MEEMA FAROUK 1-END

MEEMA FAROUK Page 41 to 50

“Abida faɗan ba sauƙi ne da shi ba, da ace zan iya tunkaran shi da wannan kalman ai da tuni na daɗe da furta mishi, Umar Faruk ya wuce yanda kike zato, yana da wani irin kwarjini da kamalan da bazan iya tunkaran shi da zancen nan ba, sannan a yanda ya ɗauke Ni yana matuƙar girmama Ni a matsayin ƙanwar sa hakan ke saka wa nake kasa yin komi.”

“Haka nan zaki daure ƙawata”. Abida tafaɗa tana sake dafa ta, “na tabbata zaki iya, idan ba haka ba wankin hula ne zai kai ki ga dare, shawaran da zan baki kina da Numban shi ki tura mishi a text message, na tabbata zai fahimce ki idan har yana ƙaunar ki, do that please.”

Shiru tayi Luwairan tana kallon ta, sai kuma ta gyaɗa kanta tace, “insha Allahu I will try my best. Zan tura mishi zuwa anjima, amma kina ganin zai amince bayan ya sami wacce zai aura?”

Murmushi Abida tayi tace, “ba na tunanin zai ƙi amince wa sabida dole zai fahimci a halin da kike ciki, idan har bazai fasa wancan auren ba sai dai ya haɗa ku duka amma ba na tunanin zai ƙi amince miki, ko don halaccin da Momy tayi masa, ko domin kunyan ta bazai ƙi son ɗiyar ta ba.”

Daga haka shawara Abidan ta ci gaba da bata. Har sanda lecturer ya shigo sannan suka dakata suna gyara zaman su tare da ba shi attention ɗin su.

  

✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️

         Dariya sosai Laɗifa take sha saboda yanda MEEMA ta dage wajen furta yaren Hausa, tana koya mata ne amma duk kalma ɗaya idan ta faɗa sai ta tuntsire mata da dariya har da riƙe ciki

Tun MEEMAN ba ta kula ta itama tana tayata dariyan har dai ta gaji ta koma hararan ta, ganin ta ƙi denawa sai ta ɓata fuska kamar zata yi kuka tace, “Since you’re laughing at me I’ve stopped learning.”

Cikin dariyan Laɗifa tace, “I’m so sorry my dear. Wlh dariyan ne refused to stop, but…” Sai ta kama bakin ta sabida wani sabon dariyan da ya taho mata, daƙyar ta riƙe shi tana murmusawa tace, “But I’m sorry again.”

Still fuskarta a turɓune ta balla mata harara tana cewa, “I will not ask you to teach me again since you will laugh at me. I will go to Idris and he will teach me.”

Laɗifa bata kai ga yin magana ba wani saurayi yayi Nocking Yana turo ƙofan. Shima ɗaya daga cikin ma’aikatan wajen ne

And they all followed him, watching him

He smiled and said, “Hi how far?”

Laɗifa ta amsa mishi tana cewa, “Brother Idris ya turo ka waje na? I have not finished but I will finish now.”

“Eh shi ya turo Ni, amma duk da haka there are strangers who come to MEEMA.” Ya ƙare maganar da kallon MEEMAN wacce ta mayar da hankalin ta kan computer tana latsawa

Hakan yasa ta ɗago kai tana kallon sa sai dai bata furta komi ba

Laɗifa tace, “And strangers? Who are they?”

“I don’t know wlh, they were outside in the car, they demanded that I call MEEMA saying they would miss a message being sent.”

“Ok to zata zo”.

Daga haka shi kuma ya fice

Sai Laɗifan ta kalli MEEMA wacce itama ta zuba mata ido tace, “Is there anyone you expect to come to you?”

Girgiza kanta tayi sai kuma tace, “No, no one.”

“Ok get up let’s go check.”

Tashi tayi suka fice tare. Suna fita bakin Gate ɗin suka hangi baƙar mota ƙirar jip a fake, kasancewar glasses ɗin tited ne ba a ganin kowa daga ciki. Kai tsaye wajen motan suka nufa

Sun kusa isa sai wayan Laɗifa tayi Ring, tsayawa tayi a wajen tana peaking call ɗin

Hakan ya bai wa MEEMA damar karisa wa wajen motan tana bin ta da kallo

Sai kawai aka zuge ƙofa wani mutum ya fito da sauri, kafin ƙiftawar minti ɗaya har ya tura MEEMA a cikin motan ya rufe an ja motan a tsiyace

Laɗifa wacce take waya a kan idanun ta komi ya faru, sai dai kasancewar ta shiga shock ko motsi ta kasa sai da suka tafi ne sai ta kwatsa ihu tana bin Bayan motan, tuni ta jefar da wayan hannun ta sai zuba ihu take yi, ganin sun yi mata nisa da gaske ai sai ta zube a wurin tana ɗaura hannaye a kai tana ihun kiran sunan MEEMA

Kankace kobo har tsirarun mutanen da ke wajen sun nufo inda take don a zaton su wani abun ne ya same ta, kasancewar basu san me ta biyo ba shiyasa suke tambayar ta ba’asi?

Hannu kawai take nuna wa ta inda motan ta bi bakin ta na rawa tana kiran sunan MEEMA but sai dai gaba ɗaya muryan ta ba ya fita sabida tsaban ruɗu da tashin hankali.

???????????? 

*MEEMA FAROUK*

                     ????????????

*NA_NAFISA ISMA’IL*

*WATTPAD_UMMUDAHIRAH*

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT* ????????‍

*PERFECT WRITER’S ASSOCIATION* ????

“`( WE AIN’T PERFECT, BUT WE’RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS????)“`

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                   *P.W.A✍️*

               *SADAUKARWA*

_Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._

*SAKAMAKON SALLAH 1*

_Mun sani cewa a shika-shikan musulunci ɗin nan guda biyar bayan imani sai tsayar da sallah. Abdullahi Ibnu Mas’ud ya ce, “Na taɓa tambayar Manzon Allah cewa wane aiki na ɗan Adam Allah ya fi so?” Sai Annabi ya ce, “sallah”. Na sake cewa, “daga ita fa?” Sai Annabi ya ce, “kyautata wa iyaye”. Na sake cewa, “daga wannan fa?” Sai ya ce, “sai jihadi.”_

_Manzon Allah ya taɓa ce ma Abu Zarrin, “in Mutum yayi Sallah domin neman yardar Allah, duk zunuban sa za su zube Kamar yadda ganye yake zubewa daga itace,” Abin lura a nan shi ne sallah tana kawar da ƙananan zunubai. Manyan kam sai an tuba. Amma in Allah ya ga dama yana iya yafe sagiran da kaba’iran don sallar da mutum yayi. Amma kuma, ko can ba ayi ma musulmin ƙwarai kallon zai riƙa kuntuka kaba’ir, manyan laifuka. Ban da ma haka duk mai Sallah yakan yi istigfari ne, a ƙarshe ya roƙi Ubangiji ya gafarta masa zunuban sa, manya da ƙanana._

_Abu Sa’id Khudri, Allah ya yarda da shi ya ce, “ya taɓa jin Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi na cewa: “ko wace ɗaya daga cikin sallolin nan biyar tana kankare zunuban da suke tsakanin ta da wadda ta gabace ta.” Bari mu kawo misali da wani wanda aikin sa yake sa yayi butu-butu da ƙura. Akwai ƙoramu guda biyar suna gudana tsakanin gidan sa da inda yake aikin. In ya tashi zuwa gidan yakan yi wanka a kowace ƙorama. To, haka fa sakamakon yin sallolin nan biyar yake. Ana yafe duk wasu kurakurai da zunubai da suke tsakanin salloli biyu saboda istigfari da tuba da ake a kowace sallah._

_Manzon Allah yakan riƙa kawo mana ire-iren misalan nan ne don ya nuna mana irin ƙarfin da sallah take da shi wajen kawar da zunubai. Idan mun yi watsi da jin tausayi na Ubangiji, ba za mu kuka da kowa ba sai kan mu._

_Ba shakka ɗan Adam mai yin kurakurai ne. Muna iya yin ayyuka da dama wa’danda za su saɓa ma Ubangiji, mu kuma gamu da hushin sa da horon sa. Amma kuma mu duba irin jin ƙan da Ubangijin mu yake mamaye mu da shi. Ya nuna mana yadda za mu sadu da rahmar sa da jin ƙan sa. Abin takaici ne ƙwarai a ce mun bari wannan baiwa ta wuce mu, bamu kama ta mun riƙe da hannu bibbiyu ba. Rahmar Allah kusa take ƙwarai ga mai Sallah. Sallah falala ce daga Allah ya zo, ya gusar da abin da yake damun zuciya. Haka aka san Manzon Allah da Sahabban sa suke yi._

_Ɗan Adam yana yin Sallah tun safe har ya zuwa sallar isha’i da fatar dacewa da rahmar Allah. Bayan isha’in mutane sun kasu gida uku. Akwai waɗanda suke su gare su daren hanya ce ta samun lada da tubarraki. Waɗannan su ne masu raba dare suna bautar Allah, lokacin da wasu suke ta shara Barci. Su kam lada suke samu daga Ubangijin su. To, sai kuma mutanen da suke mayar da daren wani kaya mai nauyi da masifa gare su saboda yin ka-ce-na-ce cikin miyagun ayyuka da talatainin dare. Ba abin da daren yake kawo musu sai baƙin ciki. Sai kuma kashi na uku wanda ya ƙunshi masu hayewa gado kawai bayan sun gama isha’i. Su kam ba yabo ba fallasa. Irin su sun kauce wa hadisin Manzon Allah da yake cewa, “ku dimanci yin Sallah a gidajen ku ko baiwar Allah da rahmar Allah su iso gare ku.” Allah yasa mu dace duniya lahira._

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button