MEEMA FAROUK Page 41 to 50

“Haka ne Mom. Mu ma hakan muke tunani.” Sannan sai ya ɗan ja fasali kana yace, “zan tafi Office nayi late.”
Addu’a ta soma jero masa kamar ko yaushe da ta saba
Shi kuma yana amsa wa da, “Amin.” cike da jin daɗi a ransa, hakan yasa kaso ashirin bisa ɗari a cikin damuwar sa ya ji sun yaye, har yana jin zuciyar sa na masa sanyi tana rage zafi da raɗaɗin da take mishi. Daga nan ya miƙe yana shirin fice wa
A lokacin ne Luwaira ta fito a cikin shirin ta na zuwa school tana gaishe shi
Ɗan tsaya wa yayi yana kallon ta, sai da ya ɗan ƙura mata idanu kafin ya saki murmushi tare da amsa mata yana tambayar lafiyan ta da yanda ta tashi?
Ita kuma cikin murmushi ta amsa mishi zuciyar ta na sake yalwata da farin ciki, a ranta tunani take yi, “shin yaga saƙon ta ko kuwa har yanzu be gani bane da har yanzu be dawo mata da reply ba?” Sai dai zuciyar ta tana ƙara mata ƙwarin gwiwa a kan, “tabbas ya gani sai dai idan shi ne be yi ninyan dawo mata da reply ba,” amma kuma ta saka a ranta, “muddin taci gaba da jin shiru daga wajen sa to zata sake tura masa wani”.
Umar Farouk tuni ya fice daga Part ɗin, sai da ya koma sashin shi ya ɗauko maganin shi kafin ya dawo ya shiga motan da aka buɗe masa. Kana drever ya ja suka bar gidan, yayinda shi kuma yake ƙoƙarin kiran Hashim a cikin wayan sa.
✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️
Sajjad be dawo Kaduna ba sai washe garin ranan, da kaya niƙi-niƙi ya dawo
A sanda ya shigo gidan MEEMA na zaune a ɗaki a saman katifan ta haɗa kai da gwiwa, duk ta wani firirice ta yamushe saboda tashin hankali da zullumi, cuty face ɗin ta ya sake ramewa yayi fayau da shi tamkar wata me ciwo, to zan iya cewa ciwon take yi saboda a halin da take ciki, jikin ta har zafi yayi sabida a halin da take ciki, izuwa yanzu kumburin da goshin ta yayi sakamakon faɗin da tayi har ya saɓe. Tana jin motsin Sajjad ta ɗago rinannun idanuwan ta ta bi shi da kallo wanda ke nuni da tsantsan tsanar da take mishi
Shi kuwa kanshi tsaye wajen ta ya nufa ya zube mata ledojin gaban sa yana cewa, “morning my dear. I have brought you food and clothes, bathe and change your clothes.”
Uffan bata ce mishi ba sabida wani ƙululun baƙin ciki da ya tokare mata wuya. Lokaci ɗaya ruwan hawaye suka cika mata cikin idanu, sai tayi sauri ta ɗauke kanta tana mayar wa a kan cinyan ta
Shi kuma be ce komi ba ya juya ya fice. Kai tsaye kichen ya nufa ya kunna gas ya ciro tukunya a cikin kayan da mutumin jiya ya kawo mishi. Ya ɗaura a gas bayan ya kunna, silale indomie yayi ba tare da kayan miya ba illa maggi kaɗai da ya saka, sai ya juye a Plate guda biyu ya wuce ɗakin MEEMA ya ajiye mata ɗaya, idanun sa a kanta yace, “baby wake up and eat food.” Daga haka ya juya ya koma Parlour, kunna t.v yayi ya zauna ya soma kallo yana cin indomien, sai can kuma da ya gama ya koma ɗakin MEEMA. Ganin ta zaune har yanzu a yanda take sai ya kama ƙugu yana kallon ta, “Baby do you want me to feed you myself? If you not wake up and eat I’m going to feed you myself, and don’t say I’m kidding you.”
Wani irin kallo ta watsa mishi kana tace, “I don’t eat, I don’t want to eat, what do you care about with Me?”
Murmushi yayi cike da tsantsan ƙaunar ta yace, “baby I love you so much, You are very impressed with me, your character and everything I like. I love you so much. I have to own you today, I hope you will join me because I can’t stand to see you like that? I need you in my life.” Sai kuma ya fice ya dawo ɗauke da wani magani a hannun sa, buɗe wa yayi ya ciri guda uku a hannun sa kana ya nufe ta
Babu zato babu tsammani sai gani tayi ya janyo ta jikin sa. Nan da nan jikin ta ya soma rawa tana shirin buɗe baki tayi ihu sai ya saka hannun sa wanda ke da maganin ya toshe mata baki dashi, yanda take numfarfashi tsaban ya liƙe mata baki da hanci lokaci ɗaya ta haɗiye maganin a cikin bakin ta hawaye na saukar mata a kunci
Murmushi yayi ganin ya samu nasara. Sai ya janyo Plate ɗin abincin ya ɗibo zai bata
Take ta buge hannun sa tana ƙoƙarin tashi tare da rushe wa da kuka
Zaunar da ita yayi ya haɗa ta da jikin sa
Ko kaɗan ta kasa motsi sabida yanda ya matse ta nan ta soma ƙaƙarin amai
Hakan yasa ya haɗe bakin su waje ɗaya and he slowly sucked on her
Duk yanda ta so ta ƙwace jikin ta ta kasa, domin gaba ɗaya ta rasa kuzarin ta, wani irin yanayi take ji yayinda duniyar ta soma juya mata, gaba ɗaya ta soma rasa tunanin ta daga ƙarshe sai lumshe idanunta tayi tana sauraron saƙonnin da yake aika mata
Sai da ya ga ta dena motsi kafin ya cire bakin sa yana mayar da numfashi. Sai ya saka hannun sa yana shafa mata kyakykyawar fuskar ta cike da wani irin salo tare da kiran sunan ta
A hankali ta buɗe idanunta ta zuba mishi rinannun idanuwan ta da suke buɗe wa daƙyar suna rufe wa, dishi-dishi take kallon sa sakamakon ƙwayoyin da ya bata sun soma mata aiki, gaba ɗaya babu ƙarfi a jikin ta tamkar an zare mata laka haka take jin ta, shiyasa har ya soma bata abincin ta kasa hana sa illa kallon sa da take faman yi lokaci zuwa lokaci hawaye na sauka daga fuskar ta
Sai da ya tabbatar ta ci abincin sosai kafin ya tashi ya bar ta wajen. Mota ya ɗauka ya fita a gidan. Like two hours sai ga shi ya dawo tare da wasu Mutane su huɗu, ɗaya ne kaɗai Dattijo while sauran samari, har da waɗanda ya bai wa aikin ɗauko MEEMA tare da biyan su maƙudan kuɗi. Shiga parlour’n suka yi suka zauna
Shi kuma ya wuce ɗakin ya fito da MEEMA wacce ke kwance bata san inda kanta yake ba sakamakon ƙwayoyin da ya bata sun rigada sun bugar da ita, ko ɗaga yatsan ta ba ta iya yi sai yanda yayi da ita. A ƙasa ya zaunar da ita sannan ya zauna shima tare da jingina ta a jikin sa, kana ya kalli tsohon nan yace, “Malam wannan ita ce yarinyar, kamar yanda nayi maka bayani ƙanwata ce, da mahaifi na da mahaifin ta ƴan uwa ne, iyayen mu sun mutu sun bar min ita a rashin lafiya, to kuma muna zaune a haka shiyasa naga ya dace in aure ta, ba na son wani abu yazo ya shiga tsakanin mu ba tare da aure ba, ina son ta a zuciyata shiyasa zan aure ta.”
Dattijon da ke kallon fuskar MEEMA wanda idanun ta suna rufe ruff, gaba ɗaya bata san ma me ake yi ba tunda ba ta cikin hayyacin ta. Cewa yayi, “babu damuwa yaro ai abinda kayi shi ne dai-dai, tunda gamu ka zo damu zamu zame maka shaidu domin mallakar ta, yanzu zan ɗaura muku aure tare ita kuma Allah ya bata lafiya me amfani.”
“Amin Malam.” Yafaɗa cike da nuna damuwa a kan fuskar sa
Malamin yace, “yanzu sai ka kawo sadakin aure Ni zan zame mata waliyi kai kuma ka zama wakilin kanka, waɗannan kuma sai su zame mana shaidu.”
Sajjad yace, “to Malam.” Sannan ya laluba aljihun sa ya ciro kuɗi dubu ɗari cas ya miƙa masa
Daga nan Malam ya ɗaura musu Aure sannan yayi musu addu’ar zaman lafiya
Cike da farin ciki Sajjad ya ɗauki kuɗi ya basu tare da godiya sannan suka bar gidan. Shi kuma tsaban murna kamar ya zuba ruwa a ƙasa ya sha, yau ga shi ya mallaki muradin ransa ya san wata rana dole zata so shi tunda babu wanda ya isa ya raba shi da ita, zai ci gaba da ɓoye ta har sai ya dasa mata ƙaunar shi a rai ta amince da shi sannan sai ya bayyana ta, daga nan ko me zai faru sai dai ya faru. Kai tsaye kichen ya nufa ya dafa ruwan zafi ya kai bayi, sannan ya dawo wajen ta ya hau tuɓe mata kaya don yin mata wanka. Yau ya san burin sa zai cika na kasancewa Ango a wajen masoyiyar sa, gaba ɗaya murna farin ciki ya tabaibaye shi coz ga shi ga MEEMAN shi babu me mishi shamaki da ita, ta zama mallakin sa daga yau sai yanda yayi da ita.