MEEMA FAROUK Page 31 to 40

Duk dariya suka yi har su Hajiya da suke hiran su daban
Yayinda ita kuma ta shagwaɓe fuska da cewa. “Uncle I am still a young girl.”
“Really?”
Tura masa baki tayi
Murmushi yayi yana sanya hannu ya ɗan bugi goshin ta
Tace, “oshhh! Uncle it’s hot.”
“You still don’t change my daughter.”
“I also see that she is still unchanged.” Cewar Jalila tana murmushi
Hajiya tace, “Now that you’re back, you’re going to get marry her.”
“No. I’m not going to get married now. I haven’t finished my studies yet. I’m just starting to work and I’ll be long before I get married.” Tafaɗa tana kallon shi
“Well daughter no matter what you say, what you want is what I want too.” Shima yayi maganar idanun shi a kanta yana mata murmushi
Itama murmushin tayi tana sake mayar da kanta a jikin shi
Jalila tashi tayi tana cewa, “Hajiya bari in Kai kayan mu ɗaki.” Ta wuce ta ja Trollyn tayi sama
A lokacin ne Zabba’u ta dawo da Custard ɗin ta gama dama mishi. Ta zauna tana cewa, “to zo ga shi na gama dama maka ka sha.”
Taso wa Habeeb ɗin yayi daga jikin Hajiya ya taho wurin ta. Ita take ba shi da kanta bayan ta zaunar da shi a cinyan ta.
Da haka dai suka kasance a ranan suna tare suna ta hira. Sallah kaɗai ke tayar da su a wurin. Sai da aka gama abinci suka haɗu gaba ɗaya suka ci a saman dainning sannan suka dawo Parlour suka dasa hira.
✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️
“Har yanzu Allah be bamu Sa’a a kan wannan yaron ba, na rasa meyasa har yanzu yake tsallake shirin mu. Yanzu wai ya zamu yi ne?”
“Momy ba fa matsalar mu bane, kin san kwana biyun nan ba ya zama dole baza mu samu damar aiwatar da komi ba, kuma kinga yau gidan cike da jama’a duk masu taya shi murnar samun kujeran nan ne, dole mu jira har sanda komi zai yi sauƙi.”
Tsaki ta ja tana tashi ta soma zagaye. Can kuma ta juyo tana kallon Abdul tace, “yanzu ina Umar Faruk ɗin?”
“Na bar shi da wasu Mutane a waje, ya ce yanzu zai shigo idan suka gama.”
“To ka tashi ka je kar yazo ya tarar da mu a nan.”
Tashi yayi ya fice.
Babu jima wa sai ga Umar Faruk ya shigo parlour’n da sallama
Momy saurin sauya fuskar ta tayi tana murmushi tace, “ah ah my son ƙariko mana ka zauna.”
Taho wa yayi ya zauna a kujeran da ke facing ɗin nata
“Yanzu Abdul ya fita yake sanar min da daddaɗan labari. Ashe har an sanar da zaɓen ne?”
Murmushi yayi da cewa, “A’a Momy akwai saura, mu namu ba’a tabbatar ba dai. Zuwa anjima muke tunanin komi zai kammala.”
“To ai dai tunda kaji haka insha Allahu kai ne da Nasara, na san yaro na bazai wuce shi ne da Nasara ba da yardan Allah. Kai na Mutane ne kamar yanda mahaifin ka shima na Mutane ne, ina da tabbacin kai ne zaka lashe zaɓen nan.”
“Amin Momy.” Yafaɗa cike da jin daɗi
Gyara zaman ta tayi tace, “ya maganar mu da muka yi da kai a kan neman matar aure? Kar ka manta fa yanzu kowa idon shi na kanka, kana da wannan babban matsayin amma ace baka da mata wannan be dace ba, dole ka nema wa su Hafsah mahaifiya ko su ma zasu ji daɗin uwa a halin yanzu, Nusaiba ta rigada ta tafi inda kowa zai je baza ta taɓa dawowa ba. Ba na so Mutane suna ma yaro na kallon ƙaramin mutum wanda zai gaza musu. A kullum da wannan batun nake kwana nake tashi kullum ina cikin zullumi da tunani.” Ta ƙare maganar nata fuskar ta cike da damuwa
Shiru yayi kansa a ƙasa ya gaza cewa komi
“Umar ka duba magana ta komi ina yi ne domin ka, bazan so ace yau duniya tana zagin min ɗa ba, kai ɗana ne wanda nake ji kamar Ni na zuƙuna na haife ka. Mahaifiyar ka ta haife ka ne kawai amma Ni nafi kowa ƙaunar ka. Ina son ka ba na son abinda zai same ka, ba na iya barci a ɗan kwanakin nan tunda ka kama siyasan nan.” Ta ƙare maganar da fashe wa da kuka
Da sauri ya ɗago yana kallon ta jin muryan kukan ta. Sai kuma ya tashi izuwa gaban ta jikin sa har rawa yake yi ya riƙo hannayen ta. “haba don Allah Momy mene ne na kuka kuma? Don Allah ki dena. Duk abun nan da kika ga ina yi; wa nake da shi da zan yi dan shi idan ba ku ba? Bani da kowa sai ku, na rasa kowa nawa amma kun zauna da ni, kin zame min mahaifiya sannan ga ɗan uwa na samu ga kuma ƙanwa duk kin maishe su nawa. Kina nuna min duk ƙaunar da uwa zata nuna wa ƴaƴan ta. Don Allah ki dena kuka na yarda zan yi aure ko domin farin cikin ki ne Momy.” Sai yayi shiru saboda jin hawaye sun cika mishi ido. Daƙyar ya furta. “Zan yi auren Momy.”
Murmushi tayi tana saka hannu ta riƙe nashi hannayen tace, “Allah ya maka albarka my son, Ni dama buri na inga kana farin ciki ne a rayuwa, tunda Matar ka ta mutu ka gaza yin aure wanda hakan be dace ba, kowa yana maka kallon Mutumin kirki ba na son a soma maka akasin haka tunda yanzu ka ga idanun duniya a kanka suke, kana da babban matsayi a duniya, ina son aci gaba da kallon ka a haka. Tashi ka je Allah yayi maka albarka.”
Amsa mata yayi yana miƙe wa tsaye cike da sanyin jiki ya fice. Kai tsaye Part ɗin shi ya wuce ya shiga. Ɗakin yaran shi ya wuce ya duba ya ga suna barci sai ya haye sama inda ɗakin shi yake. Ya shiga ya yiwa kansa masauki a gaban gadon shi. Shiru yayi yana me kama kanshi da hannayen shi biyu. Shi Mutum ne me sanyin hali da rashin son hayaniya, shiyasa ko ya ya ne aka yi wani abu ko ya ɗan samu damuwa a ranshi yanzu sai duk ya rasa kuzarin shi, sai nan da nan kanshi ya soma ciwo har ya rasa sukunin shi, yana da matuƙar sanyin hali da tausayi sosai, abu kaɗan ke ɗaga mishi hankali shiyasa a sanda ya rasa Matar shi tashin hankalin da ya shiga ne ya haddasa mishi ciwon zuciya. Wanda har yanzu fama yake yi da kanshi kullum cikin magani. Ba ya son abubuwan da za suna tuno mishi da matar shi a koda yaushe shiyasa ya kasa ƙara aure yau kimanin shekaru shida kenan. Ta haifi Yusra da kwana ɗaya Allah ya ɗauki ranta sakamakon guban da ta ci a cikin abinci wanda su Momy suka sanya mata.
Nusaiba ta kasance ɗaliban likitanci yarinya ɗaya tilo a wurin mahaifan ta da suka kasance Malamai, a nan Kaduna suke zaune kuma ba wasu masu kuɗi bane, sai dai suna da rufin asiri sosai. Tun Umar Faruk yana karatu a ƙasar Amurka lokacin ya dawo hutu suka haɗu da ita sanda ya kai ziyara wajen wani abokin shi a makarantar su. Kamun kanta da tsantsan tarbiyyar ta yasa Umar Faruk ya faɗa soyayyar ta, domin Nusaiba ba wata kyakkyawar yarinya bace amma akwai ta da tarbiyya sosai, tun tana ƴar shekara goma tayi saukar alƙur’ani me girma. Kuma a sanda ta girma tana koyar da ɗaliban mahaifin ta a makarantar da ya buɗe. Binciken farko da Umar Faruk yayi a kanta wajen abokin shi wanda ya santa sosai. Shi ya tabbatar mishi da Malama ce ita sosai da kuma ƙoƙarin ta. Hakan yasa ya faɗa soyayyar ta kafin komawar shi ƙasar waje. Be yi ƙasa a gwiwa ba da taimakon abokin nashi ya bayyana mata soyayyar shi. Inda cikin ƙanƙanin lokaci suka gina soyayyar su me tsafta har zuwa sanda ya gama karatun shi ya dawo ya aure ta. A lokacin ya rasa iyayen shi domin tun yana yaro mahaifiyar shi ta rasu, shi kuma mahaifin shi ya auri Hajiya Salamatu wacce ita ce Momy, ta zo da yaran ta biyu gidan kuma tayi zama da mahaifin shi na shekara ɗaya kafin Allah ya ɗauki ranshi sakamakon ciwo da yayi. A lokacin Umar Faruk ya sake zama Maraya babu uwa babu uba bare ƴan uwa, sai Momy da ƴaƴan ta da suka nuna mishi ƙauna bisa son mallakar dukiyar shi da suke son yi, ya ɗauke su tamkar jinin shi be taɓa tunanin ba da zuciya ɗaya suke ƙaunar shi ba, be da wasu dangi da suka fi mishi su, duk abinda suke so yana musu kuma yana tsananin yiwa Momy biyayya tunda ya ɗauke ta kamar ita ta haife shi, yana ji a ranshi ya rasa uwa ce amma ita ce ta maye mishi gurbin ta. Sai dai shigowar Nusaiba cikin rayuwar shi sai ta fara fahimtar zagon ƙasar da suke yi mishi, wanda ta so ta fahimtar da shi ba ƙaunar shi ta Allah da Annabi Momy take yi ba amma ina bata ci galaba ba. Lokacin ta haifi Hafsah da shekara biyu ta samu cikin Yusra. Tun lokacin suke tagen yanda za ayi su kashe ta domin ba sa son tazo ta haihu ta sama mishi Magaji na miji, domin shi kanshi so suke yi su kawar da shi a doron duniya su mallaki komi da kuma dukiyar shi, basu ci Nasara ba sai da ta haihu a lokacin tana fama da rashin lafiya sakamakon haihuwar ya zo mata da tangarɗa, suka saka mata guba a cikin abinci ta ci ta mutu wanda ya ja cece kuce a tsakanin likitocin asibiti da ƴan sanda sakamakon a asibiti ta mutu, an gane cewa guba taci sai dai maganar be kai ga kunnen Umar Faruk ba suka san yanda suka yi suka siye ɗan sandan aka binne maganar.