MEEMA FAROUK 1-END

MEEMA FAROUK Page 51 to 60

Shi kuma yana shigowa kanshi tsaye ɗakin ya shigo, yana sanye da ƙananan kaya ya saka ear phone a kunnen sa, sai takawa yake yi sakamakon waƙar da yake sha yana juyi, dayake waƙar soyayya ce shiyasa yake a cikin farin ciki ya nufe ta fuskar sa cike da walwala. Hannu ya kai ya taɓa mata kai yana kiran sunan ta, “my Baby I’m back.” Sai ya saka hannu ya ɗaga kanta saboda ganin ta ƙi motsa wa. Zaro idanun sa yayi ganin yanda fuskar ta tayi jazur da cikin idanun ta sakamakon kukan da ta sha. “common Baby what’s wrong with you?Why do you worry? I am your husband. Stop worrying about me you are already mine. No one is enough to separate you from me.” Sai ya shafo fuskar ta yana sakin murmushi

Ita kuwa ta kasa yin motsi illa tsayawa da tayi tana kallon sa hawaye na ambaliya a fuskar ta, lokaci ɗaya kawai zuciyar ta ta bata mummunan shawara wanda take jin gwara ta kashe shi ta huta. Shiyasa lokaci ɗaya be yi zato ba domin har ya shige jikin ta ganin ko motsi ta ƙi yi yana ta faman shinshinan ta; sai ta zaro wuƙan ta tura shi da ƙarfinta ta luma mishi a ciki. Kafin kace me ta sake zaro wa ta sake luma masa

Tuni ya saki ƙara ya faɗa saman gadon yana ƙoƙarin riƙe hannun ta, sai dai yanda ta zare wuƙan ta sake luma mishi ne yasa shi sakin wani bahagon ihu me kama dana kenwa, lokaci ɗaya jini ya soma ambaliya a jikin sa har ta cikin bakinsa aman jini yake yi, yayinda numfashin sa ya ɗauke gaba ɗaya

Ruɗewan da MEEMA tayi ne yasa ta kasa guduwa, hannun ta na kan wuƙan daƙyar ta saki, sosai hankalin ta ya tashi wanda lokaci ɗaya tabi ƙofa da gudu har tana cin tuntuɓe, kuka ta saka sanda ta isa bakin ƙofan ta jijjiga taga a rufe yake. Tsaban ruɗe wa ta gaza inda zata je domin tunanin ta ya gushe ta manta inda zata samu mukullin, sai da ta gama wuri-wuri a wajen sannan ta koma ɗakin inda Sajjad yake a kwance a mace ta laluba aljihun wandon sa jikin ta na rawa kamar ace ket da gudu. Tana cin karo da keey ɗin ta ɗauka ta fita aguje, tunda ta buɗe ƙofan ta zura aguje bata tsaya ba. Cin gudu kawai take yi kamar sabuwar mahaukaciya domin kanta ko ɗankwali babu, daga ita sai doguwar riga ƴar kanti wanda da kaɗan ya wuce gwiwan ta. Gudu take yi sosai har ta fito cikin jama’a ta tasar wa titi, babu tsammani ta yanki titi sai ga ta a yashe wani me moto yayi ƙwallo da ita sakamakon hawa kan titin da tayi ba tare da ta duba ba

Nan da nan Mutane suka yo wajen ana zuba salati

Mutumin da ya bige ta shima tuni ya fito yana salati

Tsaban tsorata ne yasa ta sume gau, sai kuma ƙafan ta da a yanzu ɗin suka ga yana zubar da jini

Shiyasa nan da nan jama’ar wajen suka soma bata taimakon gaggawa, wasu har sun soma mata fifita, wasu na faɗin, “a kawo ruwa.”

Mutumin da ya buge ta yace, “a taimaka a saka mishi ita a mota sai akai ta asibiti tunda akwai asibitin a kusa.”

Nan kuwa ɗaya ya ɗaga ta aka saka ta a mota. Sannan ya shiga ya ja ya nufi asibitin da ita.

            A asibitin an bata taimakon gaggawa kuma ta farfaɗo, sai dai babu abinda ya same ta illa buguwa da tayi a ƙafa sosai, wanda har targaɗe ta samu ga kuma ciwo, an mata treating wajen. Tunda ta farka ɗin take kuka

Shiyasa mutumin yayi ta rarrashin ta but ta ƙi shiru. Shiyasa ya ƙyale ta ya fita ya kira likita

Shima da yazo ya tambaye ta, “ko akwai abin da ke damun ta ne bayan ƙafar?”

But ta ƙi magana sai rera kuka take yi. Sai daƙyar suka samu tayi magana, ce musu tayi, “She will go home, they will take her home and she will not stay.”

Duk yanda Likitan ya so ya rarrashe ta domin ta zauna ko zuwa anjima ne sai a sallame ta but ta ƙi

Dole mutumin yace, “a basu sallama.” Sannan ya je ya biya Bill ɗin yace mata, “ta tashi su je.”

Sai dai ta kasa tafiya dole aka kira wata Nurse ta taimaka ta riƙe ta zuwa wajen motan Mutumin

Shi ya tambaye ta address ɗin ta sannan ya wuce da ita kai tsaye gidan Hajiya.

✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️

        Ƙarfe huɗu aka soma shirye-shiryen tafiya Dinner 

A wannan karon ƙawayen amarya sun sha ankon jan atamfa ce wanda aka yi silƙi da fari da me ruwan toka, sai suka yi amfani da farin ɗan kwali. Yayinda Abokan Ango duk suka sha fararen shadda

A mota ɗaya aka ɗauki Ango da Amarya zuwa hall ɗin da za ayi taron. Tunda suka shiga babu me yin motsin kirki

Shi Umar Faruk ya kwantar da kansa a jikin kujeran ne while idanun sa a rufe ruf. Yana sanye da farar gezna uban-uban su me tsananin tsada. Riga da wando ne da malin-malin ɗin sa, sai yayi amfani da hula kalan aikin rigan, yayinda agogon hannun sa da takalman sa suka kasance farare su ma

Haka itama Luwaira ta saka farar gown ne me dogon hannu, rigan tayi matuƙar kama ta tare da fito mata da kyakykyawar surar jikin ta, sai aka yi mata amfani da golden ashobe aka yi mata ɗaurin Amare, fuskar nan nata ya sha makeup wanda ko ka santa ma baza ka iya gane ta ba tsaban yanda kwalliyan yayi mata ɗau a face, yayinda hannayen ta suka sha zanen lalle ja da baƙi suka ɗau white skin ɗin ta. Itama kanta na sunkuye ne ta ƙame waje ɗaya ko motsi ba tayi

Motan gaba ɗaya ta gume da ƙamshin turaren su wanda ya sake bayar da wani irin sassanyan ƙamshi me saka nutsuwa a zuciya

Koda motan ta faka a haraban hall ɗin abokan ango ne suka zo suka buɗe musu. Su suka haɗa su waje ɗaya tare da saka shi ya riƙe hannun ta

Sai dai shi ya ƙi sabida gani yake yi ai bata zama matar sa ba tukunna, shiyasa koda suka matsa mishi sai yayi gaba ya bar su a wajen. Dole suka bi bayan sa suka tsayar da shi suka jera da Luwairan zuwa hall ɗin da ya cika maƙil da Mutane, yayinda music me sanyin daɗi ke tashi na tarban su

Kasancewar harkan na manyan Mutane ne babu inda be ƙayatar ba a wajen, musamman yanda suke gudanar da abubuwan nasu a cikin tsari

Amarya da Ango sun zauna a mazaunin su inda aka fara gudanar da shagulgula cikin girma da arziƙi

Bazan iya misalta muku farin cikin da Luwaira take ji a wannan lokacin ba, bakin ta ya ƙi rufuwa don daɗi. Abun da take buri da fata kenan ya zamana bikin ta ya zama babban biki da ko ina sai an sani, ga shi ta cika burin ta, ta auri muradin ranta sannan kuma tana ɗaya daga cikin Matan da suke da Sa’a a duniya

Umar Farouk baza ka taɓa gane a halin da yake ciki ba, duk da ba ya farin ciki a zuciyar sa but ko kaɗan baza ka ga hakan a fuskar sa ba, musamman kasancewar sa me kwarjini da kamala a fuska, ko be yi fara’a ba baza a taɓa gane hakan ba, yanzun ma fuskar sa sai shainnig take yi tana fizgar ƴan matan wajen wanda gani suke yi ba kowa ne me dacen samun santalelen kyakykyawa kamar shi ba, haƙiƙa ƙawar su tayi Sa’a babba.

             Taro ya soma yin nisa inda masu hotuna da bidiyo sai haska su suke yi

Daidai lokacin ne kuma wayan sa tayi ƙara. Ganin sunan Hashim shiyasaka ya ɗaga saboda dama ya san da tahowar sa a yau ɗin domin halartan bikin sa

Luwaira wacce ta ɗago kai ta zuba masa idanu tana kallon sa, sai dai ba ta jin abinda yake cewa kasancewar ya kare bakin sa tare da kawar da kansa gefe. Gani tayi kuma ya tashi zumbur kamar wanda aka tsikare shi ya sauka a wajen ya tasar wa ƙofa ya fice. Kasa ɗauke idanu tayi a kan ƙofan tana jiran ta ga dawowar sa, sai dai kuma har kusan mintuna goma suka wuce babu shi babu labarin shi, take a nan zuciyarta ta soma mata ƙunci wanda har ta soma tara ruwan hawaye a cikin idanun ta

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button