MEEMA FAROUK Page 51 to 60

Da gudu ta fita
Yusra tana take mata baya da ƙorafin, “ita zata je kiran ta.”
Duk kiran da yayi mata don, “ta dawo.”
But tuni ta fice ta bi bayan Hafsan.
Yana nan zaune a kan dainning ɗin koda ya gama cin abincin, sai ga su sun dawo tare suna sanar mishi, “Momy tace bata dawo ba.”
“Ok ku je ku zauna kuyi karatun Alkur’ani inda aka ƙara muku before Malamin ku ya zo.”
“To Dady.” Suka faɗa suna tashi da gudu suka soma rige-rigen shige wa ɗakin su
Shi kuma tashi yayi ya bar wayan sa a wajen ya haura sama. Sauya kaya yayi zuwa farar shadda me tsananin maiƙo da ɗaukar ido, tamkar ango haka kayan suka yi mugun fito da shi, har ƙara gyara gashin sajen sa dana kanshi yayi, ya sake liliye su da mayuka masu saka sheƙi da ƙamshi, sannan ya ƙwama hulan sa tangaran me kalan aikin kayan. Ya ɗauki keeys ɗin mota ya fice. A parlour’n ya zauna inda su Yusra suke karatu yana faman sauraron su, idan da gyara kuma sai ya gyara musu
Haka har malamin su ya zo wanda ya ke musu karatun islamiyya, ɗaya security ya zo ya sanar mishi
Don haka yace, “su shiga ɗaki su saka hijabin su su wuce wajen karatun.”
Tashi suka yi suka ɗauko suka zura suka fice
Shi kuma yana zaune har yanzu ɗin, sai dai yanzu ya mayar da idanun sa a kan fantsamemen t.v plasman da ke jikin bangon parlour’n yana kallo.
Luwaira ce ta shigo parlour’n da sallama
Hakan yasa ya bi ta da kallo yana amsa mata sallaman nata a hankali
“Yaya gani, Momy tace kana kira na?” Tayi maganar itama idanun ta a kanshi. Yanda ya ƙure ta da kallo ne yasa ta sauke kai ƙasa domin baza ta iya juran kallon ƙwayar idanun sa ba, sosai take jin faɗuwar gaba da shiga wani mawuyacin hali da haɗa idanu da shi
“Ki zauna.” Ya bata umarni ba tare da ya ɗauke kai har yanzu daga ƙare wa jikin ta kallo ba, tun daga sama kuwa har ƙasa, domin haka kawai ya ji yana buƙatar yau ɗaya ya kalle ta sosai
Sai da ta ɗago ta kalle shi suka sake haɗa ido, sai tayi maza ta ɗauke kai tana zama a kan sofan da ke kallon nashi, kamar wata salaha ta wani tattare waje ɗaya hannayen ta a haɗe wuri ɗaya
Wayan sa da ke saman dainning ne ta soma ƙara. Sai ya bata umarnin, “ta ɗauko mishi.”
Hakan yasa ta tashi da sauri ta nufi wajen
Shi kuma sai ya samu damar ci gaba da kallon ta, sai da ya ga zata juyo sannan ne ya ɗauke kansa yana wani lumshe idanu tare da buɗe su ya sake mayar wa a kanta. Wayan ta miƙa masa ya kai hannu ya amsa
Sannan ta je ta koma ta zauna
Hashim ne ya kira shiyasa yayi peacking suka yi magana kaɗan kafin ya kashe kiran ya ajiye wayan. Ya mayar da hankalin sa gare ta yana faman kallon ta, sai da ya ja ɗan soconni be iya cewa komi ba kafin ya cije leɓe yana ɗan lashe na ƙasan, before ya Kira sunan ta a hankali a cikin sanyin muryan sa wanda a koda yaushe haka take
Ita kuwa amsa mishi tayi tana sake jin gaban ta na matsanancin faɗuwa domin tabbas ta san zancen text ɗin ta ne yasa ya kira ta, ba ta raba ɗayan biyu
“Luwaira Did you really send me text today and that day? Do you want to send your message to me?”
Kai ta gyaɗa mishi kanta a ƙasa tana sake duƙar dashi
“Magana zaki yi min ba ɗaga kai ba”.
A hankali ta furta, “Eh.”
Shiru ne ya biyo bayan amsar ta. Ya kasa yin magana sai da ya ɗau lokaci me tsawo wanda ita har ta sare da jin maganar nasa, yayinda ta sake shiga tashin hankali da jin me zai faɗa mata. Numfashi ya ja yana tsayar da idanun sa a kanta kana ya buɗe baki a cikin sanyi da daɗin muryan sa yace, “kiyi haƙuri Luwaira duk da na san ba ƙaramin ƙoƙari kika yi ba wajen bayyana min abin da ke ranki, sai dai kuma Ni na ɗauke ki tamkar ƙanwata wacce muka fito ciki ɗaya da ita, kinga kuwa babu zancen maganar aure a tsakanin mu, ba wai don ba na son ki ko wani abun ba, a’a, look at my words and understand, Ina da wacce a halin yanzu nake neman auren ta, so don’t think of anything in your heart ok?”
Shiru ne ya biyo bayan zancen nasa domin ta kasa ko motsi, nan da nan hawaye suka cika mata idanu wanda har wasu tsiraru sun soma ɗigowa, hakan yasa ta sake duƙar da kanta sosai
Shi kuma jin tayi shiru sai ya kirayi sunan ta
But ta kasa amsa wa, sabida tabbas idan ta buɗe baki kukan ne zai taho gadan-gadan
“Ke ƙanwata ce Luwaira, kuma ba na son ki saka damuwa a ranki, ba naƙi amince wa da ke bane a kan wani abu ba tunda kin kai ko wanne ɗa namiji ya so ki, But you heard my argument, Ina so ki bar zancen nan a tsakanin mu domin ba na so Momy ta ji, You promise?”
Kanta ta gyaɗa tana kai hannun ta ɗaya ta goge hawayen fuskar ta
Shima ya fahimci kuka take yi, sai dai be da yanda zai yi, gwara yayi mata magana tun yanzu ta san makomar ta tunda ba ya son ya cutar da ita, bazai iya auren ta ba, yanzu zuciyar sa Mutum ɗaya kacal take so, da ita take son ƙare rayuwar ta, idan har ya shigo da Luwaira a cikin rayuwar sa ƙwaran ta kawai zai yi domin be taɓa son ta ba, kuma ba ya jin zai taɓa. Umarni ya bata a kan, “ta tashi ta tafi.”
Don haka ta miƙe da sauri ta juya ta tafi
Kallon ta kawai yake yi har ta fice a parlour’n. Sai ya kwantar da kansa a jikin kujeran yana lumshe idanuwan sa zuciyar sa cike da tausayin ta, domin shi Mutum ne me tsananin tausayi, yana da rauni matuƙa musamman ma a kan Mace. ya jima a haka ko motsi ba ya yi sai yatsun hannayen sa da yake ƙas-ƙas da su. Almost five minutes ago before ya buɗe idanun nasa yana miƙe wa ya ɗauki wayan sa ya zura a aljihu, sannan ya nufi ƙofa ya fice.
????????????
*MEEMA FAROUK*
????????????
*NA_NAFISA ISMA’IL*
*WATTPAD_UMMUDAHIRAH*
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT*????????
*PERFECT WRITER’S ASSOCIATION* ????
“`( WE AIN’T PERFECT, BUT WE’RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS????)“`
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._
*SHAR’ANTATTUN SALLOLI*
“`A dukan mazhabobi sallolin da aka shar’anta sun kasu kashi biyu ne, farilla da nafila. Amma shi kuwa Abu Hanifa ya ce uku ne: farilla, wajiba da nafila. Ita farilla ɗin ta kasu biyu.
_1. Farlu aini._ Wannan ita ce sallar da take kama baligi kansa, ba wani da zai iya ɗauke masa yinta, kamar dai su sallolin nan biyar da sallar juma’a.
_2. Farlu kifaya._ Ita ce sallar da take kama baligi, amma idan wani ɓangare na mutane suka yi ta, ta faɗi ga sauran jama’a, misali sallar jana’iza. Idan sashin mutane kuwa ba su yi ba, jama’a duk sun yi laifi.
A mazhabar Abu Hanifa wajibi kashi biyu ne:
_1. Wajibi don kansa-_ watau abin da wajabcin sa bai dogara akan wani abu daban ba, kamar sallar wuturi da sallar idi da sujadar tilawa.
_2. Wajibi don wani abu-_ wannan shi ne abin da wajabcin sa yake dogara ga wani abu daban, kamar sujadar rafkannuwa da raka’o’in ɗawafi da bakantacciyar sallah da ramakon sallah wadda ta ɓaci. Watau, sujadar rafkannuwa ba ta wajaba sai don rafkanar wani abu a cikin sallah. Su kuma raka’o’in ɗawafi ba sa wajaba sai don ɗawafi, bakantacciyar sallah ma ta wajaba ne saboda bakance. Ita nafila kuwa ramakon ta bai zama farilla ba sai da ɓacin tun farko.