MEEMA FAROUK Page 51 to 60

Zabba’u wacce take kallon ta; sai ta ji ta bata tausayi, hannun ta ta riƙe da cewa, “it’s he MEEMA, I’m sorry don’t say you will raise your mind kinga you are not feeling well.”
Gyaɗa kanta tayi hawayen na sauka a kan fuskar ta, sai ta saka hannu da sauri ta share su, har ta kawar da kai kuma ta sake kallon ta da cewa, “But he says he loves me. Did he lie to me? Why would he do that to me?” Sai kuma tayi saurin kwanciya jin kuka ya taho mata, ƙudundune kanta tayi tana sakin kukan bayan ta toshe bakin ta yanda baza a ji ba
Zabba’u ta rigada ta gane a halin da take ciki, shiyasa tayi ta bata baki but ko kula ta ta ƙi yi
Ana haka sai ga Umar Faruk ɗin da Hashim sun shigo ɗakin
Dalilin da yasa Zabba’u ta tashi ta ba su wuri kenan, ta fice bayan sun gaisa
MEEMA wacce ta ji muryan su tuni ta shanye kukanta ta saka hannu ta share hawayen
Sai dai Hashim yana kallon idanun ta ya gane tayi kuka, shiyasa ya rikice da tambayar ta abinda ke damun ta?
Ta kasa yin magana bare ta ɗago ta kalle su
Yayinda Umar Faruk na tsaye a setting ta yana faman kallon ta kamar zai cinye ta, yana sanye da wani uban-uban su na farar shadda bugaggiya sai maiƙo take yi, kowa ya kalle sa ya san Ango ne saboda yanda yake wani walƙiya ga tashin ƙamshi da yake yi. Fuskar sa har ta zurma shima saboda damuwar da ke ransa
“Daughter please what’s wrong with you? What happened to you? Tell me?” Uncle Hashim ya sake faɗa yana tallabo kanta ta yanda zasu haɗa idanu
Ita kuma saka idanun ta tayi a cikin nasa sai ga hawaye sun sake cika mata idanu. Sai kawai ta ɓare baki ta saka mishi kuka
Hakan yasa ya sake rikice wa ya hau rarrashin ta duk hankalin sa ya tashi
Ita kuwa ta ƙi shiru sai kuka take yi domin yanda take ji a zuciyar ta baza ta iya jure wa ba dole sai tayi kuka, ita kanta bata san me ke damun ta ba sai dai kukan ta na da alaƙa da jin zancen auren Umar Faruk, haka kawai take jin matuƙar baƙin ciki da haushi a ranta
Yayinda shi kuma lumshe idanun sa kawai yayi yana sauraron kukan nata, ya kasa cewa komi illa sake buɗe ido da yayi yana kallon ta, a duk sokon ɗaya ƙauna da begen ta na ƙara shigan sa. Jin son ta yake yi har a can cikin jini da ɓargon sa, ko son da ya yiwa matar sa Nusaiba be ji makamanciyar abin da yake ji a game da soyayyar MEEMA ba a halin yanzu, be san ya zai yi ba idan ya rasa ta.
Daƙyar Uncle Hashim ya rarrashe ta tayi shiru tana faman shashsheƙa
“Please daughter tell me what’s wrong with you?”
Shiru tayi ta kasa yin magana
Dole ya ƙyale ta sannan ya kalli Umar Faruk yace, “ka zauna mana ka tsaya a tsaye. Ka ga Daughtern nawa iya rigima ce dole sai an ta fama da ita.”
“Nan ya isa.” Yafaɗa a maƙoshi sabida halin da yake ciki
Shi kuma kansa ya jinjina masa alamun ya gane. Sai ya kalli MEEMA yace, “Daughter did not congratulate my dude. Today he is married.” Ya ƙare maganar da murmushi a face ɗin sa
Wani irin ƙunci ne ya sake tabaibaye ta wanda lokaci ɗaya ta ji wani kukan zai taho mata, sai tayi saurin sauke kanta ƙasa tana tsiyayar da hawaye, sosai tayi juriya wajen ta hana bayyanuwar kukan nata but ina ta kasa, kawai kifa kanta tayi a kan cinyanta ta dinga rera kukan har wani jijjiga take yi
Mamaki ne ya cika su, sai dai shi Uncle Hashim sosai ya gane tabbas zancen auren ne ya saka ta kukan nan, dama ya gane tana son shi domin ya ga soyayyar abokin sa a idanun ta, sai dai be yi tunanin har haka ba, sai wani irin tausayin ta ya kama shi, yanzu ya za suyi tunda an rigada an yi auren shi? Dole ya koma rarrashin ta
Yayinda Umar Faruk tuni ya fice a ɗakin sabida bazai iya sauraron kukan ta ba, hakan na ɗaga masa hankali tare da ƙara masa raɗaɗi a zuciya.
Koda Zabba’u ta shigo ta gansu a haka itama nan ta zauna tana sanar da Uncle Hashim ɗin, “da alamu saboda Umar Faruk ne take kuka. Ya kamata ka san yanda zaka yi ka saka yarinyar ka a cikin farin ciki, tana son abokin ka be kamata a bar su haka basu mallaki juna ba, zancen wancan Sajjad ɗin a saka shi ya sake ta don baza a barta da auren shi ba.”
“Ki dena ma zancen wancan banzan don Allah, maganar auren su ma babu shi don ba na son ana sake maganar.” Cewar sa cikin zafi
Dole Zabba’u tayi gum da bakin ta ganin ya nuna fushi nan da nan tunda dama a ɗane yake. Dayake likita yayi musu bayanin halin da take ciki. Yanda yayi mata amfani da drugs waɗanda suke gusar mata da hankali, har abortion ɗin da aka yi mata wanda ya ja mata matsala a halin yanzu, ko yaushe zubar da jini take yi, ga ciwon ciki da ya saka mata shiyasa aka riƙe ta a asibitin a halin yanzu
Daga ƙarshe tashi yayi ma ya fice ba tare da ya sake cewa uffan ba
Zabba’u tace, “an shiga uku! Mutum sai zuciyar tsiya, wannan da ace yaron nan ba ya a halin da yake ciki ai ina tunanin kashe shi zai yi, don ɗaukar shi zuwa barikin su zai yi ya gana masa azaba, sojoji ko mugaye! Allah ya cece shi shima”.
✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️
*TO FA… BABBAN MAGANA… NESA TA ZO KUSA KENAN….*
*Albishirin ku masoyana masoyan littattafai na…. Nesa ta zo kusa… Ƙasaitacce kuma fitaccen littafi na da zai fito muku a sabuwar shekara, salon na daban ne domin Ni kaina ban taɓa yin littafin da ya ɗaukar min hankali kamar wannan ba, iya basirata da ƙwarewata duk na bazar dashi a cikin wannan littafin. _ƊAN SANDA ????????_ kai daga jin sunan ma kun san akwai badaƙala a cikin sa, ƴar uwa ko ɗan uwa kar ka bari kar ki soma a baki labari ki nemi naki kawai ki ga cakwakiyar da ke ciki, ke da kanki zaki san tabbas littafin yayi, tabbas ya ci kuɗin sa domin sai Abu me kyau ake iya cire kuɗi a siya… A kan farashi me sauƙi ɗari biyun ki zai biya miki buƙata domin samun farin ciki a zukata… Tirƙashi _ƊAN SANDA_ labarin wani murɗaɗɗen saurayi ne da ke cike da burin ɗaukar fansa, ya hana kansa sukuni sai ya zaƙulo waɗanda suka kashe mishi Mahaifi, inda kuma gefe ɗaya yana tare da maƙiyan sa ba tare da ya sani ba, Matarsa ita ce ke da burin ganin bayansa, itama zuciyarta cike take da burin ɗaukar fansa, ta sha alwashi sai ta ga bayansa zata haƙura, dalilin da yasa ta shiga aikin ƴan Sanda kenan… Shin mene ne yayi mata da zafi haka?… Tirƙashi ƙa-ƙa ƙa-ƙa ƙa-ƙa muje zuwa FAN’S kar ku soma a baku labari ku nemi naku.. littafin zai zo a watan January a kan farashi me sauƙi 200 kacal. ???? Domin ƙarin bayani ku tuntuɓi wannan Numban only WhatsApp 07065334256 ko kuma 08146470539*
✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️
Zuwa dare aka kai Amarya Luwaira Part ɗin Angon ta Umar Faruk. Ɗakunan ƙasa aka ajiye ta tunda nan ya zaɓa mata aka saka mata kayan ta
An kai Amarya an watse har ƙawayen Amarya sun tafi babu Ango babu labarin shi. Abida ce kaɗai zaune da ita
Luwaira kuka take ta mata domin ta kasa jure wa
Dole Abidan tayi ta bata baki tana faɗa mata, “daga yau shikenan, ta kwantar da hankalin ta, idan ma be sanja ba zasu ɓullo masa ta hanyar da dole zai sanja, ko ta halin ƙaƙa sai sun juyar da hankalin sa zuwa gare ta.” Haka Abida ta zauna tayi ta ziga ta tana bata shawarwarin da ita taga ya kamata. Ƙarshe itama tafiya tayi ta bar ta tunda be zo ba kuma dare nayi
Su Hafsah suka zauna da ita, daga ƙarshe su ma suka wuce ɗakin su saboda barci suke ji, kasancewar Hafsah ta fi wayau sosai ita ta ciro musu kayan barcin su suka saka suka kwanta, dama wata rana ita take saka musu kayan idan Dadyn su ba ya kusa suna jin barci.