MEEMA FAROUK 1-END

MEEMA FAROUK Page 51 to 60

     A mazhabobin maliki da shafi’i da Hambali nafila ita ce duk abin da yake ba farilla ba. Watau, abubuwan da Hanifawa suke ɗauka wajibi ne don kansu, a wurin sauran mazhabobi suna cikin sunna ko mustahabbi sabida cewa wajabcin ba don zatin su ba ne, illa dai sabuban da aka ambata.

     Ita nafila ɗin an kasa ta gida biyu:

_1. Nafila mu’akkada,_ watau wadda aka ƙarfafa sunnancin ta, kamar su sallolin idi da wuturi da raka’o’in ɗawafi, waɗanda Hanafawa suke kira wajibi.

_2. Nafila wadda ba mu’akkada ba,_ watau wadda ba a ƙarfafa sunnancin ta ba, kamar su nafilolin da ake yi gabanin azahar ko bayanta, da waɗanda ake yi gabanin la’asar da bayan magriba da kuma gabanin isha’i da bayan ta.

        Allah yasa mu dace.“`

                       *NO_34*

             Babu ranar da ya kai wannan lokacin a wajen Sajjad domin mallakar abar ƙaunar sa, wanda yana jin ya fi kowa farin ciki a duniyar nan tamu, tsantsan ƙaunar da yake yiwa MEEMA shi ya jawo duk abin da yake mata a halin yanzu, izuwa yanzu ya mallake ta a matsayin Matar sa kuma ya zamar da ita cikakkiyar Matar sa. Kasancewar ba ya son ta riƙa mishi gardama a zamantakewar su shiyasa har yanzu ya ci gaba da ɗura mata ƙwayoyi wanda ke gusar mata da hankali

A sannu a sannu sai ta koma tamkar mara hankali domin ba ta sanin ma a halin da take ciki. Shiyasa yake kiɗan sa yake rawan sa da ita duk yanda ya juya ta haka take bin shi

Yanzu ba shi da wani matsala bare shamaki da ke hana sa kusantar abar ƙaunar sa. Shi ke mata komi na rayuwa, ya cika gidan da kaya yanzu komi na more rayuwa ya zuba. A nan yake kwana yake wuni sai idan yayi kwana biyu ne sai ya koma can Yola gudun kar iyayen sa su zargi wani abun. A yanzu ya yanke shawarar da zaran zai tafi abroad karatun sa zai tarkata har da ita ne ya tafi, tunda dama yana neman karatu a UK.

              Haka rayuwar ta ci gaba inda a yanzu ga shi har MEEMA ta shafe wata ɗaya a hannun Sajjad. Kuma har a lokacin yana ci gaba da banka mata magunguna ba tare da yayi la’akari da hakan zai cutar da ita ba, domin shi ya fi son ganin ta a haka su zauna lafiya babu wani gardama da zata yi masa, muddin tana a cikin hankalin ta ya san zai sha fama da ita, ƙarshe bazai taɓa jin daɗin rayuwar sa ba. A sannu a sannu sai ga shi ta soma ciwo wanda lokaci ɗaya ta fita hayyacin ta ta rame sosai. Hakan yasa dole ya ɗauko Likita tunda ya ga jikin nata ya ƙi daɗi

Likitan bayan ya duba ta shi yayi masa bayani a kan, “ya dena bata ƙwayoyin da yake bata saboda sun soma mata illa a ƙwaƙwalwa, idan har hakan ya ci gaba da faruwa zai iya rasa ta sabida a halin yanzu magungunan sun fi ƙarfin ta.” Kasancewar shi Likitan dama shi yake ba shi maganin da yake ɗura mata wanda zai riƙa gusar mata da hankali ya zamana ba ta iya taɓuka komi sai yanda aka yi da ita, kuma tunanin ta zai riƙa gushe wa a jikin ta 

Shi kuma Sajjad bayan ya bata ne sai ya ci gaba da bata don kawai ta ci gaba da zama a haka

Likitan ya sake mishi bayani a kan, “tana da shigan ciki.”

Koda jin haka sai hankalin sa ya tashi domin shi be shirya haihuwa yanzu ba, yana son sai ya gama more rayuwar sa inyaso daga baya sai su soma tara yara, shiyasa yace mishi, “a zubar da cikin.”

A nan take kuwa yayi mata allura aka zubar

Sai dai ta sha wahala matuƙa tunda har suma tayi kasancewar ta zubar da jini

Haka likitan ya ƙara mata ledan ruwa sannan ya tafi

Shi kuma Sajjad zuwa yayi ya zauna a gaban gadon da take kwance ya zuba mata idanu har da yin tagumi

Tana kwance ne idanuwan ta a rufe ruf, fuskar nan nata ta ƙara zama ɗan siriri tayi fayau tamkar mara jini a jiki. Daga ita sai shimi fara wacce ya sanya mata, sai ya rufa mata blanket a jikinta

Hannun ta ɗaya mara drip ɗin ya riƙe, kana kuma ya duƙa ya sumbaci hannun yana shafa mata saman goshi har izuwa gashin kanta. Cike da shauƙin ƙaunar ta yake kallon ta da cewa, “very soon zaki samu lafiya my dear, I love you so much! Ina yin komai ne domin Ƙaunar ki kar ki ga laifi na.” Ya sake faɗa yana kai bakin sa kan nata ya sumbata, har ya cire kuma sai ya sake mayar wa yana saka bakin nasa a cikin nata ya ci gaba da tsotso na tsawon lokaci kafin kuma ya tashi ya fice zuwa kichen. Daga shi sai gajeren wando a jikin sa ya shiga ya ɗaura girki, taliyan makoronni ya girka sannan ya sako rabi a flet, sai da ya koma ɗakin ya ga har yanzu tana barci kafin ya wuce Parlour ya zauna ya soma cin na flet ɗin, yana yi yana kallo a t.v cike da nishaɗi da walwala a face ɗin sa.

✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️

       Bazan iya misalta muku a halin da mutanen gidan su MEEMA suka kasance ba a cikin wannan watan. Tun suna saka tsammanin za’a ganta ga shi yanzu har sun gajiya sun soma cire rai da ganin ta, abun ya sake ɗaga musu hankali musamman yanda suka ji shiru wanda hakan ya sa suka cire tsammanin kidnappers ne suka ɗauke ta, tunda da su ne da tuni sun kira sun buƙaci kuɗi

Babu irin fafutukar da Uncle Hashim be Yi ba don ganin an samu MEEMA, sai dai abun ya cutura. Izuwa yanzu dole yayi haraman koma wa Abuja tunda hutun da aka ba shi a wajen aiki ya ƙare, dama wata ɗaya suka ba shi lokaci har yayi yana neman gotawa, babu yanda ya iya haka ya shirya kayan sa ya wuce Abuja tare da danƙa komi na binciken a hannun Umar Faruk tunda komai tare suke yi

Shi kansa shima yana cikin halin damuwa da tashin hankali da rashin MEEMA, tunda soyayyarta ta matuƙar kama mishi zuciya wanda a yanzu ta hana sa sukuni matuƙa. Tafiyar Uncle Hashim ne ya kwanta ciwo sabida yanda yake saka damuwa a ranshi ga shi yana fama da ciwon zuciya. Dole aka wuce da shi asibiti yayi jinya na ɗan kwanaki

Likitan shi ya yiwa Momy bayanin halin da yake ciki

Shiyasa koda suka koma gida ta tsare shi da tambayar abun da ke damun sa?

Ya ƙi sanar mata da halin da yake ciki sai da ya ga ta nuna damuwarta ƙwarai kafin ya sanar mata da damuwar sa

Cike da tausayin sa a fuska tace, “My son don Allah ka cire damuwa a ranka, yarinyar nan fa idan rabon ka ce zaka same ta, Allah zai bayyana ta a duk inda take, amma kuma be kamata ace kana saka damuwa har ya kwantar da kai ciwo ba.” Sai tayi shiru tana jan numfashi, sake kallon sa tayi da cewa, “Ni bazan zauna in zura maka idanu kana cutuwa a haka ba, idan da ace kana da Mata da duk hakan be faru ba, da tuni ita zata riƙa kula da kai sosai yanda ya kamata, ka ga kuwa dole ne kayi aure yanzu, bamu san lokacin da za’a ga yarinyar nan ba, Ni ina ga a shawarata idan har zaka iya bin abun da nace maka ka auri Luwaira, ka ga ita ƴar uwan ka ce zaku zauna lafiya, ina matuƙar tausayin ka shiyasa ban son ganin ka a cikin damuwa.”

Shiru ne ya biyo bayan zancen nata domin ya kasa yin magana, maganar sosai ta buge sa shiyasa ya kasa ɗago kai bare ya bata amsa

Sai ta kira sunan sa da cewa, “Umar na san ko ba Luwaira ba dole zaka sake aure, amma idan ka tsaya jiran yarinyar nan baka san sanda zata dawo ba, sannan mutanen gari suna yamaɗiɗi da kai a kan rashin ajiye mata hakan ke jawo ka-ce-na-ce a tsakani na da ƙawaye na idan na fita waje, to yanda ake yawan maganar ne ba na jin dadi, Ni kai na zan fi so ace ka aje mata ko don lafiyar ka shiyasa na zaɓa maka ƙanwar ka, wacce ta san ka ta san halayyar ka, haka zalika kai ma haka. Idan baka amince ba babu komi wlh ka faɗa min ra’ayin ka.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button