙuri ya taho nan ya aure ta ta bi shi, hakan shi ne maslaha a rayuwar ta don baza ta iya zama a cikin Nigeria ba, har yanzu ƙasan be mata daɗi ba, but idan ta auri Ishaq sun koma can hakan ba yana nufin ta ƙi bin umarnin Abee ɗin ta bane. Share hawayen fuskar ta da tun ɗazu suka soma sintiri tayi tana gyara kwanciyar ta, ƙanƙame jikin ta tayi tana sake jin kewar Abee na ratsa mata zuciya, da ace yana da rai da ba haka ba, komi nata na farin ciki ya ruguje, ba ta tunanin akwai ranan da zata sake farin ciki da walwala babu Abee ɗin ta, Abee shi ne farin cikin ta kuma ya tafi ya barta, rayuwar ta gaba ɗaya ta ruguje tun tafiyan Ummee, shiyasa gaba ɗaya laifin alhakin mutuwar Abee take ɗaura shi a kanta, ita ta kashe mata Abee ɗin ta da a yanzu suna tare cikin ƙaunar junan su, baza ta taɓa yafe mata ba. Daƙyar a daren barci ya ɗauki MEEMA tare da mafarkai kala-kala. ???????????? *MEEMA FAROUK* ???????????? *NA_NAFISA ISMA'IL* *WATTPAD_UMMUDAHIRAH* *SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT*???????? *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* ???? ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS????)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ *P.W.A✍️* *SADAUKARWA* _Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._ *TUNATAR WA* _Kamar yadda sallah take ibada ce ta ruhu, haka nan muka lura cewa wajen yin ta jikin yakan sami babban ƙarsashi saboda motsa shi da ake yi. Ƙwararrun masana wasannin motsa jiki sun yaba da abubuwan da sallah ta ƙunsa, harkokin nan daban-daban waɗanda ake nanata su a cikin raka'o'in Sallah. Wadannan harkoki ba su barin wata gaɓa a jikin mutum mai Sallah sai sun motsa ta. Watau dai, yadda musulmi suke samun ibada ta ruhu a cikin sallah, haka nan ma suna samun amfani babba na motsa jiki._ _lada da fa'ida da mai yin Sallah zai samu kenan. Ina hukuncin wanda ya yi watsi da ita, ya ƙi bari ta zame masa garkuwa?_ _Duk wanda ya juya wa sallah baya ya guje wa Musulunci, ya saɓi Ubangijin sa. Ya karya dokokin imanin sa, ya kuma kama hanyar halaka. Duk ayyukan sa na ƙwarai sun ɓalɓalce don kuwa ya kauce wa umarnin Ubangiji game da Sallah - duk wanda ya saɓa ma Allah tamkar ya ce ba shi ne ma, domin kuwa ai da ya amsa cewa akwai Allah ai ba shakka da ya bi umarnin sa, kamar dai yadda yace, a cikin Alƙur'ani mai tsarki:_ *"Kuma ku tsayar da Sallah. Lalle sallah tana hanawa daga alfasha da abin ƙi"* _Suratul Ankabut, aya ta 45._ Allah yasa mu dace. *NO_16* *WASHE GARI* MEEMA na cikin barci ta ji ana shafa mata face, tana buɗe idanuwan ta suka faɗa cikin na Sajjad dake durƙushe a gaban gadon ya tsira mata idanu, da sauri ta sake zaro idanun nata don sake gasgata shi ɗin ne a lokaci ɗaya tana me tashi zaune "Good morning my love." Yayi maganar yana mata murmushin sa me kyau Bata iya amsa wa ba kuma bata cire idanun ta a kan sa ba, sai ma tamke kyakykyawar fuskar ta da tayi tana mishi mugun kallo Tashi yayi ya zauna a gefen ta, kana ya saka hannun sa zai riƙe nata Tayi saurin daka masa tsawa tana janye hannayen nata, "don't touch me again". "Why dear?" Yayi maganar kamar zai yi kuka Tashi tayi daga kan gadon tayi hanyar Toilet ta shige Da kallo ya bi ta kamar zai haɗiye ta tsaban yanda tayi masa kyau a cikin guntun rigan barcin nata, ko kaɗan ya kasa ɗauke ido a ƙofan har sanda ta fito Ganin sa a zaune har yanzu sai ta ɗauke kai kawai tana sake haɗe fuska, wajen Trolly ɗin ta ta nufa ta ciro towel da abubuwan da zata buƙata ta sake shige wa Toilet ɗin Sajjad buga tagumi kawai yayi still idanun sa a kan ƙofan ya ƙi ko gezau. A lokacin da ta fito ai sandare wa yayi ganin ta daga ita sai towel, gaba ɗaya santala-santalan cinyoyin ta a waje suke Ita kanta bata yi tunanin zata sake ganin sa ba kasancewar ta ɓata lokaci a cikin Toilet ɗin, da sauri ta ja ta tsaya tana kallon sa cike da haushi, "I will prepare. Please Get out." Numfashi ya sauke sabida jin daddaɗan muryan ta a kunnen sa, yanda yake ji a jikin sa bazai iya magana ba shiyasa a hankali ya taka ya fice a ɗakin har yana sake waigen ta, ji yake yi kamar ya koma ya haɗa jikin su wuri ɗaya tsaban feelings ɗin da yake ji Ita kuma yana fita ta ja dogon tsaki ta nufi kayan ta, gaba ɗaya zuciyar ta ba ta mata daɗi har ta gama shirin ta cikin wata doguwar riga fara ne wuyan love, rigan Robber ce gaba ɗaya ta bi ta lafe mata duk ta fito mata da shafe ɗin jikin ta, dayake akwai ɗan guntun Hijab ɗin sa maroon color da aka yi design da less a ƙasan, shi ta saka ya tsaya mata a iyakan kafaɗa, da agogon ta da flet shoes ɗin da ta sanya duk na kayan ne white color, tayi kyau sosai duk da fuskar ta babu abun da ta sanya, wayan ta dake ajiye ta ɗauka ta fita Parlour Babu kowa sai Sajjad dake zaune. Yana ganin ta ya tashi tsaye idanuwan sa kamar za su faɗo a kanta, tsaban kyan da tayi masa tamkar ya je ya haɗiye ta haka yake ji, sosai MEEMA take da mugun kyau shiyasa gaba ɗaya ta zauta shi ya koma kamar wani soko a kanta, shiyasa ko barcin kirki ba ya iya samu sabida rashin kula sa da take yi, ba zai iya haƙura da ita ba a rayuwar sa, tabbas idan ya rasa ta mutuwa zai yi domin be taɓa ƙaunar wata mace ba sai ita, duk da yana da tarin ƴan mata domin Sajjad na mata ne but sai dai ya gara su be san cewa akwai ranan da wata mace zata shiga zuciyar sa kamar yanda MEEMA tayi ba... Idanuwan sa ya lumshe sanda ta gifta sa ta wuce ƙamshin daddaɗan turaren ta na Arab ya bugi hancin sa. Ya buɗe su yana bin bayan ta da kallo har ta zauna a saman dainning. Wani irin numfashi ya ja nan da nan idanun sa suka soma kaɗa wa, bazai iya jure wa ba dole ya nufi inda take shima ya ja kujera ya zauna, kamar zai yi kuka tsaban yanda yake kallon ta yace, "Zulaiha". Kallon sa tayi sanda ta kai tea Cup bakin ta, ido cikin ido suke kallon juna sai dai fuskar ta a tamke yake tun zaman sa a wurin ta sake haɗe wa "I love You, why don't you love me?" Kawar da kanta tayi bata iya cewa komi ba taci gaba da shan tea ɗin, sosai yake tururi but haka take kaiwa baki tana kurɓa a hankali Sai shima yayi shirun ya sanya mata idanu zuciyar sa babu daɗi Wayan ta ta ɗauka ta soma latsa wa still tana kurɓan tea ɗin, Numban Ishaq ta rubuta sannan tayi dealing but switch off, tsaki ta ja tana ajiye Cup ɗin ta tashi tsaye ta wuce Har ta kusa shiga ɗaki Umma da ta fito a nata ɗakin ta kwaɗa mata kira Hakan yasa ta tsaya tana kallon ta, sai kuma ta buɗi baki a hankali tace, "Morning Mom". "Kar ki koma ɗakin nan ki zo ki gyara mana parlour, sannan ki shiga kichen ki ɗaura mana girki". Ita dai MEEMA tsaya wa tayi tana kallon ta bata ce uffan ba tunda bata san me tace ba Sajjad da ya taho wurin ya kalli Umman yace, "Umma wani girki kuma? Haba Umma daga zuwan nata tana baƙuwa sai ki saka ta aiki? Ni gaskiya baza a saka min mata aiki ba". "Sajjad ka fita ido na tun kafin in nuna maka fushi na, idan bata yi aikin ba haka zata zauna mana a gida sai dai muyi mu bata taci tayi kashi kamar wata uwar mu?" Sai kuma ta juya ga MEEMAN tace, "ke ko baki ji abinda nace bane kin tsaya kin wani kafa min idanu kamar wacce zata haɗiye Ni?" Sajjad yace, "to ai bata san me kike cewa ba ko kin manta ba ta jin Hausa ne?" "Ohh! To sai ka sanar mata da abun da nace". Juya wa MEEMAN tayi kawai zata shige ɗaki Umman tayi saurin janyo ta tace, "babu inda zaki shiga dan uban ki, na ce ka sanar mata ko?" Ta ƙare maganar da daka wa Sajjad ɗin tsawa "Umma yawa fa kike yi wlh, haba don Allah baki ga yanda take bane taya zata iya wani aiki? Kema daga gani kin san ƴar hutu ce baza ta iya waɗannan aikin ba Gaskiya, don Allah Umma kiyi hakuri ki barta". "Iyeeeee Sajjad Ni kake faɗa wa haka don uban ka? Wato ta zauna sai dai Ni nayi ita tana luƙume a ɗaki saboda ita ƴar hutu? To nan ba gidan uban ta bane wlh idan har tana son zaman ta a gidan nan dole ne sai ta yi min bauta". Ta ƙare maganar tana jan hannun MEEMAN da cewa, "ai dole ki gane idan na tasa ki gaba". Da sauri Sajjad ya riƙe Umman yana cewa, "don Allah Umma ki sake ta wai meye haka ne? Ni zan yi aikin a madadin ta ki sake ta". While MEEMA kallon su kawai take yi zuciyar ta kamar ta fito tsaban baƙin ciki, ganin Umman ta ƙi sakar ta sai ta ƙwace hannun ta idanuwan ta har sun soma cika da hawaye, bata ce komi ba ta juya ta shige ɗakin Nan Umma ta yunƙura zata bi bayan ta tana kiran sunan ta But Sajjad ƙiri-ƙiri ya tare ta ya hana ta wuce wa, "haba Umma haba Umma ki ƙyale ta". A fusace tace, "to bari uban naka ya dawo barin gidan nan zata yi". Sai ta wuce fuuu ta nufi kichen Shi kuma ɗakin Murjanan ya wuce zai shiga, sai dai MEEMAN ta garƙame ƙofan da keey, dole ya haƙura ya wuce nasa ɗakin. MEEMA bata buɗe ɗakin ba har sanda ta ji muryan Murjana kafin ta zo ta buɗe mata ta juya ta koma Da kallo Murjana ta bi bayan ta tana ƙare wa rigan jikin ta kallo, har ta shiga ciki ta kasa ɗauke ido a kan rigan domin yanda take matuƙar son irin rigan a rayuwar ta, sai dai har yanzu bata mallake sa ba don har kasuwa suka je a lokacin ita da Habiba but basu samu ba, dole suka haƙura tunda a lokacin sun so suyi ankon ta ne sanda za'a yi auren Amina. Cire kayan ta tayi ta sanya riga da skert na atamfa kafin ta fice ɗakin. Can sai ga ta ta shigo a lokacin MEEMA ta buɗe Trolly ɗin ta ta ciro computern ta ta koma ta zauna. Tsaki ta ja tana ɗauke kai daga kallon ta Ita kuma MEEMAN sai a lokacin ma ta ɗago da idanun ta ta dube ta, kawar da kai tayi ta ci gaba da abin da take yi While Murjana tuni ta sake fice wa tunda dama wayan ta ta dawo ɗauka Fitan ta babu daɗe wa Habibah ta shigo tana kiran sunan MEEMAN fuskar ta ɗauke da fara'a Itama ganin ta yasa ta tsayar da abinda take yi tana murmusawa "Sister I miss you so much, I can't bear to say let me come and see you." Tayi maganar bayan ta zauna a gefen MEEMA ta riƙe hannun ta Sitll da murmushi a fuskar ta tace, "me too". "But your dress looks good on me, and it looks great on you. You are so beautiful." Kallon ta kawai tayi bata ce komi ba illa murmusa wa da take yi "Aren't you working? Because we're going to our Part today stay for us there, I'll be happy with that". Jinjina kanta tayi kafin tace, "ok I will go". Ta ƙare maganar da rufe computern tana ɗauka ta tashi ta mayar a cikin Trolly ɗin ta, sai ta zaro irin rigan dake jikin ta sak sai dai shi blue color ne, ta kalli Habiban dake zaune tace, "take it's for you". "Wow! Thank you so much. Thanks again". Tafaɗa cikin farin ciki bayan da ta taso ta amsa rigan "Don't worry there is no gratitude between us." Itama MEEMAN tafaɗa cikin murmushi kana ta mayar da Trollyn ta rufe sannan ta tashi tana kallon ta tace, "ok let's go". Suna fita Habibah da ta hangi Murjana zaune a kan dainning, da gudu ta isa wurin ta tana shaida mata kyautar rigan da MEEMA ta bata Yayinda MEEMAN ke tsaye a wurin da ta barta bata motsa ba tana kallon su, sai dai a yanzu ɗin murmushin fuskar ta ya gushe Ita Murjana taɓe baki tayi cike da isa tace, "ai yayi miki kyau tunda kin je kin roƙe ta kin zubar mana da mutunci, ke dai wlh Habibah baki yi ba a rayuwa". Sai ta ja tsaki tana banka mata harara ta mayar da hankalin ta kan abincin ta Habibah da ta saki baki tana kallon ta sai tace, "to fa! Gaskiya Murjana akwai gyara a lamarin ki, har yanzu baza ki dena wannan ɗabi'an naki ba bayan kin san da cewa ita ƴar uwan ki ce, to Ni meye ma a wuri na don na roƙe ta ai kin san Ni ba irin ki bace domin ba Ni da girman kai". "To kar dai ki gaya min magana don Allah ki tashi min akai". Tsaki kawai Habiban ta ja tana juya wa ta wuce wurin MEEMAN da har yanzu idanuwan nata a kan su suke, bata iya mata magana ba sai jan hannun ta da tayi suka fice. Suna fita Murjanan ta tashi da sauri ta nufi ƙofan ta leƙa su, ganin da tayi sun bi hanyar Part ɗin su Habiban sai ta koma ta rufe ƙofan ta wuce ɗakin ta da sauri, tana shiga ta nufi wajen Trollyn MEEMAN ta saka hannu zata buɗe. Share this [ad_2]