MEEMA FAROUK Page 51 to 60

“Haba Momy ta ya ya zan ƙi ƙaunar ƴar ki? Bazan iya bijire miki ba domin tamkar umarni nake ganin zancen naki. Allah ya zaɓa mana abin da ya fi zama alkhairi.” Yafaɗa a cikin matsanancin sanyin murya
Murmushi ne ya suɓuce a fuskar Momy da cewa, “kana nufin ka amince?”
“Eh Mom.”
“Masha Allah. Haƙiƙa zan fi kowa farin ciki da wannan haɗin, Allah yayi maka albarka ya sanya albarka a auren naku. Alhamdulillah.” Ta faɗa a cikin farin ciki
Shi kuwa be iya cewa komi ba har ya bar parlour’n. Sosai ya shiga damuwa sai dai ba shi da yanda zai yi, bazai iya duban idanun Momy ya ƙi amince wa da buƙatar ta ba, Momy tayi mishi komi bazai taɓa bijire mata abun da ta saka shi ba, amma ya zai yi da zuciyar sa da ta mutu a ƙaunar wata? Ko kaɗan ba ya ƙaunar Luwaira, to sai dai kuma akwai tausayin ta a zuciya zai iya yin haƙuri da ita ya zauna da ita, sai dai kuma bazai taɓa haƙura da MEEMA ba. “Allah ya baiyana min ke My love, nayi kewar ki sosai!”. Ya furta a laɓɓan sa yana me mayar da idanun sa ya rufe ruf.
Daga ranan ne aka soma shirye-shiryen auren su tunda har an tsayar da ranan aure
Murna wajen Luwaira kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha tunda Momy ta sanar mata da zancen. Ta kasa yarda da gaske zata auri Umar Faruk. Har kuka sai da tayi tsaban farin ciki
Shi kuwa Umar Faruk baza ka taɓa gane a halin da yake ciki ba a kan zancen auren, ko kaɗan ba ya nuna abun da ke ransa a fili. Uncle Hashim ne kawai yake kwantar masa da hankali tunda ya sanar mishi da komi
Shima ya ga dacewar auren nasa tunda bazai zauna haka be da mata ba, bare shi ɗan siyasa za’a yi ta yamaɗiɗi da shi ne, sai dai kuma ya jiwa MEEMA haushi a kan rasa masoyi kamar Umar Faruk, ya so burin sa ya cika a kan ta auri abokin sa domin ba ƙaramin dacewa suka yi da juna ba. Sai dai basu da tabbacin sanda za’a ganta, basu san a wani hali take ba a halin yanzu? Basu san tana raye ne ko tana mace ba? Sai dai addu’a da ƙarfafa wa kansu haƙurin rashin ta da suke faman yi a halin yanzu. Insha Allahu Allah zai bayyana ta tunda sun tashi tsaye sosai wajen addu’o’i da saukar alƙur’ani
Ba dare ba rana ake sauke Al’ƙur’ani don dai aga inda take. Tuni walwala da farin ciki ya ƙwaurace wa su Ummee a halin yanzu. Burin su kawai su ga MEEMA ta dawo gida. Ɓacewar ɗan Mutum sulluguda? Abun ɗaga hankali ne.
**** ***** ***** **
Wata ɗaya aka saka bikin shiyasa aka tasar wa gyaran gidan su gadan-gadan, kama tun daga Part ɗin Umar Faruk har izuwa part ɗin Momy, gaba ɗaya gidan sai da aka sauya mishi sabon penti. Gyara sosai ake yi a gidan ana kashe mishi maƙudan kuɗi
Umar Faruk shi ya ɗau ragamar komi na bikin, har kayan da za’a zuba wa Luwaira, a ƙasan Dubai aka yo odan komi, tunda shi Yakamata yayi mata komi na biki a matsayin sa na Yaya a wajen ta, bare kuma yanzu shi zata aura.
Yau da gobe kayan Allah sai ga biki ya ƙarato inda har an soma shagulgulan biki, yanda aka tsara bikin ana yin shi cikin girma da arziƙi sosai hakan ya faranta ran Luwaira, dama haka take so ta ga bikin ta na kere wa Sa’a wanda za’a riƙa faɗan shi a ko ina. Ita kanta ta san yanzu ta zama big classes Girl domin har a makaranta zuwa ake yi ana ganin ta, musamman ƴan mata wadanda suka ci burin auren Umar Faruk, da waɗanda suka san shi a zahiri da waɗanda suke jin labarin shi
Ba irin gyaran Amaren da Luwaira bata yi ba, musamman suka ɗauko me gyara ita da Abida ake mata a gida. Kasancewar ta kyakykyawa itama son kowa ƙin wanda ya rasa shiyasa ta fito a Amaryan ta sosai, sai shainnig take yi gunun sha’awa
Sun shirya events kala-kala ita da ƙawayen ta. Shiyasa tunda aka shiga satin bikin aka soma yin event ɗin
Babu wanda Umar Faruk ya halarta domin shi har yanzu be wani damu da auren ba, kuma har yanzu be taɓa neman Luwairan ba, sai ma da bikin ya zo ne ya kira ta ya ba ta ATM card ɗin shi yace, “Ta je ta dauki kuɗin da take buƙata, idan ta gama hidiman bikin ta kawo mishi.”
Ita ko a jikin ta wai don be damu da ita ba, tunda Abida tana kwantar mata da hankali a cewar ta, “idan suka yi aure zai zamo nata ita kaɗai, a nan ne zata mayar da hankali ta sace zuciyar sa sai yanda tayi da shi.” Shiyasa bata damu ba don ba ya nuna kulawan sa a kanta.
Yau ma party suka shirya a haraban gidan ita da ƙawayen ta. Ƙawayen ta sun yi ankon doguwar riga Robber brown color, sai aka yi design da zare kalan coffee aka ɗaura flower a gefen kafaɗan rigan na hagu, gaba ɗayan su ƙawayen nata ɗinkin iri ɗaya ne har Abida, sai suka yi amfani da farin ɗankwali aka yi musu ɗauri me Steps
Itama kuma Luwairan doguwar riga ce ta ɗinka, sai dai nata Golden corral ne, daga bayan yana jan ƙasa sosai yayinda gaban rigan aka ɗigile shi da designing ɗin love aka yanka gaban rigan, ita Stones aka yi mata amfani da shi wajen kwalliyan rigan a gaban; masu tsananin ƙyalƙyali da ɗaukar idanu, sai tayi amfani da ashobe ja aka yi mata ɗauri me kyau irin na Amare, fuskar nan ta sha make-up na zamani wanda ke sauya halitta, don ko ka san ta baza ka gane ta ba a ranan sabida yanda ta koma, tayi amfani da dogayen takalma masu tsinin gaske don daƙyar take iya tafiya tamkar zata faɗi.
Sun gabatar da taron su gunun sha’awa sun kuma cashe irin na wayayyun ƴan mata, kasancewar da yamma aka yi har sai da aka kira magriba kafin suka tashi.
Zuwa gobe kuma shi ne zasu yi dinner Wanda shi Abokan Umar Faruk ne suka shirya masa, gaba ɗayan su zasu halarci wajen, zuwa jibi kuma sai a ɗaura Aure akai Amarya ɗakin ta.
_To Fans na Luwaira muna gayyatar ku shagali fa, an soma ya kamata ku hallaro, saura ku ce baza ku zo ba._ ????????
????????????
*MEEMA FAROUK*
????????????
*NA_NAFISA ISMA’IL*
*WATTPAD_UMMUDAHIRAH*
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT*????????
*PERFECT WRITER’S ASSOCIATION* ????
“`( WE AIN’T PERFECT, BUT WE’RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS????)“`
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._
*NO_35*
Da sannu-sannu MEEMA ta soma samun lafiya. Zuwa yanzu ta soma dawowa a cikin hankalin ta kasancewar Sajjad ya dena bata maganin sosai, sai yayi kwanaki ma be bata ba saboda shi be so ta riƙa mishi gardama. A kullum sai tayi kuka sabida baƙin cikin halin da ta tsinci kanta, ji take yi kamar ta kashe kanta sai dai bata da ƙarfin ƙwatan kanta, a haka ta zura wa Sajjad idanu yana yin duk abin da ya ga dama da ita, sai dai tana iya bakin ƙoƙarin ta wajen hana shi but ya fi ta ƙarfi haka tana ji tana gani take ƙyale shi
Shi kuwa ce mata yayi, “she calmed down because she became his wife saying, no one should take her from his hand and be his property.”
Ta kan yi kuka sosai ta share hawayen ta ta zira masa idanun ta kamar yanda ya zame mata jiki tunda babu abinda take iya yi. Sai dai tunda ta soma samun lafiya take ta yunƙurin guduwa amma Allah be bata Sa’a ba tunda ba ya wasa da barin ƙofa.
Kamar ko yaushe yau ma tana zaune a ɗakin da ya zame mata nata, ta haɗa kai da gwiwa tana ta sharɓan kuka, ƙunci da baƙin ciki ya addabi rayuwar ta, tana jin baza ta iya ci gaba da rayuwa a haka ba gwara ta kashe kanta, shiyasa kawai ta tashi da hanzari ta fita Parlour, dube-dube ta soma Yi sai kuma ta zarce kichen, a nan idon ta suka faɗa kan wuƙa sai ta nufi wuƙan da sauri ta ɗauka, ta saita da ninyan lumawa kanta har ta kai cikin nata sai kuma ta tsayar da wuƙan tana me fashe wa da wani irin kuka me ban tausayi, yayinda ta faɗi a kan gwiwowin ta ta dinga rerawa kamar ana yankan naman jikin ta. Kuka take yi sosai wanda ta shafe tsawon lokaci a wajen. Sai da ta jiyo ƙarar motan Sajjad wanda ya dawo daga yawon sa; hakan yasa da sauri jikin ta na rawa ta miƙe, sai ta wawura wuƙan ta ɓoye a Bayan ta ta nufi ɗakin da gudu, pilow ta ɗaga ta ɓoye wuƙan sannan ta hau kan gadon ta zauna, sai ta mayar da kanta a saman cinyanta ta ci gaba da kuka