MEEMA FAROUK Page 51 to 60

Luwaira ta kasa kwanciya saboda hankalin ta ya gaza kwanciya, a yanda take ji tamkar ta mutu tsaban baƙin ciki, wai yau ranan farin cikin ta, ranan da ta ci burin zuwan ta shi ne ta zame mata a haka? Taya zata iya jurewa? Dole tayi kuka, kuka ba kaɗan ba. A haka ta kwanta a gadon ko kayan jikin ta ta kasa sauyawa sai barza kuka take yi, tun tana yi da karfi ta koma yi a hankali.
Shi kuwa Umar Faruk sai ƙarfe 11:00pm. Ya shigo gidan, ko irin ledan nan na tarban Amare be shigo da shi ba, shi da farko ma yayi tunanin ta daɗe da barci, tunda da ya shigo ɗakin su Hafsah ya shiga yayi musu addu’a kafin ya fito zai zarce ɗakin sa. A nan ne ya tuna da ita ya tura ƙofan ta ya shiga, ganin haske tarwai sai ya tsaya kallon ta, a lokacin ne ya ji shashsheƙan kuka na tashi wanda ya tabbatar ita ce ke yi, hakan yasa ya nufe ta jiki a sanyaye tare da jin tsantsan tausayin ta na shigan sa. Kiran sunan ta yayi bayan da ya tsaya a bakin gadon
Hakan yasa ita kuma ta ɗago da kanta hawaye sharkaf a fuskar ta, har yanzu ta kasa yin shiru kuwa sai ma wani kukan ne ta sake taho mata
Ya kasa ce mata komi domin be san ta ina zai fara ba, sai mulmula hannayen sa yake yi daga ƙarshe kuma ya daure ya soma bata haƙuri da cewa, “kiyi haƙuri Luwaira na san ban kyauta miki ba, but ban yi hakan domin in ɓata miki ba, don Allah kiyi min uzuri ki yafe min kinji?”
Shiru tayi sai dai ta kasa ɗago kai ta kalle shi bare tayi magana, har a cikin zuciyarta ta ji sanyi sai dai ƙuncin da ke ciki ya gaza tafiya, zuciyar ta na mata ƙuna idan ta tuna Mijin da take Aure ba ta ita yake yi ba, ta wata banza can yake yi, wanda har a ranan auren su ya fifita ta a kanta, wannan abun baƙin cikin da me yayi kama?
Shi kuma jin tayi shiru sai ya samu waje ya zauna a gefen gadon, ya ɗau fiye da three seconds be iya furta komi ba. Daƙyar ya iya saka hannu ya janyo ta jikin sa wanda sai da yayi dauriya da jarumta wajen aikata hakan, hannun sa ɗaya kawai ya ɗaura a kanta ya soma rarrashin ta ba tare da ya furta komi ba
Sai dai ita tuni tayi tsit ko motsin ta ba a ji, ta gama sandare wa da shiga wani hali da jin ta a jikin wanda ta fi ƙauna fiye da rayuwar ta, yau ce rana ta farko da hakan ta taɓa faruwa da ita a game da shi, yau ita ce wai a jikin Umar Faruk yana faman rarrashin ta. Wayyo Allah daɗi! Bazan iya misalta muku a yanayin da ta shiga ba
Shi kansa ya gane hakan da yake mata ya saka ta shiga wani hali. Shiyasa ya janye jikin sa tare da ɗaga kanta da ta sake luƙume shi a jikin sa, cikin sanyin murya yake kallon ta da faɗin, “ki kwanta ki huta sai Allah ya kai mu gobe kinji?” Be jira kuma amsar ta ba ya tashi da sauri yayi ficewar sa
Tsaban baƙin ciki ya turnuƙe ta sai ta fasa kuka tana komawa ta kwanta. Kuka take yi sosai tare da sake shiga baƙin ciki. Ranar da ta ci burin zuwanta ta kasance da masoyin ta wai shi ne zai tafi ya barta a haka? Babu yanda ta iya; a haka sai dai barci ɓarawo ya sure ta cike da baƙin ciki da damuwa a ranta.
Washe gari da sassafe Umar Faruk yayi shirin sa ya bar gidan ko bi ta kanta be yi ba, yaran sa kawai ya duba, burin sa kawai ya isa asibiti wajen MEEMA ya ga lafiyan ta daga can sai ya wuce Office, domin shi ko ɗaukan hutun nan ya ƙi yayi tunda be ga amfanin zaman shi a gida ba, ba wannan ne karon farkon sa na aure ba.
Luwaira sai ƙarfe takwas ta tashi barci. Shima ɗin su Hafsa ne suka tashe ta da ƙiriniyar su, kasancewar suna murnan kawo musu Luwaira a matsayin Aunty da suke yi. A wajen su ta ji labarin Dadyn nasu ya fita, tunda a lokacin har tayi wanka ta cancare a cikin wata farar atamfa me silƙin ja da ruwan goro, ɗinkin riga da skert sun matse ta gam sun yi mata daram tamkar zata fashe tsaban yanda suka yi mata, kasancewar ta me jiki Masha Allah. Yayinda Fuskar nan nata ta ɗauki make-up kamar wacce zata je gasar kyau. Sai dai tunda taji ya fita sai ta koma ta zauna kamar ta fashe tsaban haushi. Tsawa ta daka wa su Hafsan a kan, “su bar mata ɗaki ko ta ci uban su.”
Sun rikice yaran kasancewar ba haka suka saba gani ba, in fact ma babu wanda yake musu tsawa bare hantara yau sai ga shi sun samu a wajen Luwaira, shiyasa suka fice da gudu Yusra har da kukan ta suka wuce Parlour suka zauna. Ko abinci sun kasa ci dama suna jira ne Luwaira ta zo ta basu tunda Talatu ta kawo ta jera, amma yanda ta nuna musu ne yasa suka koma suka zauna zugum suka yi shiru.
Ita kuwa tana ɗaki tana waya da Abida yayinda take sanar mata da komi abinda ya faru, wulaƙancin da Umar Faruk yayi mata na ƙin kwana da ita, ko irin tarban nan na Amare be yi mata ba
Abida tace, “gaskiya dole mu tashi tsaye Ƙawata don zancen zama be taso ba. Wlh sai kin yi da gaske wajen samun zuciyar mijin ki tunda har yana wajen wata, wai to kin san yarinyar da yake so ɗin ne ya kamata fa idan zamu tashi tsaye dole sai mun san ita kuma da me ta fi ki da har yake rawan ƙafa a kan ta?”
Da damuwa Luwaira tace, “nima ban santa ba gaskiya, sai dai na ji Momy tana faɗin ƴar Abokin sa ne.”
“Kina nufin ƴar abokin sa zai aura? Wato yarinya ce kenan?”
“No yarinyar Auntyn Abokin sa ne, sai dai kuma ba a nan tayi rayuwar ta ba daga Abroad Wai ta zo.”
“Cab ɗi… Ai ko dole ya rikice a kanta don ko ban ganta ba na san zata fi ki gaskiya, kin san nan da can ba ɗaya ba wayewan ku zai bambanta, wa ya sani ma ta ba shi ya sha? Well. Yanzu ki bari zan zo sai mu zauna mu sake tattaunawa, idan ma ya kama mu sanar da Momy komi domin ta taimaka mana sai muyi…”
Da sauri Luwairan tace, “a’a ba na son a saka Momy a zancen nan gaskiya domin har yanzu ba wai yarda da ita nayi ba…”
“Kamar ya? Ban gane ba?” Abida ta katse ta da faɗar haka
“Idan kika zo zamu yi maganar please. Sai kin zo ɗin”. Daga nan suka yi sallama ta ajiye wayan tana kwanciya tare da tsira wa waje ɗaya idanu ta hau tunani.
????????????
*MEEMA FAROUK*
????????????
Share this
[ad_2]