MEEMA FAROUK Page 31 to 40

Momy wacce ta lura da kallon da yake yiwa MEEMA yasa ta mayar da kallon ta gare ta, sai yanzu tayi mata kallon ƙurilla domin tun shigowar ta baza tace akwai ta a cikin ɗakin ba ma, duba da yanda ta ja can baya ta tsaya. Hakan yasa ta ɗan washe baki tana cewa, “ita kuma wannan kyakykyawar yarinyar fa daga ina?”
Zabba’u tayi saurin bata amsa da faɗin, “ai ɗiyar Hajiya ƙarama ce, sunan ta MEEMA.”
“Allah Sarki! Masha Allah yarinyar kyakykyawa da ita.”
Duk murmushi suka yi
While Abdul da shima sai yanzu ya kula da ita, tunda ya kafa mata ido ya kasa ɗauke wa, sai ƙare wa halittan ta kallo yake yi daga sama har ƙasa tamkar idanun sa za su fito waje har buɗe baki yayi
Uncle Hashim da shima yana kula da kallon da Umar Faruk yake bin MEEMA da shi, sai yayi murmushi yana matso da fuskar sa gefen sa, ya ɗan raɗa masa maganar, “sai na tsole idon idan baka dena kallon ta ba, ko dama ba jinya kake yi ba?”
Hakan yasa ya saki kyakykyawar murmushin sa yana ɗan lumshe idanun kamar zai rufe su sai ya juyo su ga kallon Uncle Hashim ɗin, be ce komi ba illa murmushin da yake saki, sai kuma ya ɗan karkata kai ya kalli Habeeb da ke jikin Jalila ya yafico shi da hannu
Hakan yasa yaron ya iso wurin shi
Yayi mishi murmushi da cewa, “har da kai kaima ka zo duba ni?”
“Eh Uncle. Ya jikin ka?.”
“Alhamdulillah my boy. Kai ma ya naka jikin?”
“Ai naji sauƙi.” Yafaɗa yana ɗaura hannun sa a kai
Zabba’u tace, “ai ya ji sauƙi sosai in dai Habeeb ne.”
“Eyya shima be da lafiya ne ashe? Allah ya sawwaka ɗan yaro na, taho mu gaisa ko.” Cewar Momy fuskar ta cike da fara’a
Daga Hajiya har su Ummee amsa mata suka yi da, “Ameen Ameen.”
Iso wa yayi wajen ta, ta ɗaura shi a cinyan ta tana tambayar shi
Daga haka ɗakin yayi shiru illa sauraron surutun da Habeeb yake yi tare da Momy.
Ita kuwa MEEMA duk ta gama gajiya, gaba ɗaya fuskar ta ta sauya tamkar zata yi kuka sabida rashin sabo
Ta gefen ido duk Umar Faruk yana kallon ta, a ransa kuwa dariya ta ba shi yana mamakin sangarta irin nata domin ya kula tsayuwar nata ne ya dame ta take shirin kuka. Sai dai ya kasa yanda zai yi yayi mata magana bare yace, “ta zauna.” Wanda hakan ne a cikin zuciyar sa
Shima Abdul ya kula da yanayin ta hakan yasa ya buɗe baki da ninyan yin mata magana
Sai Uncle Hashim yace, “Daughter, you are tired? Come here and sit down and let me out.”
Murmushin yaƙe ta ɗan saki sai dai bata ce komi ba ganin inda yake nuna mata ta zauna ɗin, ma’ana a saman gadon shiyasa ta kasa motsa wa
Hajiya tace, “ai mu ma ba daɗe wa zamu yi ba, But before we leave, go and sit down since you are tired.”
Kanta ta ɗan gyaɗa ta nufi wajen ta ɗofana mazaunan ta a inda Uncle Hashim ya matsa mata, hakan yasa har jikin ta ke gogan juna da cinyan Umar Faruk. A tare suka lumshe idanun su ko wanne yana jin wani abu ya tsirga mishi; wanda ita ta kasa jure wa dole ta sake jan jikin ta ta matsa gefe sosai ta yanda baza su haɗe ba.
A haka dai suka zauna jigum sai su Hajiya da suke ɗan taɓa hira. Sai da wasu mutane da suka zo gaishe da Umar Faruk ɗin suka shigo sannan su Hajiya suka yi musu sallama suka fice a ɗakin. Manyan Mutane ne kusan su goma ƴan siyasa suka zo gaishe da shi.
Uncle Hashim da MEEMA a mota ɗaya suka koma. Dayake zai sauke ta a wajen aiki. Yana zuwa ya sauke ta ya wuce tunda akwai inda zai je
Tunda ta shiga ciki suka gaisa da waɗanda ta ci karo da su ta wuce Office ɗin su. Sai dai tana shiga babu kowa sai ta tsaya ba tare da ta zauna ba. Tana shirin juya wa zuwa Office ɗin Idris sai wata me suna A’isha wacce itama aiki take yi a gidan t.vn, ita ta hange ta ta ƙariso wurin ta tana cewa, “Hi MEEMA”.
“Hi.” Ta amsa mata tana kallon ta
Murmushi A’isha tayi tace, “Today I thought you would not come, and Laɗifa did not come, and you is ok?”
“Fine. I went somewhere.”
Isowar Idris wajen shi yasa A’isha ta yiwa MEEMA sallama ta wuce
Yana isowa suka gaisa yake tambayar ta, “Where are you going? I’ve just come to pick you up but your gate Man says you’re all out.”
“We went to the hospital.”
“Subhanallah.. Who is sick?”
Shiru tayi, sai kuma tace, “This man we went to his house me and Laɗifa and interviewed, amm… Senate.”
“Ok Senator Umar Faruk Aliyu, You went to him?”
Gyaɗa masa kai tayi da faɗin, “na’am.”
“Ok I heard, right now I want to go and talk to him about the accident, now go to the office and rest when I finish my work so we can go together and talk to him. From there we go to greet Laɗifa and She is not feeling well.”
Fuskar ta ne ya sauya tana ɗan sake buɗe manyan idanuwan ta tace, “really? I don’t know, i didn’t call her, easily her body?”
Ɗan numfashi ya ja kafin yace, “Calm down, insha’Allah. Her body is fine, but I just called her and she couldn’t pick up the phone. Her mother informed me of her condition. Go inside and finish your work and we’ll go.”
Ɓata fuska tayi hawaye na ciko mata a idanu tace, “I can’t work now until I see her condition. I’m scared.”
Murmushi yayi a ransa yace, “MEEMA rigima! tana jin ta kamar wata yarinya ce.” Sosai ya kula akwai dolanci da sangarta irin na ƴaƴan masu kuɗi a tattare da ita, irin waɗan da aka shagwaɓa ɗin nan sosai. komi nata tana yin sa ne tamkar wata ƙaramar yarinya, ba ta kunyar ta yiwa ko waye taɓara ko kuma tayi masa kuka, bata da wahalan kuka ko a gaban waye ne. “Fine. Let’s go to my office and pass from there.”
Kanta ta ɗaga mishi tana bin Bayan shi. Daga can bayan ya gama abinda zai yi suka fito suka wuce asibitin da aka kwantar da Senator Umar Faruk.
✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️
A can kuwa gida lokacin da su Hajiya suka koma. Me gadi na buɗe musu ƙofa Ummee ta tura hancin motan ciki. Tunda suka shiga suka ga wata jan mota wanda sun tabbatar ba na gidan bane
Me gadi na rufe Gate ɗin ya iso wurin su da gudu. A lokacin duk sun fito suna ƙoƙarin fito da Hajiya. Ya gaishe su yana cewa, “Hajiya dama baƙi ne suka zo nan gidan. Ga su can a cikin mota.”
“Baƙi kuma?” Da Hajiya da Ummee suka haɗa baki wajen faɗa
“Eh wlh. Nayi yunƙurin tsayar da su daga waje amma sun ƙi tsaya wa, dole suka saka Ni na buɗe musu ƙofa suka shigo. Bari inyi musu magana sai su zo.” Ya ƙare maganar yana wuce wa wajen motan da hanzari
Bayan yayi musu magana ne sai suka fito daga motan
Ai Ummee na ganin su ta gane su, Kawu Ali ne da Kawu Zubairu
Hajiya kuma sai da suka iso gab da ita itama ta shaida fuskar su
Su suka fara gaishe da Hajiya kafin itama ta saki fuska ta amsa su tana musu lale marhaban
Ita Ummee ta kasa musu magana sai kallon su da take yi, domin ta san halin su tunda ta gansu a nan ba alheri ne ya kawo su ba, baza ta manta sanda suke zuwa can Riyadh suke cin musu mutunci ba ita da Faruk da ɗiyar su. Sanadi har da rashin ƙaunar da suke nuna mata yasa ta bi ruɗin ƙawaye ta bar mijin ta a halin laluran da yake tsananin buƙatar ta ta taho nan. Daƙyar ta buɗe baki a yanzu ɗin ta gaishe su
Duk amsa wa suka yi fuska a ɗaure suna wani ciccin magani
Ita dai taɓe baki kawai tayi tayi gaba abin ta
Hajiya ce ta ce musu, “su shiga ciki.”
Sannan ne suka bi bayan su suka shiga Parlour. Sai da suka zauna aka ƙara gaisa wa
Kafin Kawu Ali ya soma magana da faɗin, “ba wani abu ya kawo mu nan ba sai maganar Zulaiha. To mu mun zo ne mu tafi da ita kawai babu wani kace nace duk da dai wulaƙancin da ɗana ya fuskanta zuwan shi nan, yarinyar nan ta ci mana mutunci ba kaɗan ba amma duk da haka muka biyo baya saboda a matsayin mu na dolen ta, ba don haka ba wlh babu yanda za’a yi mu tako ƙafar mu mu taho nan. Don haka sai ku bamu ita mu tafi da ita abun da ya kawo mu kenan.”