MEEMA FAROUK 1-END

MEEMA FAROUK Page 41 to 50

Lokacin Hajiya na zaune a saman sallaya tana ta lazimin safe

Da shigar ta ta nufi wajenta tare da kiran sunan ta

Hakan yasa Hajiyan ta sakar mata murmushi tana kallon ta har ta iso ta duƙa a gaban ta

As usuals hannun ta ta kama ta sumbata tana kallon fuskar ta cike da murmushi a face ɗin ta tace, “Grandma good morning.”

Sai da ta shafa addu’ar nata kafin tace da ita, “Morning my dear. Today you have done very well, Masha Allah you look so cute.”

“Thanks Grandma.” Tafaɗa itama tana murmusawa

“You eat breakfast?”

“Na’am grandma. I’m go”.

“Ok God help give Luck. Take care of yourself?”

Amsa mata tayi tana sake mata peak a hannun ta kana ta tashi ta fice

While Hajiya ta raka ta da kallo.

              Sama ta nufa sabida su gaisa da Uncle Hashim. Kafin ta sauko ne Idris ya shigo gidan, yana zaune a Parlour suna surutu da Zabba’u ta sauko ƙasa

Shima yana ganin ta ya miƙe yana murza idanu, sai ya ɗan soma ɗaga kai Like yana leƙen bayan ta

Ita kuma tsayawa tayi tana kallon sa da mamaki, sai tace, “what you look?”

Waro ido yayi da cewa, “wai You mean like you? A mean MEEMA?”

Murmushi tayi coz ta gane tsokanar sa ne ta motsa

Itama Zabba’u da ke jin su dariya tayi tace, “Today you see her has changed a lot, she has joined us Hausa, she is very beautiful.”

Tafa hannayen sa yayi yana matsowa kusa da ita, fuskar sa cike da fara’a yace, “wow my cuty friend! I never thought you were so beautiful until today, have you seen? You’ve done very very well, You look so cute.” Ya ƙare maganar da ɗaura hannun sa a baki ya huro mata kiss ????

Sosai take dariya a lokacin nan wanda hakan ya bai wa dimples ɗin ta damar fito wa sosai

“I’ve never seen you laugh beauty. Laughter is so good for you. Please do it ok?” Yafaɗa still yana kallon ta yana murmushi

Bata ce komi ba illa sake ƙawata fuskar ta da smile da tayi

Shi kuma juyawa yayi ga Zabba’u yace, “to ranki ya daɗe! Yau dai bazan ci abincin ki ba sauri muke yi, idan Hajiya ta fito kice ina gaishe ta mu mun tafi.”

Tana dariya tace, “kace yau abinci na ya huta da tsegumi? yau babu sharhi. To a dawo lafiya Allah ya tsare.”

“Ai kar ki damu yau zan ci na rana a nan don haka ki girka da Ni, ki gode wa Allah ma yau ina sauri but anjima dai zamu haɗe ɗin.” Yafaɗa yana yin gaba ya bi MEEMA wacce har ta fice ma.

✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️

               Gaba ɗaya yau tunda Luwaira ta tashi babu walwala a tattare da ita, idanunta duk sun kaɗa sun yi jawur sabida kukan da ta sha a daren jiya, ga rashin barci da bata samu tayi ba. Shirin ta na school tayi saboda tana son ta je ta rubuta test, ba don haka ba ba ta tunanin zata iya zuwa ko ina a halin da take jin kanta. Koda ta fita Parlour ɗakin Momy ta shiga, ta sanar mata, “zata wuce school”.

Kallon ta Momy tayi tace, “ba dai kuka kika yi ba Luwaira?”

Shiru tayi tana ɗauke kanta gefe

Tsira mata idanu tayi na ɗan lokaci kafin ta kaɗa kai da cewa, “kin yi Breakfast ne da zaki tafi?”

“Ba na jin yunwa Momy.” Sai ta juya ta fice bata jira cewar ta ba

Ita kuma Momy ta raka ta da kallo har ta fice. A yanda take jin baƙin ciki a zuciyar ta da zata iya cire soyayyar Umar Faruk a zuciyar ƴar ta da tuni ta cire, sosai take baƙin ciki da hakan sai dai babu yanda zata yi, tabbas koda ta saka auren su ya yiwu ba ta jin zata kasa cika burin ta a kansa, dole ne sai ta mallaki komi nashi kafin hankalin ta zai kwanta, dukiyan sa da ƙadarorin sa duk mallakin su ne, ta san ita kanta Luwaira baza ta gane abinda take guje mata ba sai nan gaba. Amma kuma yanzu ta yanke shawaran barin ta ta auri Umar Faruk domin hakan shi ne maslaha a wajen su a kan ya auro wata ya kawo ta cikin gidan nan, inyaso daga baya bayan Luwaira ta haihu da shi sai su kashe shi su mallake komi ya dawo hannun su, a lokacin kuma zata san duk hanyar da zata bi domin fahimtar da Luwaira sannan ta mantar da ita shi a gaba ɗaya rayuwar ta, a lokacin zata auri wanda ya fi shi ta sake sabuwar rayuwa, su kuma burin su ya cika. Numfashi ta ja tana yalwata fuskarta da murmushi, tabbas ta san Umar Faruk yana jin maganar ta idan har ta ba shi umarnin auren Luwaira zai amince, amma ta ina zata bi ta fahimtar da shi ba tare da ya ɗarsa wani abu a cikin zuciyar sa ba?

                 ********

        Tana fita mota ta shiga drever ya ja ta zuwa school ɗin su. Koda ta shiga aji ta tarar da Abida tana zaune, sai dai kasancewar tayi latti a lokacin Malamin su ya shigo shiyasa basu yi wani magana ba suka natsu suka mayar da hankalin su kan karatun. Bayan ya fita ne wani ya shigo daga nan ne suka sami break

Abida wacce ta lura da yanayin Luwairan ita ta soma mata magana da tambayar abinda ke damun ta ganin halin da take ciki

Sai kawai Luwaira ta fashe mata da kuka saboda tsananin ƙuncin da ke damun ta

Da sauri ita kuma ta sanya hannu ta kama ta tana faɗin, “Haba Luwaira zaki tara mana mutane ne? Me ke damun ki meye ya saka ki kuka? Please kiyi shiru haka nan ki sanar min.”

Daƙyar ta iya tsakaita wa da kukan duk da bata yi shiru duka ba, daƙyar ta buɗe baki take sanar mata da zancen auren Umar Faruk, kana ta ƙara da cewa, “ban san ya zan yi ba Abida, ban san ya zan yi ba muddin ya ƙara aure, wlh ji nake yi kamar zan kashe kai na tsaban ƙunan da nake ji a raina, ina matuƙar ƙaunar sa amma be san ina yi ba, ya zan yi ne?”

Tausayin ta ne sosai ya kama Abida, tabbas so da zafi musamman idan kana yin shi a inda ba’a san ma kana yi ba, hakan ya fi komi ɗaci da tada hankali. Rarrashinta ta soma yi kafin tace, “Ni a nawa shawaran Luwaira ki fito fili ki sanar mishi kina ƙaunar shi, that is the only solution. Idan kika bar abun a ranki be san ma kina yi ba, idan da tun farko kin sanar mishi maybe da tuni be ga wancan ya ce yana so ba, kina fa da duk abinda ɗa namiji zai so ki, Ni a tsari na ba na barin abu ya cutar da Ni don haka dole ke ma ki samu hanya mafi sauƙi ki sanar mishi, sai ki ga me zai ce, idan ya amshi soyayyar ki Fine, Idan kuma be amsa ba dole mu san abin yi, ko ta wani hanya ne zamu bi domin ki samu zuciyar shi, ke ƙawata ce Luwaira zan taimaka miki a duk sanda kike neman taimako, ai yanzu kai ya waye sai mutum ya so yake barin damuwa ta karshi.”

Kallon ta Luwaira tayi yayinda idanun ta suke ci gaba da zubar da hawaye tace, “Abida wlh hanya ɗaya ce na san zan samu Umar Faruk cikin sauƙi, muddin Momy ta amince da auren mu na san shima zai amince ko ba ya so na, but She is still silent and refuses to tell me anything and yesterday she told me we would talk.”

“To meyasa baza ki same ta kuyi maganar ba? Inaga idan kun zauna kika sanar mata da halin da kike ciki zata fahimce ki, Ni abun yana ɗaure min kai meyasa ba ta son ki da shi ne?”

“Uhmm baza ki gane bane Abida.” Sai kuma tayi shiru tana ɗaura kanta a kan deks

Itama Abidan shiru tayi tana kallon ta, sai kuma tace, “idan har baza ki iya zuwa wajen ta kuyi magana ba ni zan je, Let’s go together sai in faɗa mata halin da kike ciki.”

Ɗago kai Luwaira tayi ta kalle ta, ba dai tace komi ba illa ɗauke kai da tayi tana saka hannu ta soma share hawayen ta

Sai Abidan ta dafa ta tace, “don Allah ki kwantar da hankalin ki, ki bi shawara nan yau ɗin nan ba sai gobe ba ki same shi ki sanar mishi, barin kashi a ciki ba ya maganin yunwa kina jina?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button