MEEMA FAROUK Page 51 to 60

Abida wacce ta kula da ita; ita ce ta taho wajen tana raɗa mata cewa, “ina Angon nata ya tafi ne? Ya kamata ace ya dawo.”
“Nima ban sani ba Abida, ban san inda ya je ba be faɗa min ba.”
“Ok bari in duba wajen, but ki ɗan saki fuskar ki sabida kinga yanda kika yi ne?” Daga nan ne ta fice domin duba shi, sai dai ko me kama dashi babu a wajen haraban, kuma babu motan da suka zo na Amarya da Ango
Dayake ita ya hau ya bar gidan ya wuce gidan Hajiya. Kasancewar kiran da Hashim ɗin yayi mishi ya masa albishir da dawowar MEEMA ce, wanda hakan yasa ya kasa jure wa ya fice domin zuwa ganin ta.
Abida koda ta dawo ta faɗa mata. “babu shi da alamun ya bar wajen ma.”
Sosai Luwaira ta shiga damuwa. Kuka ne kawai bata saki a wajen ba tsaban baƙin ciki, wannan wulaƙanci da me yayi kama? Ana taron ta but Ango ya tafi ya bar ta babu ko sallama?
Abida ita ke ta kwantar mata da hankali
Su kansu Abokan sa da suka ga ba ya wajen sun ta neman sa a waya but switch off. Dama ya san za a neme sa shiyasa ya kashe wayan
Haka aka tashi a taron ba tare da Ango ba wanda hakan ya soma jawo zance daga wajen ƙawayen Amarya, har ma da Mutanen wajen
Yayinda Luwaira ta sake shiga tashin hankali matuƙa. Suna koma wa gida ɗaki ta shige ta faɗa kan gado ta dinga rera kuka sosai
Abida wacce ta biyo bayan ta; ita ta kulle ɗakin kar ma wani ya zo ya tarar da ita a hakan, sannan ta zo ta zauna a gefen gadon ta dinga rarrashin ta
Sai dai Luwaira ta kasa yin shiru, daga ƙarshe ɗago kai tayi tana kallon Abidan yayinda idanun ta suka Kaɗa suka yi jazur hawayen ciki sun kasa tsayawa tace, “don Allah wannan abun da me yayi kama Abida? Kenan kowa sai ya tabbatar ba ya so na? Da ya san zai min wannan wulaƙancin ai da tun farko ba’a yi ba hakan zai fi min, baki ji yanda nake ji ba a zuciya ta! ina ne ya fi masa da zai je ya bar taron bikin sa? sai yanzu na soma dana-sani da auren nan, ban san kuma wane baƙin ciki ne zan tarar a gaba ba?”
Abida numfashi ta ja tare da dafa ta tace, “Ni don Allah ban ga wani abun tayar da hankali haka ba duk da be kyauta miki ba, amma kiyi masa uzuri mana ba fa ya ƙi zuwa taron bane gaba ɗaya, Ni na tabbata bazai miki haka domin ya wulaƙanta ki ba, akwai abun da ya sha mishi kai ne wanda ya aikata hakan…”
“Wanne abu ne ya sha mishi kai da har zai kasa sanar min ya tafi ya bar Ni? A bainar jama’a fa Abida.” Ta katse ta da faɗan hakan a cikin kuka
“Don Allah kiyi haƙuri mana tunda komi ya rigada ya faru, daga yau ne fa gobe kin zama tashi komi zai wuce, sai yanda kika yi dashi idan kika zama matar shi, ke ce zaki jawo hankalin sa gare ki, wannan dai ya rigada ya faru amma ki cire damuwa kar wani ya fahimci halin da kike ciki Please.” Da haka Abidan tayi ta rarrashin ta har ta samu ta kwantar mata da hankali.
????????????
*MEEMA FAROUK*
????????????
*NA_NAFISA ISMA’IL*
*WATTPAD_UMMUDAHIRAH*
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT*????????
*PERFECT WRITER’S ASSOCIATION* ????
“`( WE AIN’T PERFECT, BUT WE’RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS????)“`
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._
*NO_36*
Bazan iya misalta muku farin ciki da murnar da su Hajiya suke ciki ba sakamakon dawowar MEEMA
Ita MEEMA kuka sosai ta fashe da shi da tayi arba da su, musamman da ta ganta a jikin Ummee wacce ta rungume ta itama tana zubar da hawaye. Sake ƙanƙame Ummeen tayi tana ta kuka me tsuma ran me sauraro, ko kaɗan ta kasa sakin ta sabida dama tana matukar kewar jikin ta, rabon da ta ji ta a jikinta ta manta shiyasa yau ta kasa sakin ta
Sai da Uncle Hashim ya zo sannan ne ta basu labarin abun da ya faru, ta kuma sanar musu da Sajjad ne ya ɗauke ta
Babu wanda be yi kuka ba sabida tausayin ta.
Da ƴan sanda da Mutumin da ya taimaki MEEMA suka wuce anguwan da ya ɗauko ta kasancewar ita bata san gari ba. Bayan ya kai su wajen ne itama kuma ta nuna hanyar da ta biyo domin ta kai su gidan, daƙyar aka samu ta iya tuna inda ta biyo tunda a lokacin a rikice take
Sun shiga gidan sun tarar da Sajjad kamar yanda ta bar shi, ya zubar da jini sosai domin sun yi tunanin ya mutu, sai dai koda aka kai shi asibiti an tabbatar yana da rai
Uncle Hashim shi ya saka aka je har Yola aka kamo Kawu Ali a daren, domin yace, “duk da halin da Sajjad yake ciki bazai yarda ba sai an hukunta shi.” Kotu za’a kai shi kai tsaye
Shima Kawu Ali da ganin abun da ke faruwa da gudan ɗan shi hankalin sa a tashe ya dinga masifa, a cewar sa, “bazai yarda ba shima sai ya ɗau mataki.”
Rikici fa sosai ya kaure a tsakanin su
A lokacin an wuce da MEEMA asibiti don jikin ta ya rikice sosai
A can asibitin Umar Faruk ya je ya tarar da su. Tunda ya ji labarin abun da ya same ta zuciyar sa tayi wani irin tuƙuƙi tare da tsantsan baƙin ciki da ya turnuƙe sa, bazan iya fasalta muku a halin da ya shiga ba domin yadda zuciyar sa take tafarfasa haka yake huci kamar wanda zai dambe, ya kasa jure a halin da yake ciki dole ya silale ya koma cikin mota ya haɗa kai da gwiwa, taya ma za’a ce mishi wani ne ya auri wacce yake ƙauna? Yanzu kenan akwai igiyar auren wani a kanta? Gaskiya bazai iya juran hakan ba, idanun sa gaba ɗaya sun kaɗa sun yi jazur kasancewar sa me rauni wanda ba ya iya jure tashin hankali ko ya ya ne
Ƙarshe Hashim ne ya bincika inda yake tunda ya neme shi ya rasa, a nan ya tarar da shi a cikin mota a matsanancin tashin hankali domin ciwon sa ne yake neman tashi, hankalin Hashim a tashe ya yunƙura da nufin kiran likita
Sai dai shi ya riƙe shi da cewa, “ba ya buƙata, ya san idan ya koma gida ya sha magani zai warke.”
Dole ya haƙura sai dai shi ya tuƙa shi ya mayar da shi gida. Sai da ya zauna da shi a can har ya samu ya sha maganin sa barci ya ɗauke shi kafin ya baro gidan. Ya san saboda MEEMA ya shiga wannan halin shiyasa yake matuƙar tausaya mishi
Momy kuwa da taji labari tunda Hashim sai da ya kira ta, itama ta tashi hankalinta ta nuna damuwar ta tsantsa, sai dai a ranta tayi murna tunda ta san bazai taɓa tsallake auren Luwaira ba kasancewar gobe ne, ko ba komi dole ya ƙyale wancan, shiyasa bata wani damu da dawowar MEEMAN ba
Yayinda Abdul ya shiga murna shi kuwa. Ya rigada ya saka a ranshi duk sanda aka ganta zai je har gida ya sanar mata soyayyar shi ko zata amince, tunda ya san yanzu an yi mishi maganin matsalan shi Umar Faruk ya sami wata, yanzu hankalin sa kwance zai je ya same ta da zancen
Luwaira kuwa a ranan haka ta kwana da baƙin ciki, musamman da ta ji inda ya tafi, ashe dama sabida dawowar MEEMA ce ya bar wajen taron su? Tabbas akwai matsala sai yanzu take ganin haka. Haka suka kwana da Abida suna ta shirya abubuwan da zasu yi duk sanda Luwaira ta shiga gidan Umar Faruk, baza su taɓa bari ya aure ta ba duk hanyar da zasu bi sai sun bi wajen ganin sun raba su.
Washe gari aka ɗaura auren senator Umar Faruk Aliyu Bature da Amaryan sa Luwaira Shamsudden Aliyu Bature cikin sadaki mafi ƙaranci.
MEEMA wacce take gadon asibiti a wajen su Hajiya ta ji labarin bikin tunda har su ma sun leƙa a sa’ilin tana barci suka bar ta da Zabba’u. Sosai maganar ya daki zuciyar ta wadda har sai da ta ɗauke wuta na tsawon lokaci, ta kasa yarda ko shi Umar Faruk ɗin da ta sani ne shiyasa ta sake buɗe idanuwan ta waɗanda suke rufe har sun tara ruwan hawaye ta kalli Zabba’u tace, “You mean Uncle Umar Faruk who says he loves me?”