MEEMA FAROUK 1-END

MEEMA FAROUK Page 41 to 50

Da sauri ya saka hannun sa ya ɓanɓare mata daƙyar, har nishi yake yi tsaban ya soma wahala, sosai ya tsorata saboda yanda ta birkice masa lokaci ɗaya a dole sai ta bar gidan, daƙyar yake iya riƙe ta sai kokawa take yi da shi, hakan yasa ya samu dama ya taska mata mari idanun sa sun kaɗa sun yi jazur

Take a nan tayi ƙasa tana ƙwalla ƙara tare da riƙe kumatun ta duka biyun saboda tsananin azaban da ya ratsa ta

Shi kuma cikin fusata ya duƙa ya riƙo fuskarta ta yanda zata kalle shi dole yace, “Focus your mind on your body. I don’t want to argue. If you say you’re going to argue with me and I’ll make you suffer, I’ll surprise you. I have to marry you because you’re mine alone.” Sai ya nuna kansa da yatsa yana zare mata idanu yace, “I am Sajjad Aliyu Ahmad Riskuwa and you are mine, there is no one who can stop me from marrying you. From now on, you will not be able to leave this house. Here we will continue to live until you trust me, and I will teach your heart my love because you must love Me, we are here with you.” Sai ya sake ta yana tashi ya fice ba tare da ya tsaya ba, rufe ƙofan yayi ya nufi parlour’n yana ta zagaye. Sai safa da marya yake yi kafin kuma daga baya ya fice zuwa haraban gidan

Yana nan tsaye sai ga wani mota ta danna horn daga wajen Gate, hakan yasa ya fita ya leƙa sannan ya buɗe masa Gate ɗin. Motan cike take da kaya haka sukai ta fito da su tare da Mutumin da ya tuƙo motan suka yi ta shiga da shi ciki, yawanci kayan abinci ne sai kujeru guda biyu da t.v da wasu abubuwan amfani. Sai da suka haɗa t.vn kafin Mutumin yayi masa sallama ya fice

Shi kuma ya zauna a kan sofa yana kwantar da kansa tare da lumshe idanuwan sa, duk bugun da MEEMA take yi a ƙofa suna jin ta amma babu wanda yayi magana, ko a yanzu ɗin ma be yi yunƙurin tashi ya je ya duba ta ba illa ɗaukan wayan sa da yayi wanda ke ƙaran kira, ganin sunan Umma sai yayi peacking yana kara wa a kunne

“Hello Sajjad”.

“Na’am Mom.” Yafaɗa a kasalance wanda hakan ke nuni da cewan a gajiye yake

Ita kuma can cikin tashin hankali take magana da cewa, “wai ina ka shiga ne tun safe baka dawo ba? Ka san dai ba lafiya ne da kai ba meyasa zaka fita ka ƙi dawowa?”

Sai da ta ajiye numfashi kafin ya buɗe baki murya a narke yace, “Mom ki kwantar da hankalin ki ina nan lafiya. Sai gobe zan dawo na je gidan Aboki na ne.”

“Amma meyasa baka faɗa mana ba ga Abban ku yana ta faɗa?”

“Ki ba shi haƙuri Mom Ni bazan dawo ba sai gobe. Kuma zan kula da kaina kar ki damu.”

Shiru tayi tana sauraron yanda yake fitar da numfashi da ƙarfi, can kuma sai tace, “Anya kana lafiya Sajjad? Meyasa ba ka jin magana ne baza ka haƙura da yarinyar nan ba? gaba ɗaya ka tsangwami kanka ka hana kanka sukuni sai kace ita kaɗai ce Autar mata?”

“Umma baza ki gane ba but wlh ina tsananin ƙaunar ta, ni bazan iya rabuwa da ita ba komi zan iya yi a kanta idan har zan same ta. Sai anjima zan yi sallah.” Be bari tayi magana ba ya tsinke wayan, tashi yayi ya shiga Toilet ɗin parlour’n ya ɗaura alwala sannan ya fito ya gabatar da salla a parlour’n, ya haɗa da sallan isha’i kasancewar lokaci yayi sannan ya fice a gidan, motan sa ya shiga ya bar gidan da mugun gudu.

              *********

        MEEMA kuwa tayi bugun ƙofan har ta gaji ta zame a bakin ƙofan tana ta rusa kuka, sai kiran sunan sa take yi tana zagin shi ta uwa ta uba domin ya zo ya buɗe mata but ko sauraron ta be yi ba, daga ƙarshe haka ta haɗa kai da gwiwa tana gunjin kuka har da su majinu, ta kasa yin shiru har kanta tuni ya ɗau zafi sakamakon tashin hankalin da take ciki ga tsoro da ya mamaye ta. Tana nan zaune ko motsi ba ta yi ga wahalar yunwa da ƙishin ruwa da ya gama galabaitar da ita, tun safe rabon ta da saka wani abu a ciki sanda ta fito gida, ganin ta rasa kuzarin ta sai ta faɗi a wurin a yashe idanuwan ta a rufe but hawayen ciki na ta kwaranya domin sun kasa ƙafe wa. Tana jin sanda Sajjad ya dawo gidan ya buɗo ƙofan falo, hakan yasa ta tashi zumbur tana kafa wa ƙofan ɗakin ido

Take a nan sai ga shi ya buɗe ya shigo. Da kallo ya bi ta yana riƙe da baƙin leda a hannun sa, hannun sa ɗaya ya saka a cikin aljihun wandon sa yana sakin killer smile, kamar bazai yi magana ba sai kuma yace, “My baby, you are bothering me yourself. Why don’t you understand? This is your house. Let go of your body. I have nothing to do with you.”

Hannayen ta biyu ta haɗa idanun ta jazur a kansa, cike da shashsheƙan kuka wanda maganar nata ke fita a hankali tace, “please, please help me Please, let Me go please I beg you”.

Dariya yayi da ajiye ledan a wajen, sai da ya duƙa ya riƙo hannayen nata duka biyun ya haɗa da nashi ya matse

Da idanu kaɗai take bin shi domin ta kasa cewa uffan, illa sake matso wasu sabbin hawayen da take yi suna fita a hankali yayinda zuciyar ta tamkar zata fashe sabida tsaban baƙin ciki da tsantsan tsanar sa

While Shima kallon nata yake yi, sai kuma ya saka ɗaya hannun nasa a kafaɗan ta ya soma shafa wa har zuwa saman cuty face ɗin ta da ya sanja kala shima yayi jazur tsaban kukan da ta sha, har wani muku-muku yayi

Kasa jure wa tayi ta fizge jikin ta da sauri tana matsa wa baya still tana zubar da hawaye

“Baby, I will never let you leave this house until I own you. I say you are mine, I love yo. I love you! Why don’t you understand me? What have I done to you in your life that you hate me? I love you, why do you not love Me?”

“I don’t like you. I don’t want you to insist. Take me home.” Tayi maganar tana fashe wa da sabon wani kukan me tsuma rai

Ɗan kallon ledan gaban sa yayi kafin ya mayar da idanun sa a kanta, ya ɗan shafa tulin gashin shi yana wani lumshe idanun sa, still kuma ya buɗe a kanta kana yace, “I know you are hungry. Here is the food I brought for you to take and eat. Please I do not want you to starve. Tomorrow I will be married to you.” Sai ya miƙe da zummar fice wa

Da sauri ta taso ta biyo bayan sa tana faɗin, “You’re lying, I won’t marry you, I don’t love you, I don’t love you!….”

Maganar nata ne ya ƙage sakamakon haɗa ta da bango da yayi ya haɗe bakin su waje ɗaya domin ko kaɗan ya tsani kalman tsanar shi da take faɗa a koda yaushe, bazai iya jura ba.

_Just the beginning my FAN’S, ku gyara zama kawai yanzu ne za’a soma Labarin. Abu ɗaya kawai nake nema very more and More Comments, Idan babu uhmm zaku riƙa ji na yau ku neme ni gobe ku rasa, haka zamu riƙa tafiya, yau akwai gobe babu._

08146470539

???????????? 

*MEEMA FAROUK*

                        ????????????

*NA_NAFISA ISMA’IL*

*WATTPAD_UMMUDAHIRAH*

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT*????????‍

*PERFECT WRITER’S ASSOCIATION* ????

“`( WE AIN’T PERFECT, BUT WE’RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS????)“`

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*

                 *SADAUKARWA*

_Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._

                             *NO_32*

             Zaro manyan idanuwanta tayi waje zuciyar ta na wani irin bugawa da ƙarfi, yanda take jin lokaci ɗaya sauran kuzarin ta da take dashi ya tafi, daƙyar ta iya tattaro jarumtar ta ta soma kokawan ƙwatan kanta daga nanuƙetan da yayi a jikin sa, duk yanda taso ta ƙwace ta gaza domin ƙarfi ya saka mata. Sosai take hawaye a wannan lokacin zuciyar ta na zafi da baƙin ciki

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button