MEEMA FAROUK Page 31 to 40

Shi kuma ya kasa tsayar da ita yana kallo ta fice domin be san me zai ce mata ba, shi dai ya bi umarnin zuciyar sa ne wacce ta saka shi ya kira ta ba shi da abun ce mata.
Tana isa wajen motan ta buɗe ta shiga
Idris da ke faman jiran ta kallon ta yayi ya tambaye ta, “Did you interview him?”
Girgiza masa kai tayi kamar baza tayi magana ba sai kuma ta kalle shi tace, “He says he doesn’t need to talk to us.”
Mamaki ne bayyane a fuskar sa, sai yace, “But why does he need to see you if not the interview would bother us?”
“I don’t know.” Tafaɗa a hankali tana kawar da kanta gefe
Shima be ce komi ba ya ja motan suka fice. Sai da ya cilla motan a kan titi kafin ya sanar mata, “their house Laɗifa will pass.”
Bata ce masa komi ba har suka kai bakin gidan
Ya taka birki suka fito suka shiga cikin gidan su Laɗifa. Da Umman ta suka soma cin karo a tsakar gida don haka Idris ya gaishe ta. Itama MEEMA ta gaishe ta da Hausan jin Idris ya gaishe ta
Cike da fara’a ta amsa musu tana musu lale marhaban. Kana kuma tayi musu jagora zuwa ɗakin nasu
Suna shiga suka ga Laɗifan a kwance a saman kujera
Ganin su yasa ta tashi zaune da murnan ta tana washe baki, duk da kana kallon ta zaka fahimci tana jin jiki amma hakan be sa ta ƙi nuna farin cikin ta da ganin su ba
Idris da ya ƙware wajen tsokana sai ya kama haɓa yana cewa, “Umma anya yarinyar nan ba ciwon aure ne ke damun ta ba? Dama na faɗa miki ki gaggauta aurar da ita kin ƙi, kullum ita ciwo ba ta shafe sati bata yi ciwo ba.”
Dariya Umma tayi
While ita kuma Laɗifa hararan shi tayi tace, “masharranci kawai, kai me ya hana ka auren sai Ni zaka ce nayi? Idan ka gaji da gani na ka aurar da Ni mana.” Sai kuma ta kalli MEEMA tace, “Sister come here and sit.”
Zama MEEMAN tayi a gefen Laɗifan
Idris da shima ya sami wuri ya zauna sai ya taɓe baki yace, “ai Ni bani da kuɗin miki aure, amma zan sanar wa Baba tunda naga alamu aike na kike yi. Wlh ina faɗa miki yarinya gwara kiyi auren ki kar ki biye ta tawa, Ni yaro ne har yanzu ban isa aure ba idan kika ce sai kin jira Ni ai kuwa zaki yi kwantai a gida don Ni ba take nake yi ba, bar gani na haka na san abun da yake zuciyar ki.”
Ɓare baki tayi kamar zata yi kuka tace, “Umma kin gansa ko ki ce ya dena ba na so, nima me zan yi da kai ai kayi min ƙanƙanta.”
Zaro ido waje yayi, zai yi magana kuma sai suka haɗa ido da Umman, sai ya kwashe da dariya yace, “Allah arziƙin ki ɗaya akwai Umma da sai na faɗa miki magana Al’ƙur’an.”
Umma tace, “ai Ni Idris ba kunyata kake ji ba da kayi maganar ka ma. Hmm Allah ya shirye ka baza ka sauya hali ba wlh.”
Dariya kawai yake yi
Laɗifa kuma bata kula shi ba illa riƙe hannun MEEMA da tayi tana kallon Umman nata tace, “Umma wannan ita ce MEEMA wacce nake baki labari ƙawata.”
Murmushi tayi Umman tace, “Masha Allah ga ta kyakykyawa, Ashe Zulaiha tana da yarinya kamar ta ban taɓa sani ba wlh. Sannu ƴar nan ga shi ko ruwa ban kawo miki ba, na zauna ina jin shirmen Idris.”
Dariya yayi yace, “ai Umma bata san me kike cewa ba. Bari Ni in taimaka in ɗauko mata ruwan.” Ya tashi izuwa wurin Fridge ɗin
Ita kuma Umma tace, “au ba ta jin Hausa ne?”
Laɗifa tace, “eh Umma, har yanzu ta kasa koya wlh, kuma kwanaki har na fara koya mata amma ko tunawa ba tayi.” Ta ƙare maganar tana dariya
“Allah Sarki.” Cewar Umman. “Da sannu zata iya tunda tana tare da mu Hausawa.”
Ruwan da Idris ya kawo mata MEEMAN ta amsa ta kurɓa kafin ta ajiye. Cike da sanyin murya tace da Laɗifan, “I’m worried about you, but I’m glad to see you. God get well soon.”
Murmushi Laɗifa tayi tace, “Ameen thanks MEEMA.”
Idris yace, ,”ai ta warke sosai. Get up and let’s go since her body is fine.”
Murguɗa masa baki Laɗifan tayi da cewa, “baza ta tashi ba, a nan zata zauna, kai ka tafi kai kaɗai.”
“Kina ji ko Umma? Yarinyar nan naki ta raina Ni wlh zan fasa mata baki.”
Umma tace, “ai kun fi kusa wlh babu ruwana.”
Hakan yasa Laɗifa tayi masa gwalo
Yayi ƙwafa shi kuma yana kaɗa mata yatsa alamun, “zai riƙe ta.”
Da haka dai suka zauna suna ta shirmen su, duk da Laɗifa ba ta jin daɗin jikin ta sai da ta biye mishi don Idris akwai wasa, ko ba ka so idan ya saka ka a gaba sai ka biye mishi
Daga baya ya tashi yace, “za su tafi.” Suka yi musu sallama suka fice. Kai tsaye wajen aiki suka koma.
✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️
Zuwan Uncle Hashim da ya tarar da yanda suke ta cin ma Hajiya mutunci ai sai ya hau su da faɗa. Dama ga shi akwai fushi nan da nan ya zuciya yace Jalila, “ta ɗauko mishi bindigan shi duk sai ya harbe su.”
Yanda suka ga Uncle Hashim ɗin yake yi ne tamkar be da Kai, sun san tsab zai iya harbe su kamar yanda yace, hakan yasa suka ɗibi jiki suka fice daga waje suna ta zage-zage a kan, “sai an basu gadon su.” Daƙyar suka bar gidan
Hajiya tace, “ku ne matsiyata, gado ne za’a raba a kawo muku naku har inda kuke, MEEMA kuma babu inda zata koma a nan zata zauna.” Nan ta saka Uncle Hashim ɗin da zancen, “idan MEEMA ta dawo yayi magana da ita a kan dukiyar Mahaifin nata”.
“Ai Hajiya ki bar zancen waɗannan matsiyatan, gadon ne baza a raba ba inga wanda zai sake tako mana gida yace zai ci mana mutunci, ƴan iska matsiyata.”
Hajiya tace, “a’a dole ne a raba ko don mamacin, kana ganin yanda suke tada jijiyan wuya duk wannan fitinan a kan Faruk zai ƙare, gwara a raba ko zai samu salama a cikin ƙabarin shi, inyaso ko can Riyadh ɗin ne sai ku je tare a san abun yi.”
Kansa kawai ya gyaɗa ya haura sama da sauri domin har yanzu a cikin fushi yake, bindigan na hannun shi tunda Jalilan ta kawo mishi, Da da farko ta ƙi kawo wa ne tana tsoron abun da zai biyo baya, sai da ya hau ta da faɗa sannan ta kawo a lokacin su kuma su Kawu Ali tuni sun fice a gidan.
Su Hajiya suna falo suna mayar da zancen duk kan su sai cece kuce suke yi suna tsine wa su Kawu Ali musamman yanda Ummee take ta faɗar mugun halin su, abubuwan da suke musu tun Faruk yana da rai, dama ba shi suke ƙauna ba dukiyar shi suke so, ga shi kuma yanzu sun biyo sahu har suna iƙirarin zasu aurawa ɗan su MEEMA ne.
✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️
*TWO DAYS AGO*
“Ke ɗaga kanki mana, wai lafiyan ki ƙalau? Na kula tunda muka zo school ɗin nan kike cikin damuwa karatun ma be dame ki ba yau”. Cewar Abida wacce ke zaune a kan deks tana taunan chewing gum idanun ta a kan Luwaira. Ganin ta ƙi ɗago kai yasa ta bugi bayan ta tana cewa, “wai Ni kike wa wulaƙanci Luwaira? Ina magana kin yi banza da Ni.”
Sai a lokacin ta ɗago kan nata ta zuba wa Abidan idanu. Fuskar ta babu walwala tace, “me kike so in CE miki? Abida ba na son takura don Allah ki bar Ni in huta.”
Taɓe baki tayi tana wani yatsina da taunan chewing gum ɗin bakin ta, sai da ta dage ta ɗirka ƙwai ta fasa shi tuss a kusa da fuskar Luwairan kafin tace, “kin san hali na, idan har baki kula Ni ba wlh na dinga damun ki kenan, bazai yiwu ace tun ɗazu muna tare dake kin bar Ni ina ta zuba Ni kaɗai ba, sannan kin wani luƙume kai a benci kamar wata kunkuru ki ce bazan tanka ba. Dalla ki faɗa min damuwar ki Ni fa ƙawar ki ce.”
Tsaki Luwaira ta ja, ta san halin Abida shiyasa ta buɗi baki tace, “baza ki gane ba koda nayi miki bayani Abida…”
Katse ta tayi da faɗin, “ba dai ki fahimtar da Ni bane ta yanda zan gane, idan kika faɗa min damuwar ki ai zan gane.”