MEEMA FAROUK Page 31 to 40

Parking space ya nufa ya faka motan
Da gudu me gadin ya taho ya buɗe mishi ƙofan yana washe baki da faɗin, “Barka da zuwa ranka ya daɗe!”
Murmushi yayi mishi yace, “Yauwa. Kana Lafiya?”
“Alhamdulillah ranka ya daɗe!” Yafaɗa cike da fara’a kamar zai duƙa mishi
Shi kuma fitowa yayi a motan kafin yace, “Allah yasa Captain yana nan?”
“Eh yana nan don yanzu ya dawo gidan ma.”
“Ok.” Yace dashi sannan ya saka hannu a cikin aljihu ya zaro sabbin kuɗi ƴan dubu ɗaya ya ba shi
Nan ya soma mishi godiya kamar zai je ƙasa don duƙa masa
Shi kuma murmushi yayi yace, “kar ka damu ka dena min godiya.”
“Ai ranka ya daɗe! Dole ne. Allah ya ƙara buɗi yasa kafi haka, Allah ya tsare ka da duk kan sharrin maƙiya.”
“Amin Amin.” Ya amsa shi cike da jin daɗi kana ya wuce ya tafi. Kai tsaye ƙofan shiga parlour’n ya nufa yayi Nocking
Babu jima wa sai ga Uncle Hashim ya fito yana waya. Ganin shi yasa ya waro ido waje yana kashe wayan kana ya ba shi hannu tare da cewa. “ah ah patient ɗin mu ne a nan? Ya aka yi haka?”
Murmushi yayi ya miƙa mishi hannun suka cafke kana yace, “Ai naji sauƙi Malam.”
Matsa mishi yayi ya shigo sannan ya rufe ƙofan suka shiga Parlour
Zabba’u da Jalila ne zaune a parlour’n. Don haka suka soma gaishe shi Zabba’u na faɗin, “ikon Allah har ka samu sauki da zaka fara yawo Umaru?”
Murmushi yayi yana zama
Shi kuma Uncle Hashim yace, “nima abun da na gani kenan. Yau fa aka sallame ka? Gaskiya zan ɗau mataki a kan masu tsaron ka da har suka bar ka ka fito, i know Momy bata san ka fito ba?”
“Haka ne. “But I’m relieved. I came to greet Hajiya.”
“A’a ai baka kyauta ba kuwa. Ina kai ina zuwa gaishe da Hajiya baka da lafiya, itama baza taji daɗi ba, bari in Kira ta.” Cewar Zabba’u tana tashi ta wuce
Ita kuma Jalila tuni ta tashi ta kawo mishi drinks ta ajiye mishi
Godiya yayi mata sannan ya tambaye ta, “ina Habeeb?”
“Yana tare da Ummee a ɗakin ta”.
Fitowar Hajiya itama sai da tayi mishi faɗan zuwan nashi
Shi kuma yace, “ya zo gaishe ta ne kawai.”
Tace, “haba dai Umar. Kana wasa da lafiyan ka dai, amma mene ne na zuwa gaishe Ni bayan yau aka sallamo ka?”
Uncle Hashim yace, “hm Hajiya bar shi kawai.”
Tace, “duk da haka dai mun gode, sai dai ka riƙa kula da lafiyan ka. Ya jikin naka Yanzu?”
“Alhamdulillah Hajiya.”
“Masha Allah haka ake so ai. Allah ya daɗa tsare ku ya taimaki rayuwar ku.”
“Amin Hajiya.” Shi da Uncle Hashim suka amsa
A lokacin Ummee itama ta fito suka gaisa take tambayar shi itama jikin nashi?
Yace, “da sauƙi Aunty.”
“To Masha Allah mun ji daɗi Allah ya tsare gaba.”
Daga nan ɗan hira suka taɓa kafin suka fita da shi da Uncle Hashim zuwa waje. Sai da suka kai baƙin motan shi sannan ya kalle shi yace, “Your daughter is not here?”
“Oh ko dai wurinta ka zo ne? Tell me the truth?”
Murmushi yayi yace, “No Ina tambaya ne saboda ban ganta ba.”
Uncle Hashim yace, “bata dawo daga wajen aiki ba, amma na san yanzu zata shigo tunda three ya kusa.”
“Ok.” Yace yana ɗan kaɗa keeys ɗin hannun sa
“I still don’t trust you Dude, tell me the truth you come to her?”
“Yes. I think about your talk, I want to marry her if there is no problem, because..” sai ya ɗan ja numfashi kafin yace, “because she entered my soul. I love her!”
Farin ciki ne ya bayyana a fuskar Uncle Hashim, cike da tsantsan farin ciki yace, “da gaske kake yi Aboki na?”
“Yes.” Yafaɗa yana gyaɗa mishi kai
“Oh I can’t tell you how happy I feel in my heart, naji daɗin abun da ka faɗa, insha Allahu zan shige maka gaba a kan samun ta, ina bayan ka dude because you fit so well.”
Murmushi kaɗai Umar Faruk yake yi be sake cewa komi ba, shi kansa a zuciyar sa farin ciki ne yake ɗawainiya da shi, yana ga hukuncin da ya yanke hakan shi ne dai-dai, zuciyar sa zata fi aminta da ita a kan ta zame mishi Abokiyar rayuwa, ya san hakan zai faranta ran Momy idan yau aka ce ya je mata da zancen ya samu matar aure duk da be da tabbacin ita MEEMAN zata amince, but yana sa ran hakan
Uncle Hashim yace, “Let’s go back inside and wait for her to come back sai ku gaisa.”
Daga nan gidan suka koma. A nan Uncle Hashim yake sanar wa su Hajiya abun da ke faruwa
Babu wanda be nuna murnan sa ba musamman ma Ummee da ta fi kowa farin ciki, tabbas ta ga dacewar ɗiyarta da Umar Faruk saboda shi Mutum ne me matuƙar kirki, ko ba komi hakan zai kusanta ta da ɗiyarta tunda zata yi aure a nan, kuma tana fatan ta ga auren ta yanzu tunda ta kai girman da ya kamata tayi aure domin rayuwar mu a nan daban da can inda ta tashi, 26/27years ai ya wuce ace har yanzu tana zaune babu aure.
******
Koda MEEMA ta dawo babu wanda yayi mata maganar sai Uncle Hashim, sai yace mata, “she prepares and eat and a visitor comes to her.”
Dayake lokacin yana parlour’n sama an kai shi ya zauna zaman jiran ta
“A visitor came over me?” She asked in surprise
“Yes daughter. Get ready and go find him.”
Ɓata fuska tayi tace, “then Uncle why did you come of me?”
Dafe goshin sa yayi kafin ya kalle ta yace, “daughter please leave your questions and go to him, he will tell you what he has come to do.”
Daƙyar ya shawo kanta da tambayoyin da ta tsare shi da su. Ta ci abinci sannan tayi wanka ta saka doguwar riga kamar yadda ya zame mata jiki, Abaya ce ja da kwalliyan Stones a gaban. Sai tayi Rolling da mayafin
Har zata fita sai Jalila ta shigo ɗakin ta ganta, tace, “Where are you going to go without a make up?”
Ido ta zuba mata fuskar ta da mamaki
Sai ta kamo hannunta ta zaunar da ita a gaban mirror ta soma mata shafe-shafe
Bata ce mata komi ba illa bin ta da take yi da ido. Sai da taga abun ya wuce gona da iri domin ita ta tsani kwalliya sosai a fuskar ta, “no Aunt I don’t want. Leave me alone.”
Murmushi ita kuma tayi tana kallon ta tace, “You’re so beautiful.”
Ɗan tura baki tayi tana kawar da kai
Ita kuma dariya tayi mata ta kamo hannun ta suka fice. Sai da suka fito ta saki hannun nata tace, “Go upstairs he waiting for you”. Daga haka ta juya ta wuce Parlour inda su Hajiya ke zaune
Ita kuma kamar baza ta tafi ba sai kuma ta taka a hankali ta soma hawa matattaƙalan benen, tana zuwa bakin ƙofan da zata shiga parlour’n ta ja ta tsaya, tunani kawai take yi, “Then who came to her?” Bata da me amsa mata tambayar ta hakan yasa ta tura ƙofan ta shige. Sosai gaban ta ya faɗi kawai arba da shi da tayi zaune a saman kujera. Sai ta sake waro ido tana sake duban shi kamar wata status a wurin
Haka zalika shima kallon ta yake yi yana aiyana tsantsan kyawun da Allah ya bata, musamman yanzu da ya ganta da Powder a fuska ta saka kwalli a fararen manyan idanun ta, hakan ya ƙara fito da zallan kyan ta domin be taɓa ganin fuskar ta da kwalliya ba. Yanda ya ga ta tsaya ta ƙi takowa ne sai ya tashi tsam ya isa gaban ta
Idanun ta ƙirr a kanshi har yanzu tana mamakin ganin shi kuma tana son tabbatar da cewa, “Is he her guest?”
“Why did you stop here?” He spoke slowly looking at her
Hakan yasa ta ɗan ƙyafta idanuwan ta tana kawar da su, sai kuma ta sake ɗagowa ta kalle shi, ganin sun haɗa ido ta sake ɗauke kai
Shi kuma murmushi yayi yace, “Let’s go and sit down.” Sannan yayi gaba
Hakan yasa ta taka tabi bayan shi kamar an tsamo ta a ruwa coz yanda take tafiyar. Slowly she sat down in the chair looking at him, sai ta haɗa hannayen ta a saman cinyoyin ta ta dunƙule su wuri ɗaya tana sauraron bugun zuciyar ta da sauyin yanayin da ke baƙuntan ta