MEEMA FAROUK Page 41 to 50

????????????
*MEEMA FAROUK*
????????????
*NA_NAFISA ISMA’IL*
*WATTPAD_UMMUDAHIRAH*
*PERFECT WRITER’S ASSOCIATION* ????
“`( WE AIN’T PERFECT, BUT WE’RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS????)“`
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A*
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._
????????????????????????
_Sallah ta ƙwarai, ingantacciya, wadda aka yi ta cikin tawali’u da ƙasƙan da kai, tana haskaka zuciya, ta tsarkake ta, kana tana koya wa mai yin ta tsantsar hanyar Ibada da abubuwan da suka rataya a kansa, waɗanda suka shafi Ubangijin sa, don kuwa ta sallah ɗin ce girma da ɗaukakar Ubangiji za su tabbata a zuciyar sa. Sallah tana sa mutum ya zama sahihi, mai gaskiya da riƙon amana, mai fahimtar abubuwa, mai kunya mai auna kome yake yi, mai yawan kyauta. Tana daɗa nuna masa cewa dai Allah Ɗaya ne, yana kuma jin tsoron sa, yana kuma girmama shi. Ta yin Sallah ne yake inganta rayuwar sa, ya tsarkake zuciyar sa, ya nisanci ƙarya da makirci, zamba, fushi da fariya, gaba, tauye wa mutane haƙƙi, rowa, ƙeta da rashin biyayya, da dai sauran miyagun halaye._
_Sallah Ibada ce ta zuci da ta jiki. Mai yin ta zai haskaka da harshen Allah. Yin Sallah shi ne babbar alamar cikar imani, mafi darajar hanyoyin Ibada, kuma hanya mafi tabbata ta nuna godiya ga Allah, saboda tarin baiwar da ya yi mana. Yin watsi da Sallah yana nesanta mutum da Allah, ya rasa rahamar Sa da falalar sa da jin ƙan sa._
_Martabar sallah ta Kai ma cewa mutum ba ya iya barin ta acikin ko wane hali ya sami kansa. Dole ya kawo ta ko yana tafiya ko yana gida, ko cikin tsoro ko cikin aminci. Allah Ya sa mu dace._
*NO_31*
Ba kowa bane ya shigo sai Sajjad, yana sanye da baƙin wando da baƙin Jacket a jikin sa, ya ɗaura hulan sa a saman kanshi hannayen sa biyu a cikin aljihun Jacket ɗin
Yanda ya buɗe ƙofan ne yasa MEEMA bata hango shi ba don ta ƙara maƙure wa sosai a bayan ƙofan ta yanda ba za’a iya ganin ta ba. Numfashin da take sauke wa da ƙarfi ne yasa ta saka hannu ta rufe bakin ta
Har ya soma tafiya inda ya nufi ɗakin da take ba tare da ya rufe ƙofan ba. Sai ya juyo kuma da zummar rufewan kawai idanun sa suka faɗa kanta
Wani irin zaro idanu waje tayi saboda arba da tayi da kyakykyawar fuskar sa me kama da nata na asalin Bafulatani. Hakan yasa ta sake tamke bakin ta sosai nan da nan hawaye suka hau tseren gudu a kan dandamalin fuskar ta
Shi kuwa tuni ya nufo ta idanun sa a kanta
Ita ta kasa motsa wa sai da ta ga da gaske wajen ta ya nufo shiyasa ta wani irin bankaɗa ƙofan da ƙarfi ta kwasa a guje, wanda hakan yasa ta je ta bugu da ƙofan ta faɗi a bakin ƙofan ta kifa ciki. Wani irin kuka me ƙara ta saki sakamakon yanda ta bugu da gwiwowin ta, haka ma goshin ta tayi sujjada hakan yasa ta buge a wajen, take a wurin ta dena gani na wucin gadi saboda wani irin sarawa da kanta yayi lokaci ɗaya ta ɗauke numfashi
Shi kuwa tashin hankali ya shiga tuni ya isa wajen ta yana kwaɗa mata kira. Kafin kace kwabo ya ɗago ta yana ta faman kiran sunan ta, sai dai ganin kamar ba ta numfashi sai ya ɗauke ta da sauri yayi ɗakin ya ajiye ta a saman katifa, nan ya soma kiran sunan ta a rikice yana kai hannun sa saman goshin ta wanda tuni ya taso ya kumbura suntum
Saukar hannun nasa a saman goshin ta yasa ta ja wani gwauron numfashi wasu sabbin hawaye suna silmiyo mata tare da gangarawa ta gefen kunnuwan ta. Take ta buɗe idanun ta tana kallon sa sai dai ta kasa magana illa bakin ta da ke faman rawa tana son furta words but ta gaza, tsaban rikice wa tuni idanuwan ta sun sake yin jazur
Sajjad kamar zai yi kuka ya zare hannun nasa a saman goshin, cike da tsantsan tausayin ta domin ya san ba kaɗan ba ta bugu da faɗin da tayi ya soma mata sannu. Kana kuma ya sake kai hannu da zummar taɓa mata wurin idanun sa a cikin ƙwayan nata
Wani irin zabura tayi kamar an tsikare ta. Nan da nan ta ture shi tana ja da baya tare da ƙoƙarin tashi ta gudu
Hakan da ya gani yasa ya tashi ya kamo ta yana shirin mayar da ita
Nan kuwa suka fara kokawa don iya ƙarfinta ta dage tana ƙoƙarin ƙwatan kanta ta bar ɗakin, yanda ya dage sai ya hana ta fita yasa ta yanka kuka tare da faɗin, “Please let me go. What have I done to you? Why did you bring me here? What are you going to do to me? Let me go and don’t kill me.”
Dariya ma maganar nata ta ƙarshe ta ba shi. Sai ya riƙo ta gam yana wani faman narke fuska saboda yanda ya ji tattausan skin ɗin ta na ƙara haɗe wa da nashi skin ɗin. A hankali ya saki yalwataccen murmushi me ƙara wa fuskar sa kyau. Cikin amon muryan shi wanda zai sa ka gane yana a cikin tsantsan farin ciki yace, “Stop bothering yourself Baby, this is my house and you have come and you will never go out, you know I love you and that is why I took you back and you are here. You hate me and said you will not marry me. I will never tolerate you unless I marry you.” Sai ya ɗan yi shiru yana kallon yanda take tsiyayar da hawaye tamkar an kunna famfo, yatsan shi yasa ya lakuto hawayen, sai kuma ya narke fuska tare da kai tafin hannun nasa guda ɗaya da zummar goge mata gaba ɗaya hawayen yana cewa, “Stop bothering me with your tears, I don’t want to see you in trouble Baby…” dole ya tsayar da maganar nasa ganin ta kawar da kanta ta ƙi tsayawa. Sai ya ɗan yi murmushi ya kai fuskar sa ya soma shinshinan daga wuyan ta zuwa fuskarta
Hakan da ta gani ne ta tattakura ta hankaɗa shi, daƙyar ta iya ƙwace jikin ta tana zame wa a ƙasa. Cikin rusa kuka sosai take cewa. “Please help me get Me back, please?” Ta ƙare maganar tana haɗa hannayen ta waje ɗaya alamun roƙo, gaba ɗaya ta rikice ta gama kiɗime wa sai kuka take yi
Shi kuwa tsayawa yayi yana kallon ta na tsawon lokaci. Kafin kuma can ya ɗan ja fasali yana duƙawa a gaban ta, hannu ya saka a haɓar ta ya ɗago fuskar ta na kallon fuskar sa
Sai dai ita tuni ta mayar da idanunta ta rufe su ruf tana faman shashsheƙa, gaba ɗaya ta kasa motsawa bare ta ƙwace fuskar ta
Shi kuma magana ya soma da faɗin, “If you want me to let you leave this house, there must be a condition.”
Da sauri ta buɗe idanun ta jazur ta zuba mishi ba tare da ta furta komi ba
Sai ya ci gaba da faɗin, “I will marry you. We will be married here. I will marry you before you leave this house. I did not bring you here so that you can go easily. I brought you here so that we can live together. I love you so much That’s why I did this to you. I don’t want to rape you That’s why I decided to bring you here because I married you. If you are ready now I will go and bring those who will marry us.”
Wani irin suya da tafarfasa zuciyar ta take yi da jin zantukan sa, cikin baƙin ciki da fusata tace, “Who are you to steal me and say you are going to marry me? You are lying, you are not good enough to marry me wlh, I don’t love you at all in my heart, hurry me back home before I kill you, I will kill you!” Ta ƙare maganar da ƙara tana kai hannayenta ta shaƙo mishi wuya