MEEMA FAROUK Page 31 to 40

Mutuwar Nusaiba ya taɓa Umar Faruk sosai domin Allah ya ɗaura mishi ƙaunar ta a zuciya, yana matuƙar son ta kuma yana jin ta a zuciya matuƙa. Mace ce me shiga zuciya bata da hayaniya ko kaɗan, tana da kirki da halin ƙwarai wanda idan har ka zauna da ita dole ne sai ka so ta. Mutuwar ta ya taɓa shi hakan yasa har yayi jinya sabida damuwar da ya saka a zuciya, wanda yanzu ya haifar mishi da ciwon zuciya.
Har yanzu burin su Momy su ga bayan shi amma sun kasa cin Nasara, yanzu haka suna ta shirin yanda zasu kashe shi ne ba tare da an yi zargin kisa bane domin su mallaki komi, mahaifin Umar Faruk wato Alh. Aliyu Bature ya rasu ya bar mishi ɗumbin dukiya har da gidajen mai guda uku wanda ake ji da su a nan Kaduna. Yanzu haka shi Umar Faruk ɗin ya gina babban Company na sarrafa shinkafa wanda shi ke kula da shi tare da Abdul. Sanadin shigan shi siyasa kuma mutanen mahaifin shi ne suka saka shi, tun ba ya sha’awa sai dai ya basu gudummawa domin ya san manyan mutane sosai, har dai a yanzu sun ci galaba inda kai tsaye suka nema mishi kujeran Senata kuma ga shi Allah ya ba shi.
*****
Ajiyan numfashi ya sauke yana miƙe wa tsaye tare da nufan drowan mirror ya buɗe, maganin shi ya ciro ya buɗe ya ɗauki wanda zai sha sannan ya wuce bakin Fridge, buɗe wa yayi ya ɗauki faro ya sha maganin dashi sannan ya wuce bakin gadon shi ya soma cire kayan jikin shi. Wanka ya shiga ya fito yana tsane jikin shi da towel bayan wanda ya ɗaura a ƙugun shi. Wayan shi da ta fara ƙara ya nufa ya ɗauka yana zama a gefen gadon, peacking yayi yana kara wa a kunne. Congratulations ɗin da ake masa yasa ya saki murmushin shi me kyau yana amsa wa cike da farin ciki. Koda ya gama amsa call ɗin sai wasu kuma suka ci gaba da kiran shi dole ya ɓata lokaci yana amsa calls kafin ya tashi ya shirya a cikin sauri, wani farin tissue ya saka wanda har farin Singlet ɗin da yayi using dashi ana gani. Kayan sun yi masa kyau sabida ƴan dai-dai ne iya jikin sa, sai ya murza hula baƙi ya nufi gaban mirror yayi amfani da turarukan shi wajen feshe ko ina na jikin sa da turare, nan da nan ɗakin ya sake tashi da ƙamshi sosai. Bayan ya gama jerin takalman sa ya nufa ya zari ɗaya wanda ya kasance baƙi ne ya zura ya ɗauki keey ɗin mota da wayan shi ya fito
Fitan shi sai ga motoci sun fara shigowa gidan. Sun yi kusan goma haka suke ta tururuwan shigowa, Mutane ne cike a cikin su suka firfito suka nufe shi ko wanne yana mishi congrats
Hannu yake basu fuskar sa a washe yana amsa musu
Abdul ne ya iso wajen yana son mishi magana
Dole ya ɗau excuse a wajen su ya matsa zuwa wurin shi
Nan Abdul ɗin ya sanar mishi, “Momy ce tace a sanar mishi akwai girkin da ta shirya musu shi da abokan shi zuwa bayan sallan isha’i.”
Murmushi yayi cike da farin ciki ya gyaɗa mishi kai kana yace, “ok insha Allahu zamu yi ƙoƙarin zuwa, ka sanar mata zuwa ƙarfe goma zamu zo.”
Abdul ɗin amsa mishi yayi ya juya ya tafi
Shi kuma ya koma cikin mutanen suka ci gaba da gaisawa. Kana kuma suka ɗunguma gaba ɗaya suka fice a motocin su, while Umar Faruk Yana a cikin nashi tare da securities ɗin shi da suka bi su a baya.
????????????
*MEEMA FAROUK*
????????????
*NA_NAFISA ISMA’IL*
*WATTPAD_UMMUDAHIRAH*
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT* ????????
*PERFECT WRITER’S ASSOCIATION* ????
“`( WE AIN’T PERFECT, BUT WE’RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS????)“`
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._
*NO_24*
*WASHE GARI*
“I want you to tell me about your country, because I also want to go abroad, especially to the Arabian Peninsula.” Cewar Laɗifa tana murmushi
MEEMA wacce take latsa Laptop, ɗago Kai tayi ta kalle ta da murmushi a fuskar ta, a ranta Habibah kawai ta faɗo mata a rai. “Ok, I’ll tell you, but not now. We have a lot of work to do now.”
Ɓata fuska Laɗifa tayi tana miƙa tare da kwantar da kanta a saman kujeran da take zaune, sai kuma tace, “I’m very tired too, and I’m hungry so we should go and get something to eat.”
Hannun ta MEEMA ta ɗago tana duban agogo sai ta mayar da idanuwan ta a a kanta tace, “It’s 12:40 pm. Stay tuned.”
“No now we’re going. I’m tired of work.” Ta sake faɗa tana miƙe wa. Sai ta saka hannu ta rufe Laptop ɗin gaban MEEMAN tana cewa, “Get up and let’s go please. I’m very hungry.”
Shigowar Idris yasa MEEMA tayi shiru bata ce komi ba
Shi kuma kallon su yayi, sai kuma ya kama haɓa yana mayar da idon sa kan Laɗifa yace, “ke kuma fa? Where are you going when you get up?”
“Wlh Brother na gaji yau yunwa nake ji kamar ban ci abinci ba.”
Hararan ta yayi yace, “kin gan ki? Na kula ke acici ne wlh. Ok, let’s get up and eat now.”
Washe baki Laɗifa tayi tace, “yauwa ko kai fa Yayan mu.”
MEEMA tashi tayi itama ta bi bayan su suka fice. A motan Idris ɗin suka ƙarisa restaurant da suke shiga cin abinci. Kowa yayi odan abinda zai ci suka zauna suna ci suna hira. Ƙarfin hiran duk Idris ne yana basu labari suna dariya, kasancewar sa me son Wasa da dariya shiyasa ko baka yi ninya ba sai kayi dariya idan har yana baka labari. Da suka gama suka koma wajen aiki. Sai three O’Clock suka tashi kamar ko yaushe, Idris ya ɗauki MEEMA suka wuce gida
Suna zuwa layin gidan su suka ga motoci kusan biyar a jere, sai wasu masu baƙaƙen kaya da alamu securities ne
“It looks like something is being done here.” Cewar Idris yana faka motan shi daga bakin Gate ɗin su
MEEMA bata ce komi ba illa kallon wajen da take yi, sai kuma ta juyo da kallon ta gare shi tace, “And who are these people?”
“I don’t know MEEMA, but I think someone came here.”
“Ok.” Tace tana ɗaukar jakar ta. Sai da tayi masa godiya sannan ta buɗe motan ta fice
Shi kuma ya danna horn me gadin su ya buɗe mishi ya shige
MEEMA da ƙafa ta taka zuwa bakin Gate ɗin su ta shige ciki. Tana isa bakin ƙofan parlour zata buɗe sai Uncle Hashim ya buɗe suka fito shi da Umar Faruk. Da kallo ta bi su tana ɗan matsa wa baya
While they are also watching her
“My daughter are you back?” According to Uncle Hashim he was smiling at her
Itama murmushin tayi tana gyaɗa masa kai don she could not speak
Uncle Hashim kallon Umar Faruk wanda idanun sa ke kan MEEMA yayi yace, “this is MEEMA, the Aunty’s girl.”
“Really?” He asked looking at him
“Yes. She is back here to stay.” Sai kuma ya kalli MEEMAN yace, “My daughter this is my friend, my best friend, his name is Umar Faruk.”
MEEMA kallon shi tayi ta ɗan yi murmushi kaɗan tare da cewa, “Hello Uncle.”
“How far?” Yafaɗa shima yana kallon ta
“I’m fine.” Sai kuma ta kalli Uncle Hashim tace, “Uncle I’ll go inside.”
“Ok daughter. Let me accompany him outside.”
Kanta kawai ta jinjina mishi tana wuce wa ta shige ciki
Su kuma suka taka suka nufi waje. Sai da suka fita suka tsaya a bakin Gate ɗin
Umar Faruk yace, “but I know this girl, kwanaki ta zo gida na.”
“Haba dai? To wa ta sani a gidan?” Uncle Hashim yafaɗa da mamaki
“Sun zo ne ita da wata, amm.. ina ga From t.v I see they come.”