MEEMA FAROUK 1-END

MEEMA FAROUK Page 41 to 50

Shima sai da ya shiga yayi wanka ya saka kayan barci sannan ya hau kan gadon shi. Kansa ya ɗaura a dantsen hannun shi yayi shiru, ya jima a haka sai kuma ya ja numfashi ya karkace kai ya ƙura wa wayan sa ido da ke ajiye a saman gadon. Kamar bazai ɗauka ba sai kuma ya saka hannun sa ya ɗauka ya sake laluba Numban MEEMA ya kira ta.

✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️

              A lokacin shigowar MEEMA kenan ɗaki, ta gama shirin ta tana ƙoƙarin kwanciya ta ji Ring ɗin wayan ta da ta ajiye a saman mirror tun kafin fitan ta. Zuwa tayi ta ɗauka sai kiran ya tsinke, nan ta ga an yi mata three missed calls, ɗan jim tayi bata kai ga yin wani tunani ba wani kiran ya sake shigo wa. Sai ta nufi bakin gadon ta zauna kana ta latsa wayan tayi peacking ta saka a kunne.

             Wani ajiyan zuciya me ƙarfi ya saki jin anyi peacking call ɗin. Sai da ya ɗan gyara kwanciyar sa kafin ya kai wayan kunne yana sallama

Sassanyan muryan sa da ta bugi kunnen ta ne yasa ta ɗan lumshe idanu tana buɗe su. Sai da ta ja seconni kafin ta amsa sallaman in a very low voice

Shiru ne ya gifta na ɗan wani lokaci

Kasancewar MEEMA bata san shi bane; ko kaɗan bata kawo shi ne ya kira ta ba duk da muryan nasa yayi mata kama da wanda ta taɓa ji, jin shiru sai ta ciro wayan ta duba ta ga yana tafiya sannan ta mayar ta sake faɗin, “hello who’s online?”

Lumshe idanu yayi saboda jin yanda muryan nata ya ratsa shi har cikin jiki da ɓargon shi, sai da ya gyara kwanciyar sa daƙyar ya buɗe baki wanda muryan nasa har shaƙewa tayi ya kirayi sunan ta

Hakan yasa tayi shiru tana tunani a ranta, a nan ne tunanin sa ya faɗo mata wadda ta tabbatar da tabbas shi ne. Bata amsa ba illa shirun da taci gaba da yi

Sai yace, “Weldon, I hope I didn’t bother you calling you last night?”

Duk da ta gane shi but hakan be sa tace, “But to whom am I talking?”

Shafa kansa yayi a hankali ya furta, “Are you talking to Umar Faruk, hope now you understand Me?”

Still shiru tayi

Sai yace, “Do you still understand MEEMA?”

Jin yanda ya kira sunan ta yasa ta lumshe idanuwan ta tana zamewa a kan gadon ta kwanta, still she’s silent

Hakan sai ya saka jikinsa yayi sanyi sosai, a hankali ya sake furta sunan ta

“Na’am.” She answered him briefly

“I don’t know why you don’t want to talk to me. Does that mean you don’t need me in your life? Tell me the truth.”

Shiru ta sake yi tana jin zuciyar ta na bugawa sosai fiye da sanda ta gane shi ne

“I know I’m restricting you but I’m sorry please, Don’t say I’m bothering you That’s not my nature, but I’m in a political situation. But I have nothing to worry about, I look forward to seeing you whenever you want to let me know.”

  

MEEMA rufe idanun ta kawai tayi tana sauraron muryan nashi wanda ke ratsa mata can cikin kunnuwa yana saukar mata da kasala da wani irin yanayi a jiki

“MEEMA.” Ya kira sunan ta in a slowly

Buɗe ido tayi a hankali tana amsa mishi

“I restrict you with my words?”

“Laà.”

Sai ya ja numfashi yace, “ok but did you allow me to call you? I don’t want to restrict you because I am a person who does not want to restricted.”

Shiru tayi kamar baza tayi magana ba sai tace, “Na’am.”

“Ok thanks. I will let you rest until tomorrow. Sleep well, dream of me please.”

Wani abu ne ta ji ya tsarga mata, tayi saurin mayar da idanun ta tana sauke numfashi

Shi kuma jin tayi shiru sai yayi mata sallama ya kashe wayan. Ajiye wa yayi yana saka hannu a fuskar sa ya shafo sajen sa yana me lumshe idanu, kyakykyawar fuskar ta kawai yake hango wa hakan yasa ya saki murmushi a hankali, sai ya gyara kwanciyar sa yana buɗe idanun sa ya kafa wa wuri ɗaya ido. Tunani yayi masa yawa dole ya miƙe zaune ya buga tagumi, sai kuma can ya koma ya kwanta yana mayar da idanun sa ya rufe still haka ya ci gaba da tunanin ta a ranshi.

          ******

           MEEMA kuma tunda ya kashe wayan itama ta kasa motsi, idanun ta a rufe har sai da ta ɗauki kusan mintuna ashirin a haka kafin ta tashi ta gyara kwanciyar ta sosai ta haye kan gadon, duk yanda ta so ta cire tunanin sa tayi barcin ta but ta kasa. Sai dai ɓarawo barci daga baya ya zo ya sure ta cike da mafarkin Umar Faruk.

???????????? 

*MEEMA FAROUK*

                        ????????????

*NA_NAFISA ISMA’IL*

*WATTPAD_UMMUDAHIRAH*

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT* ????????‍

*PERFECT WRITER’S ASSOCIATION* ????

“`( WE AIN’T PERFECT, BUT WE’RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS????)“`

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*

                 *SADAUKARWA*

_Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._

                             *NO_29*

  

            *THE FOLLOWING DAY*

           MEEMA tana tashi da safe da text ɗin Umar Faruk ta soma cin karo, haka kawai sai ta ji farin ciki ya ziyarci zuciyar ta, ta karanta text ɗin ya fi sau uku, yanda ya nuna kulawar sa a kanta da yanda ya damu da ita sosai ya saka ta farin ciki, shiyasa gaba ɗaya a lokacin ta ji ta a wani irin yanayi na nishaɗi wadda ta kasa gane meye ya saka ta wannan farin cikin sosai haka, duk da gefe ɗaya kuma tana jin wani irin faɗuwar gaba. shirin ta take yi but tunanin ta na a kanshi, har ta gama shiryawa yau ta sanja shiga, haka kawai yau take son saka kayan hausawa kasancewar tunda aka ɗinko mata bata taɓa amfani da ko ɗaya ba, atamfa ce kalan ruwan madara sai aka yi amfani da ja da baƙi wajen design ɗin flower, ɗinkin riga da skert ne da suka kama ta cif kasancewar ta me diri tubarakalla, sosai kayan suka yi mata kyau suka sake haska skin ɗin ta, ita kanta ta kasa ɗauke kai daga kallon surar jikin ta sabida yanda kayan suka yi mata kyau, sai juyi take yi a gaban mirror tana ƙara kallon kanta, murmushin kan fuskar ta ya kasa gushe wa still sai juyi take yi, sai da ta gaji don kanta kana ta ɗauki ɗankwalin da ninyan ɗaurawa, sai dai duk yanda ta so ta ɗaura ɗin ta kasa, sai cikuikuiye shi take yi tana ɗaura wa tana kwance wa but ya ƙi mata yanda take so, dole ta haƙura ta gyara gashin ta ta tufke shi a ƙeyan ta, kana ta ɗauki veil ja tayi Rolling da shi ya saukar mata a iya kafaɗa, sai tayi using da black flat shoes da saman ya kasance ja, yanda ta ga kayan sun yi mata ne yasa ta ɗauki after dress tana shirin saka wa, sai kuma tayi shiru tana ɗan tunani idanun ta a kan mirror tana kallon kanta, sai kuma ta mayar ta ajiye ba tare da ta saka ba sannan ta ɗauki Handbag ɗinta ta fice ba tare da ta shafa komi a face ɗin ta ba

Babu kowa a parlour’n kasancewar safiya ne, sai Zabba’u wacce take ta ƙoƙarin shirya Breakfast a saman table. Ganin ta yasa ta washe baki tana cewa,

“wow MEEMA, you look so good, the stuff looks so good to you.”

Ita kanta murmushi take zuba wa har ta iso kusa da ita tace, “thanks. Good morning.”

“Hope you are feeling well?”

“Alhamdulillah.” Tafaɗa tana jan ɗaya daga cikin kujerun dainning ɗin ta zauna. Sannan ta soma haɗa tea

Ita kuma Zabba’u surutu ta soma jan ta dashi a haka har ta gama shirya komi a inda ya dace. Kana ta juya ta koma kichen

While MEEMA sipping tea ɗin take yi a hankali tana ɗan lumshe idanuwan ta, tunani ne a ranta har ta gama shanye tea ɗin ta ajiye sannan ta tashi ta wuce ɗakin Hajiya

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button