MEEMA FAROUK 1-END

MEEMA FAROUK Page 41 to 50

Sai da ya gaji don kansa kafin ya zare bakin sa yana ajiye fuskar sa a saman nata yayinda yake fitar da numfashi a hankali. Trying to put his mouth back into her mouth again he wanted to do sabida be gaji ba, the taste in her mouth and the desire he felt completely began to lose his focus

Sai dai tuni tayi ƙasa tana sakin kuka me ban tausayi tare da ƙudundune kanta a ƙafafuwan ta

Kasa haƙura yayi ya bi ta ƙasan

Yanda yake faman shige mata ne yasa ta tunkuɗe shi da ƙarfinta ta tashi da gudu ta koma saman katifan tana faɗa wa taci gaba da rera kukan ta

Shi kuma ya kasa motsa wa saboda rasa kuzarin sa da yayi. Sai da ya jima a wurin yana mayar da numfashi kafin ya tashi ya fice, a kan sofa ya faɗa yana ajiyan zuciya. Idanun sa ya mayar ya rufe be sake motsa wa ba, sai can daga baya ya tashi ya je ya rufe mata ƙofan ya saka keey

Tana jin shi bata iya motsa wa ba kuma har a lokacin ta kasa yin shiru, yanda zuciyar ta ke tafarfasa ji take yi kamar ta kashe shi, a duk soconni ƙara jin tsanar shi take yi a zuciya. Kuka ta sake saki tuna su Hajiya da tayi, sai ta soma kiran sunan su tana neman taimako a wajen su. Ga azababben yunwa da yake cin ta amma ta kasa motsa wa bare ta ci, ta gummaci ta zauna da yunwa. A haka ta maƙure a ƙarshen katifan har dare ya tsala bata kwanta ba, gaba ɗaya barci ya ƙwaurace mata. Sai da ta ji tana buƙatar shiga Toilet ne kafin ta rarrafa ta shiga, sannan ne da zata fito tayo alwala tazo tsakiyar ɗakin a zaune ta soma gabatar wa saboda rashin ƙwarin jiki, daga ita sai guntun veil ɗin ta, gaba ɗaya sallolin da ake bin ta ta kawo tana yi tana kuka, sai da ta idar ta koma roƙon Allah kamar zata shiɗe sabida kukan da take yi. Bayan ta idar a wurin ta kwanta ta rufe idanuwan ta, sai dai har yanzu bata dena zubar da hawaye ba. Gaba ɗaya tsawon daren nan a idanun ta ya ƙare, duk satan barci be iya satan ta ba, ko da barcin ya fizge ta sai ta farka ta ci gaba da kukan ta, daga ƙarshe da ta ji azaba cikin ta na mata ciwo sosai babu shiri ta janyo ledan nan ta soma neman abun da zata ci, kaza ne da Fresh Yo a ciki, haka ta zauna tayi ta tusa wa a cikin ta tana zubar da hawaye. Bayan ta gama ta koma kan katifan ta kwanta. Bata runtsa ba sai da asuba tayi sannan ta samu barci ya sure ta.

              Washe gari Sajjad fita yayi ya nufi super market ya yo mata siyayyan kayan saka wa da abubuwan da ya san zata buƙata. Bayan ya dawo ya ajiye mata yayi wanka ya sanja kaya ya hau motan shi ya wuce Yola, zuciyar sa cike da burin yanda zai yi ya mallake ta da zaran ya dawo, don bazai iya jure wa ba yana bukatar ta sosai a rayuwar sa, tuni ya soma tunanin yanda zai yi ya aure ta ba tare da ta kawo masa matsala ba. Kafin ma ya kai tuni ya samo idea shiyasa nan da nan ya yalwata fuskar sa da murmushi yana faman ci je leɓe da shafa kanshi da ɗaya hannun sa, ɗayan kuma yana kan sitiyarin motan.

✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️

           Kwance yake a saman ƙaton gadon sa yayinda idanuwan sa suke rufe ruf, gaba ɗaya kyakykyawar fuskar sa ta bayyana tsantsan damuwar da yake ciki, ko kaɗan idan ka lura ba ya cikin walwalan sa wanda hakan ne yasa shi kasa yin komi tun farar safiyar nan da ya tashi, tunani da damuwa sun yi masa katutu, ji yake tamkar yayi ta kurma ihu tsaban yanda yake ji, sai dai babu hali, ba shi da wanda zai iya bayyana wa halin da yake ciki bare ya rarrashe shi, zuciyar sa zafi take mishi sosai shiyasa yayi yunƙurin tashi daga kan gadon. Sauko da ƙafafuwan sa yayi a hankali yana zama sosai a bakin gadon, kana ya saka hannu ya janyo murfin drowan gadon yana saka hannu ya ɗauki magungunan shi, buɗe wa yayi ya cire wadanda zai sha kana ya tashi a hankali jiki babu ƙwari ya wuce bakin Fridge, a nan ya ciro ruwa ya buɗe ya afa maganin tare da korawa da ruwan, ya jima a wajen before ya dawo gefen gadon nasa ya zauna, ya riƙe kanshi yana me mayar da idanun sa ya rufe. Yanda fuskar MEEMA ta bayyana mishi a cikin ƙwayar idanun sa ne yasa ya buɗe idanun da sauri. Numfashi ya ja yana mayar da numfashin akai-akai. Almost two minutes yana a haka kafin ya kai duban sa kan agogon ɗakin da ke manne can sama. Lumshe idanun sa yayi yana mayar da idanun kan wayoyin sa da ke ajiye a saman drower, sai ya saka dogayen hannun sa ya ɗauka ya kunna, kasancewar tun jiya ya bar su a kashe sai da ya jira wayoyin suka gama kunnuwa saƙonni suka soma shigowa sannan ya bi su ɗaya bayan ɗaya ya soma karanta wa. A nan ne ya ga Numban Luwaira ɗauke da saƙo, abun da saƙon ya ƙunsa ne yasa shi sake ware manyan idanuwan sa da suke a lumshe yana sake bibiyan karatun, ya karanta ya fi sau uku yana son fahimtar inda saƙon ya ƙunsa, yayinda zuciyar sa cike take da mamakin ganin saƙon me ɗauke da kalaman soyayya tare da bayyana tsantsan ƙaunar da take mishi. Ya kasa yarda shi ta turo ma wa shiyasa take a nan zuciyar sa ta ba shi tunanin, “sai dai mistake ne yasa ta tura masa.” Tunanin hakan ne yasa ya ɗan saki numfashi yana ajiye wayan sannan ya miƙe ya wuce Toilet, wanka yayi ya fito ya shirya a cikin fararen kaya wanda ya zame masa kamar ɗabi’a domin a cikin kayan sa ya fi ƙaunar fararen kaya shiyasa suka fi yawa sosai, zai yi wuya kaga wasu kaloli idan har ba fari ko milk ba, sai kuma suit wanda be cika saka su ba sai idan zai yi dogon zango. Kayan sun yi masa kyau ainun sun sake haska shi sosai, ya ɗana hulan shi wanda ya ƙara fito da tsantsan cuty face ɗin sa me zagaye da siririn saje wanda suka sha mayuka suka yi luff a skin ɗin shi, sai ɗan guntun gemu wanda ba kowa ke kula akwai ɗin ba sai idan kayi mishi kallon fess. Turaruka yayi wanka da su a jikin sa nan da nan ɗakin ya gume da ƙamshi sannan ya zura takalman sa cover tare da ɗaukan wayoyin sa ya tusa a aljihu, kana ya riƙe keeys ɗin mota ya fice. Sanda ya sauka downstairs kai tsaye dainning ya nufa. Raguwar ruwan zafin da ya dafa wa su Hafsa zasu je school suka sha tea; shi ya ɗauka ya zuba sauran a Cup ya haɗa tea me kauri ya shanye a lokaci ɗaya ba tare da yayi amfani da bread ɗin da ke wajen ba. Bayan ya gama ya fice

Da gudu securities ɗin sa suka nufo sa suna mishi Barka da safiya

Kasancewar yau ba ya jin daɗi kuma ba ya cikin walwalan shi hakan yasa ya ɗaga musu hannu fuskar nan a murtuke

Ɗaya daga cikin securities ɗin har ya soma kawo mishi complain na aikin Office ɗin shi kasancewar makaran da yayi be fita da wuri ba, hakan yasa ya samu saƙonni da waɗanda suke jiran sa da kuma meetings ɗin da ake da su

Be bari security ɗin yayi magana ba ya ɗaga mishi hannu tare da yin gaba ya nufi Part ɗin Momy. Da shigan sa parlour’n ya samu waje ya zauna tare da kai gaisuwa wajen ta

Ita kuma cikin fara’a da nuna kulawan ta a kanshi ta amsa mishi, kana kuma ta sauya fuskar ta da damuwa tare da tambayar sa halin da ake ciki a game da ɓacewar MEEMA?

Wani irin suka ya ji a zuciyar sa sakamakon kiran sunan nata da tayi, sosai a wannan lokacin fuskar sa ta sake shiga damuwa da tsantsan baƙin cikin da yake ciki. A hankali ya furta mata, “har yanzu babu wani ci gaba Momy, but ban yi waya da Hashim ba amma yanzu nake tunanin kiran sa.”

Fuskar sa kawai take kallo, ita kanta ta gane damuwar da yake ciki shiyasa a ranta taji sanyi sosai, sai dai a fuska sai ta sake nuna damuwar ta tare da faɗin, “Allah ya bayyana ta, insha Allahu ko wane ne ya ɗauke ta sai asirin sa ya tonu, ko kaɗan ba na son ganin ka a damuwa my son, ka kwantar da hankalin ka insha Allahu babu abinda zai same ta, babu shakka masu garkuwa da mutane ne suka ɗauke ta.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button