MEEMA FAROUK Page 31 to 40

“Ok I understand. Tana aiki ne a gidan t.v ai, but Dude I’m wondering if I’ll give it to you? Don kallon da kake mata I think kana ciki ne.” Yafaɗa yana dariya
Shi kuma murmushi yayi da cewa, “kai halin ka na nan ko? Baza ka sauya ba, dama aka ce idan ka rabu da ganin mutum kar ka tambayi idan ya canza, domin halin shi na nan.”
Murmushi Uncle Hashim yayi yace, “Allah da gaske nake yi, ka san daughter na ce kuma wlh kun dace sosai. Tunda naga ka ƙi sake aure tun tafiya na ga shi har yanzu kana nan a haka, na san yanzu ai Yusra ta girma sosai tunda tana shan nono muka rabu.”
“She’s grown up, now she’s in school too.”
“Allah Sarki Yusra da Hafsah, insha Allahu I will come in and see them later, zamu gaisa da Momy ai”.
“Allah ya kai mu.” Sai ya ba shi hannu suka gaisa suna wuce wa wurin motan. “But will you stay here for two days?”
Uncle Hashim yace, “insha Allahu. Zan yi two weeks ni gaskiya, sai dai Jalila za su koma tunda akwai school ɗin Habeeb.”
Daga nan sallama suka yi ya shiga motan da ɗaya daga cikin securities ɗin ya buɗe mishi
Har sai da motocin suka tafi kafin Uncle Hashim ya shige gida. A haraban gidan ya tsaya yana amsa call, yana nan tsaye ne ya hangi wani guy yana shigo wa ciki, ganin ya dumfaro wurin shi sai ya katse kiran yana mayar da hankalin sa a kan shi, kallon sani yake mishi sai dai be ce komi ba har ya iso wurin shi, ya ba shi hannu suka gaisa kafin ya tambaye shi, “wane yake nema?”
Murmushi Sajjad yayi yana ɗan shafa kanshi kamar yanda ya saba yace, “suna na Sajjad Aliyu, ni ɗa ne wajen Kawu Faruk surukin nan gidan.”
Tabbas sai a yanzu ya gane fuskar MEEMA yake gani a tare dashi, sai ya washe baki yace, “ah kace daga Yola kake? You Are welcome, let’s go inside.”
Sajjad bin Bayan shi yayi har cikin gidan
Sai dai babu kowa a Parlour, sai yace mishi, “ya zauna bari ya kira mutanen gidan.” Ya wuce ciki. MEEMA ya fara kira sannan ya kira Ummee, ya shiga ɗakin Hajiya ya gunguro ta suka fito
Tunda MEEMA suka yi ido huɗu da Sajjad ai sai ta ja ta tsaya daga inda take ta kasa ƙarisowa
Shima haka yana ganin ta ya miƙe tsaya idanun sa ƙyam a kanta nan da nan farin ciki ya cika shi da ganin ta
Fitowar Uncle Hashim tare da Hajiya ya kalle ta yace, “let’s go daughter.” Sannan ya wuce
Ummee itama sai a lokacin ta fito suka zauna a kan sofa
“Ka zauna mana.” Uncle Hashim yafaɗa yana kallon Sajjad ɗin
Babu musu ya zauna. Sai kuma ya fara gaishe da su
Ummee da ke mishi kallon sani tace, “kamar na so in Gane ka? Sajjad ko?”
Murmushi yayi yace, “Yes Ummee Ni ne.”
“Ikon Allah kai ne a nan? Kai da wa kazo?” Tafaɗa da mamaki
“Ni kaɗai.”
Murmushi tayi sai kuma ta kalli Hajiya tace, “Hajiya wannan ɗa ne wurin miji na, mahaifin shi Yayan Faruk ne ai.”
“To Masha Allah, sannu da zuwa, ki ce ɗan uwan MEEMA ne ai, Ga kamanni wlh.” Tafaɗa cike da fara’a
Uncle Hashim yace, “to ai ga daughtern can ta ƙi ƙariso wa.” Sai ya ɗaga murya ya kira ta
Dole a yanzu ta iso wurin sai dai fuskar ta a ɗaure tamau tana kallon Sajjad ɗin
“Daughter do you recognize him? This is your cousin”. Cewar Uncle Hashim Yana murmushi
“Na’am. I recognize him Uncle, But what did he come to do here? I don’t want to see him.”
Mamaki duk kan su suka yi da maganar ta
Musamman Ummee da ta san zai yi wuya MEEMA ta gane Sajjad, kasa shiru tayi tace, “How come you know him after you’ve never seen him?”
Cikin muryan kuka da ya ƙwace mata tace, “When I landed here country I went to their house and stayed. They wanted to marry me without my knowledge. One day before we were to get married I knew. That’s why I came here. And I don’t want him, I hate him so much.”
“Subhanallah.. married again? Don’t you know?” Hajiya tafaɗa da tsantsan mamaki
Itama Ummee kalman auren ta sake maimaita wa fuskar ta cike da damuwa
Sajjad da kanshi ke ƙasa ya kasa cewa uffan
Sai Uncle Hashim da ya tashi a zuciye yace, “kai tashi ka kama hanya ka bar mana gida, nan ba wajen zaman ka bane…”
Hajiya ce ta katse shi da cewa, “a’a Hashim ai baka san me ya kawo shi ba, kuma kana da tabbacin da laifin shi ne?”
“Da laifin shi mana Hajiya, ba shi ne wanda za’a ɗaura mishi aure da ita ba ba bare da amincewar ta ba? Don kawai zalunci, dama ai ba ƙaunar ta suke yi ba kuma mun san da haka, tabbas akwai abinda yasa suke son yi mata aure ba tare da amincewar ta ba, wato auren dole suka so suyi mata?” Yafaɗa a fusace
Da gudu MEEMAN ta isa wurin Uncle ɗin ta rungume shi tana kuka
Hakan ya ƙara hassala shi yana kallon Sajjad ɗin da cewa, “kai baka ji me nace maka bane? Ka tashi ka bamu wuri ka koma inda ka fito tunda baku da mutunci.”
Cikin hawayen da suka kufce mishi Sajjad ɗin ya zube a kan gwiwowin shi yana roƙon su da Allah, “su bar shi a nan ya zauna, wlh yana tsananin ƙaunar MEEMA bazai iya rabuwa da ita ba…”
Katse shi yayi da cewa, “tashi nace, wlh ka bari na sake maka magana sai dai uwar ka ta haifi wani a gidan nan.”
Su Hajiya sun san halin Uncle Hashim akwai zuciya ba ya son raini, dama dalilin da yasa ya shiga aikin soja kenan domin akwai shi da zuciya sosai idan ranshi ya ɓaci. Dole Hajiya ta soma rarrashin sa da cewa, “ka ga Hashimu kayi haƙuri ya fita a hankali kar kayi masa wani abun kaji ko?”
“To Hajiya uwar me yake jira da bazai fita ba?”
Duk hayaniyar Uncle Hashim ɗin ne ya fito da su Jalila da Zabba’u suka zo suka tsaitsaya suna kallon ikon Allah
Sajjad ba don ya so ba ya tashi ya fice yana sharan hawaye
Zabba’u da ita ce bakin ta ke ƙaiƙayi take bin ba’asin me ya faru. Sai da aka sanar mata sannan hankalin ta ya kwanta. Sai kuma ta koma tana faɗan albarkacin bakin ta, sai tsiya take yi tana faɗin, “ai wannan mugunta ne ace zasu yiwa yarinya aure ba da amincewar ta ba, haka ake yi ne?”..
Shi kuwa Uncle Hashim tuni ya ja hannun MEEMA zuwa ɗakin ta, a can ya rarrashe ta domin kuka take ta yi sosai ta kasa yin shiru. Sai da ya kwantar mata da hankali kafin ya fito ya yiwa su Hajiya sallama a kan, “zai je gidan abokin shi.” Ya fice
Su kuma sai mayar da zacen suke yi, daga ƙarshe kuma suka koma hira.
The following day. Lokacin Hajiya na zaune a ɗaki tana lazimi Uncle Hashim ya shigo ɗakin duk a rikice. Kallon sa tayi tana tambayar sa, “lafiya Hashimu wani abun ne ya faru?”
Sai da ya zauna a kan sofa ya gaishe ta kafin yace, “wlh Hajiya babu lafiya, ina zaune a ɗaki aka kira Ni ake sanar min Umar Faruk yayi hatsari jiya da dare.”
“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un. Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un.. a garin ya ya? Da sauƙi dai ko?” Tafaɗa itama a rikice
“To Hajiya ban sani ba wlh, sai dai idan na je yanzu zan gani.”
“Subhanallah.. ai ba kai kaɗai zaka je ba, mu tafi gaba ɗaya, Allah sarki jiyan nan fa ya zo gidan nan, yanzu da ace mutuwa ce sai dai mu ji an ce ya mutu, oh Allah! Allah yasa dai ba magauta bane domin dama duk wanda ya shiga siyasa ai baza a raba shi da su ba.”
“Haka ne Hajiya. Nima wlh Ina tunanin haka.” Yafaɗa fuskar shi duk a dame
“To ka jira Ni bari in Yi wanka. Ka turo min Zabba’u da Allah.”
Yace, “to.” Yana miƙe wa ya fice. Sai da ya je ya sanar wa Zabba’u wacce take kichen tana haɗa kumallo kafin ya nufi Steps zai haye
A lokacin ne MEEMA ta fito daga ɗaki a cikin shirin ta na zuwa Office. Ganin shi yasa tayi saurin ɗaga murya da cewa, “Uncle good morning.”