MEEMA FAROUK Page 31 to 40

Hajiya da ta zuba musu ido tana kallon su jin yayi shiru sai tace, “to Aliyu kake ko wa? Zancen gaskiya baku yiwa yarinyar nan adalci ba, ita a yanda ta faɗa mana so Kuka yi kuyi mata aure ba tare da amincewar ta ba, hasali ma bata san da zancen ba sai da biki ya zo. Hakan ai ba kyautuwa bane…”
Bata ajiye numfashi ba Kawu Zubairu ya tada jijiyan wuya da cewa, “to ke a ganin ki Hajiya har sai an tambaye ta sannan zamu iya mata aure? Muna da ƴancin da zamu iya aurar da ita ga duk wanda muke so, sannan shi wannan yaron ɗan mu ne haka itama ƴar mu ce, ganin babu ran mahaifin ta yasa muke so mu rufa mata asiri mu aurar da ita ga ɗan mu kamar yanda ya ce yana so, amma mu ma ba’a son ran mu bane tunda babu yanda za’a yi muna ji muna gani mu ɗaura wa ɗan mu yarinyar da ta gama gantale wa ta kasa auruwa, yarinyar da kaɗan ya girme mata don mun yanke wannan hukuncin shi ne zai zama abun magana? Ai idan ba’a gode mana ba baza ayi Allah wadai da mu ba.”
Sosai maganganun Kawu Zubairu ya ɓata wa Hajiya rai
Ba ita kaɗai ba har Ummee wacce tana ji tana gani ana son aibata mata ɗiya. Shiyasa tayi saurin cewa, “maganar gaskiya Yaya bazai yiwu ace ku zo har cikin gidan mu kuna gaya wa Mahaifiya ta da ɗiya ta magana ba, idan na jure a baya wancan nayi shiru ne domin ɗan uwan ku, amma yanzu babu wanda zai zo har gidan mu ya ci mana fuska, ita MEEMA ai ɗiya ta ce kuma ta dawo hannu na baku da halin amsar ta, ita da kanta ta zaɓi nan don haka babu wanda a cikin ku zai tafi min da yarinya wani wuri.”
“Auu iyeeeee! Wuyan ki ya isa yanka Zulai mu kike faɗa wa haka?” Cewar Kawu Ali a zafafe
Hajiya tace, “gaskiya ce ta faɗa, babu inda zaku je mata da ɗiya tunda ba arziki ne da ku ba.”
Kawu Ali yace, “to wlh baku isa ba, dole sai mun tafi da ita tunda mu ne ya zama wajibi ta zauna da mu, idan ba haka ba wlh babu inda zamu je ƙafar mu ƙafar ta, har ku kun isa? Matsiyatan banza matsiyatan hofi! ɗan uwan mu ya bar dukiya dole ai ku ɗauke ta, meye bamu da labari a kai, nan ita uwar ta ta tafi ta bar su sai yanzu da kuka san ya mutu shi ne kuke da bakin cewa zaku riƙe ta, to zan gani, wlh tallahi sai dai kotu ta raba mu da ku.”
“Yo kuce kuɗi kuka biyo ba yarinya ba? Akwai wasu matsiyata ne bayan ku? Tunda ba mutunci ne daku ba ku fice min a gida tun kafin ku ga abin da zai faru da ku, ƴan iska mara sa mutunci.” Inji Hajiya itama a zafafe kamar zata tashi tsaban rigima
Nan fa sai cacan baki ya kaure wanda dole su Jalila ita da Zabba’u suka fito tunda su basu a wurin
Yanda suka taru suke ta cin ma ƴar tsohuwa mutunci ne yasa Ummee itama take tare mata
Jikin Jalila na rawa ta nufi ɗaki ɗauko waya ta kira Uncle Hashim ganin abun nasu ba na ƙare bane. Tana kiran shi ya ɗauka ta sanar mishi da halin da ake ciki
Kankace me ya kashe wayan da faɗin, “ga yi nan zuwa yanzu-yanzu.”
✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️
Idris na Isa hospital ɗin ya faka motan suka fito suka shiga ciki. Sai dai koda suka je shiga ɗakin securities ɗin shi sun hana su shiga duk da Idris ya nuna I.D card ɗin shi
Da ya dame su da naci ne sai ɗaya security ɗin ya shiga ya sanar wa da Umar Faruk ɗin. Babu jima wa ya dawo ya sanar musu, “ba ya buƙatar hira da su.”
Fitowar security ɗin ne ya bar ƙofan a buɗe wanda ya bai wa Umar Faruk damar hango kayan MEEMA, baƙin Abayar da ta sanya tabbas shi ne ya hango tunda dashi ta zo ɗazu. Sai leƙa kai yake yi sai dai ya kasa yin magana domin ya san ko ya ɗaga murya baza su ji ba, bare shi ba me son hayaniya bane. Yana kallo har suka tafi sai ya ɗan yarfa kai gefe yana mayar da idanun sa ya lumshe su. Allah yasa sai ga security ɗin ya shigo da sauri ya buɗe ido yana kallon sa ya sanar mishi, “yayi maza ya kira mishi Macen tazo.”
Hakan yasa ya fita da sauri ya isa haraban Hospital ɗin
A lokacin har sun shiga mota Idris na ƙoƙarin tayar wa
Sai ya isa wurin da sauri. Ya tsayar da shi yana faɗa mishi saƙon Umar Faruk ɗin. Ganin Idris ɗin zai fito sai yace dashi, “ita kaɗai yake buƙata.”
Koma wa yayi ya zauna Idris ɗin yana duban MEEMA wacce take zaune a cikin motan. Bata ma san me suke cewa ba tunda hankalin ta na kan waya tana latsawa. Yace da ita, “MEEMA come out and join Senator Umar Faruk he wants to talk to you.”
Duban sa take yi da mamaki but taƙi yin magana sai ɗan ƙara buɗe kyawawan idanuwan ta da tayi
“Yes. He said he should be called you. I think you will talk together.” Sai ya miƙa mata recorder ɗin hannun shi yace, “Go with this and discuss.”
Ɗan jim.. tayi tana kallon shi, sai kuma ta saka fararen hannayen ta ta amshi recordern ta fice. Bayan security ɗin tabi har zuwa ɗakin da yake ciki. Shi security ɗin ya tsaya a waje ita kuma ta tura ƙofan ta shige a hankali kamar wacce take tsoron shiga.
????????????
*MEEMA FAROUK*
????????????
*NA_NAFISA ISMA’IL*
*WATTPAD_UMMUDAHIRAH*
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT*????????
*PERFECT WRITER’S ASSOCIATION* ????
“`( WE AIN’T PERFECT, BUT WE’RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS????)“`
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._
*NO_26*
Tunda ta turo ƙofan ta shigo idanun sa na kanta ya kasa ɗauke su
Ita kuma ganin kallon da yake mata yasa ta kawar da kai tana takowa a hankali zuwa cikin ɗakin, tsayawa tayi ta kasa ƙarisawa illa sauraron bugun zuciyarta da ke ƙara hauhawa take yi
Shi ne yace mata, “Come and sit down here.” Ya nuna mata kujeran da ke bakin gadon nashi
Hakan yasa ta ɗan kalle shi sai kuma ta taka izuwa kujeran ta zauna a hankali. Kanta a ƙasa ta kasa ɗagowa
Sai ɗakin yayi shiru illa shi da yake faman kallon ta ko kaɗan ya kasa ɗauke ido a kanta, be san meyasa ba tunda ya fara ganinta ta tsaya mishi a rai, ba ya gajiya da kallon kyakykyawar fuskar ta hakan yasa be iya control kansa, wani lokacin be ma san yana kallon ta ɗin ba sai daga baya yayi ta mamakin kansa. Yanzun ma daƙyar ya iya buɗe baki yace, “Do you need anything from my place?”
Kanta ta ɗago ta kalle shi a wannan lokacin sosai sai dai fuskar ta babu walwala. Bata iya ce mishi komi ba illa kallon shi da take yi
Shima sai ya tsira mata ido yana kallon cikin idanun ta yayinda yake jin tamkar wani abubuwa suna jansa izuwa cikin nata idanun
Ta kasa jure wa ta ɗauke idanuwan ta tana mayar da su ƙasa. Sai kuma a hankali ta furta, “how your body?”
Yanda muryan ta ya bugi kunnen sa yasa ya lumshe idanun sa sabida daɗin sanyin muryan ta. Ya ɗau lokaci a haka kafin ya ware idon a kanta yana furta, “alhmadulillah. How did you get home?”
“Fine.” Tafaɗa a taƙaice. Sai kuma ta ɗan ɗago ta dube shi da cewa, “We want to talk about your accident. If you don’t mind I’d like to talk to you?”
Idanun sa cikin nata yace, “I don’t want to talk to journalists. I have nothing to tell you. And I see that you want to restrict me.”
Jin maganar nasa yasa ta tashi tsaye still tana kallon shi, sai dai bata ce komi ba ta juya ta fice tana mamakin, “to meyasa ya kira ta idan babu abinda zai ce da su?”