MEEMA FAROUK Page 31 to 40

Tsaya wa yayi ya juyo. “Ah ah my daughter. You wake up?”
“Na’am Uncle.” Tafaɗa tana Isa wurin shi. Ta kama hannun shi tayi masa kiss tana kallon shi
Shi kuma ya shafa kanta yana murmushi da cewa, “Do you go to work?”
Jinjina masa kai tayi tana mayar mishi da martanin murmushin
“Ok. Let’s go out together I’ll drop you off at work. We’re going to greet my friend who came here yesterday. It had an accident last night.”
Waro ido waje tayi da cewa, “This one we greeted yesterday?”
“Yes daughter.”
Fuskar tausayi tayi tace, “eyya. God forbid. He don’t hurt?”
Sai da ya riƙe hannun ta da alamun rarrashi yace, “insha Allah It’s easy for him, will you go and greet him?”
Gyaɗa kanta tayi don ta kasa magana, haka kawai taji gaban ta na faɗuwa while idanun ta sun cika da hawaye
Ganin yanda ta koma sai yayi murmushi yana cewa, “You Care about him?”
Still gyaɗa mishi kai tayi don ta kasa yin magana, sosai bakin ta yayi mata nauyi
“Ok let’s go to my room, don’t worry ok? Insha Allah he will be fine.”
Hannun su a saƙale da juna suka wuce sama. Ɗakin Ummee yayi Nocking still Yana riƙe da hannun MEEMA
Tana buɗe wa suka haɗa ido da MEEMA
Ita kuma tayi saurin ɗauke kanta tana sake haɗe kyakykyawar fuskar ta
Ummee yanda ta ga MEEMAN ne yasa ta tambayi Uncle Hashim bayan ta amsa gaisuwar shi. “Me ya sami MEEMA kamar akwai wani abun da ke damun ta?”
Sai da ya ɗan kalli fuskar ta kafin yace, “eh Aunty, na sanar mata da hatsarin da Dude yayi ne shi ne duk ta shiga damuwa. Dama shi na zo faɗa miki Umar yayi hatsari jiya da dare.”
“Subhanallah.. innalillahi wa’inna ilaihi raji’un.. da sauƙi ko?”
“I don’t know aunty, Amma Hajiya tace mu shirya gaba ɗaya sai mu je mu duba shi.”
“Ok to bari in shirya.” Tafaɗa tana koma wa cikin ɗakin
Shi kuma ya ja hannun MEEMAN suka wuce nasu ɗakin
Shigan su ɗakin Jalila ganin su tare yasa ta washe baki tace, “oh yau tare kake da daughtern taka har nan?”
Murmushi yayi yana zama a gefen Habeeb
While MEEMA na tsaye. Sai ta gaishe da Jalilan tana ɗan sakin fuskar ta
Habeeb da sauri ya taso ya rungume ta yana kiran ta da, “Aunty.”
Hakan yasa ta saka hannu ta sake rungume shi tana mishi magana
While Uncle Hashim kuma yana sanar da Jalila abun da ke faruwa. Sannan ya sanar mata, “ta shirya su je duba shi”.
MEEMA tana tare da su har suka shirya sannan suka sauko ƙasa. Tun suna yin Breakfast gaba ɗaya ta sauya, abincin kawai take ci hankalin ta ba ya jikin ta, haka kawai a zuciyar ta ta ƙosa ta je ta ganshi, duk ta damu fatan ta Allah yasa yana ƙoshin lafiya. Babu abinda ke mata gizau sai kyakykyawar fuskar shi, ita kanta mamakin yanda ya tsaya mata a rai take yi, amma kuma gani take yi tausayin sa ne ya shige ta kasancewar hatsari yayi, Allah-Allah take yi su tafi
Da suka tashi tafiya mota biyu suka cika suka tafi asibitin da aka ce yana can.
????????????
*MEEMA FAROUK*
????????????
*NA_NAFISA ISMA’IL*
*WATTPAD_UMMUDAHIRAH*
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT*????????
*PERFECT WRITER’S ASSOCIATION* ????
“`( WE AIN’T PERFECT, BUT WE’RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS????)“`
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._
*NASIHA*
_Duk wanda ya karya ginshiƙin addinin sa, duk wanda ya bijire wa umurnin mahaliccin sa, duk wanda ya saɓa wa koyarwar Annabin sa wanda aka aiko shi ya kasance jagora ga al’umma, duk wanda ya ji kalmomin Ubangiji da suke gaya masa me ya kamata yayi ya kuma fahimce su amma duk da haka ya dage a kan hanyar tsageranci da hamɓare su, duk wanda yake fankamar shi ya fi ƙarfin ya bauta wa Allah Ubangijin sa, to, duk wani horon da ya same shi bai yi yawa ba. In ya tsaya tsaf ya ƙi yin Sallah lalle ya fita daga daular Islama kuma ba shi da damar ya kuka da hukunci da ya dace da shi Kamar dai yadda Alƙur’ani yayi bayani. Allah yasa mu dace._
*NO_25*
A haraban Hospital ɗin suka tsayar da motocin kafin suka fito. Uncle Hashim ya fito da Hajiya ya zaunar da ita a wheelchair ɗin ta, sannan sai Zabba’u ta tura ta suka yi cikin asibitin. Tun kafin ma su tambayi ɗakin da aka kwantar da shi suka hango securities a gaban wani ɗaki. Hakan ya tabbatar wa da Uncle Hashim nan ne ɗakin da Abokin shi yake. Can ya nufa suka take mishi baya
Securities ɗin tsayar da su suka yi suna tambayar, “ina zasu je?”
Uncle Hashim ne yayi musu bayani
Kasancewar sun gane shi yasa suka bar su suka shiga
A ɗakin daga Momy sai Abdul ne zaune sun tasa Umar Faruk a gaba gunun tausayi, kai kace sun damu da shi ne a yanda suka nuna, musamman ma Momy wacce gaba ɗaya idanun ta sun jiƙe da ruwan hawaye sai kai gyalen ta take yi tana kwashe su
Yayinda shi kuma yana kwance a saman gado idanuwan sa a rufe, da alamu ba wasu rauni ya ji ba sai dai a kansa da aka naɗe mishi da bandage, sai kuma ƙafar shi ɗaya ta dama da itama duk an saka mishi bandage a ciwukan da ya ji, sai kuma ƙaramar yatsar shi itama ta hannun dama wacce aka saka mishi drip
Shigowar su yasa su Momy suka bi su da kallo suna amsa sallaman nasu. Kasancewar Momy ta gane su musamman ma ganin Uncle Hashim da tayi yasa ta washe baki tana tashi tsaye tare da musu lale marhaban
Shima Abdul tashi yayi ya bai wa Ummee kujeran sa
Sannan aka gaisa cike da mutunci. Su Hajiya suka yi musu, “ya me jiki?”
Momy ta amsa da faɗin, “alhmadulillah. Ya samu barci ne mu ma tunda muka zo be farka ba.”
“Allah Sarki! Allah ya ba shi lafiya. Wlh hankali na ya tashi da jin labarin hatsarin shiyasa muka taho gaba ɗaya.” Cewar Hajiya cike da damuwa
Momy tace, “wlh kuwa. Ai abun ne da tashin hankali. Nima ya zo ya gaishe Ni a jiyan yake ce min zai fita meeting, wlh a Raina sai da naji ban amince da fitar nashi ba, amma kuma tunda ya zama dole babu yanda zan yi, be fi mintuna goma ba aka kira mu aka sanar mana yayi hatsari, kuma motar tashi ce kaɗai ta kwace ma drever’n, Allah yasa akwai mutane tare dashi aka yi saurin taimakon shi tunda hatsarin ba sosai bane, ai mun auna arziƙi.” Ta ƙare maganar tana sake share hawayen fuskar ta
Haƙuri duk suke bata. Hajiya na sake tausan ta
Sai kuma ɗakin ya ɗan yi jugum
A lokacin ne Umar Faruk ya buɗe idanun sa
Hakan yasa Uncle Hashim da ke tsaye ya koma gefen gadon ya zauna yana kallon shi
A hankali yake bin mutanen ɗakin da kallo yana yi yana ɗan lumshe idanun sa
Uncle Hashim ya soma mishi sannu kafin sauran su soma gaishe shi da jiki
Kanshi kaɗai yake ɗaga musu yayinda ya sauke idon shi a kan MEEMA wacce ta tsaya a can baya ta zuba mishi ido
But yana kallon ta sai ta ɗauke nata idon daga kallon shi tana ɗan gyara tsayuwar ta kasancewar ta soma gajiya, ɗan ɗago kai ta sake yi ta sauke a kanshi ta ga har yanzu ya kasa ɗauke ido a kanta, sai ta janye nata tana sauke kai ƙasa tare da wasa da yatsun hannayen ta. Ta kula yana da yawan kallo a yanda ta fahimta, kaifin idanun shi yake sa take gane ita yake kallo, hakan ke haifar mata da faɗuwar gaba me tsanani, sosai gaban ta ke bugawa wanda yasa ta kasa tsayuwa wuri ɗaya tana ɗan jujjuya jiki