MEEMA FAROUK 1-END

MEEMA FAROUK Page 31 to 40

“Yunwa kuma Baby?” Yafaɗa yana ware ido

Ta gyaɗa mishi kai

“To baku ci abinci bane? Hafsah baku ci komi bane da kuka dawo school ɗin?”

Hafsah tace, “mun ci Dady, Momy ta saka Talatu ta girka mana kus-kus amma ita bata ci ba.”

Fuskarsa ne ta nuna alamun damuwa, sai dai yayi shiru be ce komi ba

Hakan da Luwaira ta gani ne sai tayi saurin cewa, “Yaya bari in dafa mata a nan tunda yunwa take ji. Me zaki ci in dafa miki?” Ta ƙare maganar da kallon Yusran tana mata murmushi

“Indomie zan ci.”

“Nima zan ci Dady ta dafa har da Ni.” Cewar Hafsah cikin sauri

“To kuna so ku mayar da ƙanwata kukun ku ne? Basu takura miki ba ko sister?” Yayi maganar yana kallon fuskar ta

Murmushi ita kuma tayi tace, “haba dai a’a wlh, ai babu damuwa, bari in je in dafa musu.”

“Ok thanks my Sister. Nima ban san meyasa Kukun su har yanzu be dawo bane, ina tunanin zan sama musu wani.”

Luwaira ita dai tuni ta tashi ta nufi kichen. Hakan yasa Hafsa ta bi ta tana tsalle-tsalle

While Yusra ita kuma ƙara maƙalewa a jikin sa tayi

Shafa kanta yayi kafin ya ci gaba da latsa computern shi, jefi-jefi yana ɗago kai yana mata magana yana hura mata iska a fuska ganin tana wani lumshe idanu

Hakan yasa ta ɗan dawo da kuzarinta ta saki jiki har tana dariya. Ta soma tsalle a jikin sa kamar yanda ta saba

  

Ɓoyayyen ajiyan zuciya ya sauke ganin ta saki jikin ta sosai. Ya san duk da yunwa ya mayar da ita haka, ko daga kallon ta zaka gane ƙarfin hali kawai take yi saboda Yusra akwai ci ba ta wasa da cikin ta, abu kaɗan ke saka tayi wani yaushi da ita tunda ta kasance me son gazar-gazar. Shiyasa yake matuƙar ƙaunar yarinyan saboda sak mahaifiyar ta ne, har lukutin jikin ta na Nusaiba ne.

*Nayi iya yi na wajen sanar muku ina buƙatar more comments but har yanzu You don’t changes, I’m very tired! from today insha Allah I will not posted again. Nima ina bukatar Comments ɗinku domin shi ke saka Ni naji daɗi a raina har na tabbatar da cewa ana karantawa, ko Thanks ka rubuta min zai tabbatar min kana karantawa, amma yanzu na gane babu masu bukata insha Allahu na dakata daga yau sai kuma sanda Allah ya waiwayo Ni. Bissalam ???????? Ina ma Real masoyana Barka.*

 

???????????? 

*MEEMA FAROUK*

                        ????????????

*NA_NAFISA ISMA’IL*

*WATTPAD_UMMUDAHIRAH*

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT*????????‍

*PERFECT WRITER’S ASSOCIATION* ????

“`( WE AIN’T PERFECT, BUT WE’RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS????)“`

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*

                 *SADAUKARWA*

_Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._

                             *NO_27*

             Bayan Luwaira ta gama dafa musu indomien sai ta zubo ta kawo musu parlour’n. Sannan tayi masa sallama ta fice

Shi kuma yana ta faman aikin shi har suka gama cin abincin suka koma wasa da juna. Daga ƙarshe kuma barci ne ya ɗauki Yusra. Hakan yasa ya tashi ya wuce sama inda ɗakin shi yake ya bar Hafsah tana kallon cartoon. Da shigan shi ɗakin inda yake ajiye towul ɗin shi ya nufa ya zari ɗaya ya wuce cikin Toilet. Wanka yayi ya fito sanye da towul ɗin a jikin sa. Kai tsaye gaban mirror ya nufa ya gyara suman kanshi kana ya wuce wajen sif ɗin kayan shi ya zaro wani farin yadi me tsananin haske da taushi, kayan dai-dai jikin sa suke sun masa kyau ainun tare da ƙara haskaka skin ɗin shi, sai yayi amfani da baƙar hula tare da cover shoes su ma baƙi, sannan ya wuce gaban mirror ya feshe ko ina na jikin shi da turaruka masu tsananin ƙamshi da shiga rai, agogo ya ɗauka ya ɗaura a tsintsiyan hannun sa kafin ya zari wayoyin sa guda biyu ya zuba a aljihun wandon sa ya fice da keey ɗin mota a hannu. 

          A lokacin da ya fita falo ya tarar da Hafsah itama tana gyangyaɗi, kai tsaye wajen ta ya nufa ya kira sunan ta. “Baby na KE ma barci kike ji?”

Kanta ta gyaɗa mishi ba tare da tayi magana ba

“To Ni kuma ga shi zan fita. Amma tashi mu je wajen Momy sai ku kwanta a can.”

Tashi tayi shi kuma sai ya nufi wajen Yusra ya ɗauke ta ya aza ta a kafaɗan shi, tare da riƙe hannun Hafsan suka fice. Part ɗin Momy ya nufa yayi Nocking a bakin ƙofan kafin ya tura da sallama a bakin sa ya shiga. Babu kowa a parlour’n don haka ya sauke Yusra a saman kujera ya shimfiɗa ta

Yana cikin gyara mata kwanciya ne sai ga Talatu me aikin Momy ta fito daga kichen. Wajen shi ta nufa tana gaishe shi tare da mishi, “ya jiki?”

Murmushi yayi mata kamar yanda ya saba ya amsa ta cikin mutuntawa. Kana ya tambaye ta, “ina Momy?”

“Tana ɗaki bari in Kira maka ita.”

“A’a ba sai kin kira ta ba, ga su Hafsah nan ki shiga da su ciki suna jin barci ne, idan Momy ta fito ki sanar mata na fita.”

“To ranka ya daɗe!” Tafaɗa cikin girmamawa kana ta matso da zummar ɗaukar Yusran

Shi kuma ya shafa kan Hafsah kafin ya juya ya fice. Kai tsaye haraban gidan ya nufa nan da nan securities ɗin sa suka nufo sa suna kai gaisuwa gare shi. Tsayar da su yayi da hannu kana ya wuce gaban wata farar mota ƙirar jib zai buɗe da kanshi, amma sai ɗaya daga cikin security ɗin ya zo da gudu ya buɗe masa. Sai da ya shiga ciki kafin ya kalle shi fuskar sa a sake yace, “ba na son ku biyo baya na.”

“Amma ranka ya daɗe!…”

Katse shi yayi da cewa, “ya isa. Haka nake buƙata ba na son ku biyo NI zan iya da kai na ok?”

“Ok Sir. Allah ya tsare.” Yafaɗa yana sara mishi. Sannan ya mayar da ƙofan motan ya rufe mishi

Shi kuma ya ja motan a hankali ya fice a gidan.

                       ******

          Momy da ke tsaye a bakin windown ɗakin ta tana kallon duk abin da ke faruwa. Bata saki labulen ba har sanda ta ga fitar Umar Faruk sannan ta ja dogon tsaki tana yarfe labulen. Sai ta koma zagaye ɗakin hannayen ta a goye a baya, gaba ɗaya damuwa ta nuna a fuskar ta kasancewar gani take yi wankin hula na son Kai su ga dare, har yanzu sun kasa cin nasara a kan shi, ga shi abinda suka shirya domin ganin bayan shi hakan be kasance ba, ya tsallake hatsarin da suka shirya mishi yanzu basu san kuma abinda zasu yi ba next? Tunanin Momy duk ya tafi ga matakin da zata ɗauka a kanshi. Ya zata yi? Zuciyar ta tana bijiro mata abubuwa da dama a ranta wanda har yanzu ta kasa yanke ƙwaƙwƙwaran makaman abin da zasu yi. Maganar Abdul ne ya faɗo mata a rai sai ta saki dogon numfashi tana komawa bakin gado ta zauna tare da tsirawa waje ɗaya ido. ita yanzu abinda ke damun ta kar yace zai auro wata ya kawo ta cikin gidan nan kamar yanda take buƙata, duk da ba har zuci take mishi maganar ba amma ba ta son ya sake aure, gaskiya akwai matsala dole ta samo mafita, amma kuma ba ta so ɗiyarta ta aure shi domin dole nan gaba zata rasa shi, “amma kuma idan dogon burin ki zai cika fa?” Wata zuciyar ta tambaye ta haka.

✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️

           A hankali yake tuƙin motan cikin ƙware wa, duk da tuƙin yake yi but hankalin shi gaba ɗaya ya tafi ga tunanin abun da ke zuciyar sa, shiyasa lokaci-lokaci yake fuszar da iskan bakin shi yana ɗan dukan sitiyarin motan kaɗan-kaɗan a haka har ya kai gidan Hajiya. Ya danna horn me gadi ya fito

Ganin da yayi Umar Faruk ne sai ya koma ya buɗe mishi Gate ɗin ya shiga da motan

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button