MEEMA FAROUK Page 31 to 40

“Hmm matsala ce ta soyayya Abida. Ban taɓa sanar da ke ba amma tunda kin matsa zan sanar miki, na san zaki kalle Ni da wani irin kallo sabida abinda zaki ji ya fito a baki na. Soyayyar Umar Faruk ne yake son kashe Ni, duk yanda na so na jure amma abin ya faskara na kasa.”
“To ban gane ba. Wani Umar Faruk ɗin? Ko kin yi sabon saurayi ne?” Abidan ta tambaye ta tana tsare ta da ido
Ita kuma sai ta girgiza mata kai, sai da ta ɗan yi shiru na wasu daƙiƙu kafin tace, “Yayana Umar Faruk wanda kika sani, wanda muke gida ɗaya da shi; shi nake nufi.”
“Kutmar…” Ta saki wani zagi tana duro wa daga saman deks ɗin da take, sai kuma ta koma ta zauna a kan kujera tana facing ɗin Luwairan tace, “ke kar ki haukata Ni mana da yawa, yayan ki dai Yayan ki wanda na sani? Senator Umar Faruk na gidan ku; shi kike so? To ta ya hakan zai yiwu bayan na san Yayan ki ne?”
Kanta Luwaira ta sauke ƙasa tace, “Ba Yayana bane, Umar Faruk ba Momy ta haife shi ba, hasali ma Momyn mu ita ce take auran mahaifin shi ta zo da mu gidan nan, sannan bayan ya rasu mahaifin shi sai ta riƙe Umar Faruk a wurin ta tamkar ɗan da ta haifa, bamu da wani alaƙa da Umar Faruk bayan wannan da nake faɗa miki.”
“Tab ɗijam… Gaskiya ban taɓa tunanin ba Momy bane ta haife shi duba da yanda take tsananin ƙaunar sa da nuna masa kulawa, duk da a yawancin lokuta ina mamakin yanda shi ya fita daban da ku, sai dai kasancewar na ga hoton Mahaifin shi shiyasa naga kamanceceniyar su tare, hakan yasa nayi tunanin shi ɗin ya biyo Mahaifin ku ne, ashe duk wannan abun shi ba ɗan Momy bane?”
Gyaɗa mata kai tayi ta ƙara da cewa, “haka ne. Amma kuma maganar gaskiya sai dai Momy ba ta ƙaunar na aure shi.”
“To a kan me? Meyasa hakan bayan duk abinda na miji me ji da kanshi ya kai har ya zarta a so shi? A ko yaushe ina ma kaina kallon ban kai ajin da Umar Faruk zai so ni ba, bayan haka da tuni na afka a ƙaunar shi, sai dai ina ganin tabbas zan sha wahala duba da yanda rayuwar shi take, ba na tunanin zai iya so na domin babu ƙofan bayyana hakan, amma ke kuna gida ɗaya da shi kuma kin fi kowa sanin yanda yake ji da ke amma ki kasa sanar mishi, tun yaushe ma kike fama da dakon son shi?”
Luwaira tace, “tun da muka dawo gidan su da zama, kamar yanda nace miki Momy ba ta ƙaunata da shi saboda wani dalili wanda sirrin mu ne bazan iya faɗa miki ba.”
Shiru ne ya biyo bayan zancen nata, yayinda Abidan ta kafe ta da idanu tana tunani a ranta. Sai can kuma ta ja numfashi da cewa, “to yanzu ya zaki yi? Idan har kin amince Ni zan taimaka miki, ya kamata ace ke ce kika mallaki babban ƙadaran nan ba wata ba, dama ce a gare ki, Umar Faruk ya wuce duk yanda kike zato, idan da zaki san yanda ƴan mata suke rushing a kanshi zaki sha mamaki tunda na san ke kanki sheda ce, amma babu inda zancen shi be zagaya ba a duk faɗin garin nan, ba na son kiyi rashin shi ƙawata, duk yanda za’a yi ki mallake shi domin kun dace wlh, idan ba haka ba zaki mutu a ƙaunar shi, ke ya kamata ki fahimtar da shi halin da kike ciki, kar ki wani biye ta Momy duk da ban san dalilan ta ba, amma ina mamakin ta ya ya take son hana auren ku duk da tarin ƙaunar da take nuna mishi.”
Shiru Luwaira tayi, a zuciyar ta tana son ta bayyana mata sirrin su na son ganin bayan Umar Faruk domin su mallake komi nashi, amma kuma tana tsoro, shiyasa ta sauke numfashi tace, “zan faɗa miki dalili amma ba yanzu ba.”
Gyaɗa kanta kawai tayi kafin tace, “fine. Allah ya Kaimu lokacin, yanzu tashi mu je mu samu wani abu mu ci yunwa nake ji, duk chewing gum ɗin nan ya gama ƙwaƙwule min ɗan hanji.”
Tashi Luwaira tayi ta ɗauki jakan ta suka fice. Sai da suka je suka ci abinci sannan suka dawo aji, dayake lecture ɗaya suke dashi ana gamawa suka yi gida. Kowa drever’n gidan su ya zo ya ɗauke ta.
Luwaira na koma wa gida ta shiga Parlour ta tarar da Momy zaune ita da su Hafsah. Da gudu yaran suka isa wajen ta suka rungume ta suna mata Oyoyo
Murmushin ƙarfin hali ta sakar musu tana rungume su duka. Daga nan ta ja su zuwa kan sofa ta zauna ta ɗaura Yusra a jikin ta
Cikin murna Hafsah tace, “Aunty Dadyn mu ya dawo, an dawo da shi daga asibiti yanzu.”
“Da gaske?” Tafaɗa cike da farin ciki a zuciyar ta jin abinda Hafsan tace
“Eh Aunty. Amma bamu je mun gan shi ba har yanzu.”
“Ok ku tashi mu je yanzu sai in Kai ku wurin shi.”
Yanda Luwairan take rawan jiki ne yasa Momy ta bi ta da harara. Sai dai kasancewar bata kalle ta ba bata san ma tana yi ba. Har suka fice sannan tayi ƙwafa tana ɗauke kai daga kallon bakin ƙofan da suka fice.
Kai tsaye Part ɗin Umar Faruk suka wuce. Babu kowa a babban parlour’n don haka suka wuce ƙaramin parlour’n
Ai kuwa yana zaune a saman sofa daga shi sai baƙar Singlet a jikin sa da dogon wando Robber kamar na sanyi itama baƙa, ƙasan wandon da mazugi wanda ya bai wa wandon damar tsuke masa ƙafa. Gaban sa kuma computer ne yana dannawa a hankali idanun sa ƙirr a kai. Jin motsin su yasa ya ɗaga kai ya dube su, ganin su yasa ya saki yalwataccen murmushi wanda ke ƙara fito da zallan kyawun sa da kamalan sa. Nan da nan ya buɗe hannayen sa suka zo suka faɗa jikin sa ko wannen su na kiran sunan, “Dadyyyy.”
Ita kuma Luwaira hannayenta ta naɗe a ƙirji tana bin su da kallo tare da sakin murmushin da be kai har zuci ba, domin a zuciyar ta ji take yi kamar ta je ta ture su ita ta shiga faffaɗan ƙirjin sa da koda yaushe yake mata gizau a cikin mafarkin ta, bata da wani buri sama da ace an wayi gari ta mallaki wannan basaraken namijin me tsananin haiba da kwarjini gami da nagarta. Tabbas duk wanda ya sami Umar Faruk ya gama dace da duniya domin duk inda na miji ya kai da ji da kanshi ya kai, kyawu nasaba gami da kuɗi duk ya haɗa, ga uwa uba tsantsan ilmi da tawali’u da son ibada. Shiyasa sosai take baƙin ciki da kishi da yaran shi duk idan ta gansu maƙale dashi, ko kaɗan ba ta iya sukunin zuciya sai dai dauriya da take azawa kanta wajen ta ga ta ɓoye abin da ke cin ranta… Maganar da yayi mata shi ya dawo da ita dogon tunanin da ta afka wanda yasa har guntun murmushin da ke fuskar ta ya gushe bata sani ba, da sauri ta gyara kanta tana sake yalwata fuskar ta da wani ƙirƙirarren murmushin tace, “na’am Yaya.”
“Ya naga kin tsaya a nan? Come and sit.”
Zuwa tayi ta zauna a kan sofa wanda ke kallon nashi still tana murmushi
Sai ya ɗan ƙura mata ido tare da cewa, “me ke damun ki naga kamar kina da damuwa ko? Please faɗa min abinda ke damun ki domin ba na son ganin ki a cikin damuwa, ko kaɗan ba na jin daɗi.”
“Oh Yaya babu komi wlh, babu abinda ke damuwa.” Tafaɗa maganar tana sosa kai tare da sake faɗaɗa fuskarta da fara’a
Numfashi ya ja tunda shi dama ba Mutum bane me son takurawa makusantan shi. “Well. But kiyi haƙuri har yanzu ban cika miki alƙawarin ki ba. Ki ƙara haƙuri da Ni kinga yanzu nauyi ya hau kaina Ni kaina yanzu bani da lokacin kai na, amma insha Allahu i promise you wannan week ɗin motan ki zata shigo.”
“Allah yaya babu komi na san ai baka manta da Ni ba, Allah ya kai mu rai da lafiya.”
Murmushi yayi yace, “Amin.” Sai kuma ya mayar da kallon sa kan Yusra wacce ta langaɓe masa a jiki yace, “Ya dai my Baby?”
Tura baki tayi gaba tace, “Dady yunwa.”