MIJIN MATACCIYA Page 1 to 10

Budar bakin Abba sai cewa yayi ai muddin idan suka ga ba ayi auren nanba tofa kwanan dayane acikinsu ya kare amma shi ko bayan ransa bai yarda Hanan ta auri wani miji bayan abokinsa ba,shine kadai mijin da ya zaba mata kuma ya yarda ta zauna dashi,
Haka mamaye tafito jiki babu kwari domin Abba fada yayi ta yimata yana cewa ya zata biyewa shirmen Hanan duk da ta girma ai har yanzu bata san abinda zai amfaneta agaba ko sabanin haka ba tunda abinda babba ya hango daga zaune yaro ko yahau rimi ba lallai ya hangoba,shi yasan mijin da yadace da hanan sannan yasan waye ya kamata yazama tare da ita shiyasa yayi mata wannan zabin.
Kasancewar yanzu bata iya kuka yasata yin shiru tana sauraren fadan da mamaye ke yimata cikin lallami da nasiha tana cewa ta daure ta cije tayiwa mahaifin ta biyayya insha Allah zataji dadi agaba sannan zatayi farin ciki ko dan biyayyar da tayiwa mahaifin ta sannan mamaye ta kara da fadin,
“Insha Allah Hanan sai kin yi alfahari da mahaifin ki,sai kinyi dariya agaba ko dan bin umarnin mahaifinki da kikayi kika masa biyayya,iyaye ba zasu taba cutar da yayansu ba sai dai abisa kuskure,duk abinda kikaga mahaifinki yayi to yayi miki ne dan soyayyar da yake yimiki,ke kanki shaida ce mahaifin ki yana tsananin sonki saboda ma soyayyar da yake yimiki da ace bani na haifeki ba to da bazan iya zama daku ba domin yafi fifitaki akaina… Ko kin manta yanda kuke hade min kai keda shi…?”
Murmushi mamaye tayi,itama Hanan din murmushi tayi tana tuno shekarun baya nan abubuwan da suka faffaru abaya suka soma dawo mata kamar yanzu ne suke faruwa,
Kamar yanda mamaye taso haka ta dan saki ranta tana hira har da su dariya idan mamaye ta fada mata wani abu,sai da aka kira sallar magriba sannan suka tashi,ita da yake bama sallar zata yi ba kitchen tawuce ta zubo abinci dan kadan domin yanzu bata iya ci dayawa,sai da tagama cin abincin sannan takoma cikin daki nan ta bude sakon da minister ya aiko mata,
Ledar tafara budewa nan taga tamfatsetsiyar sabuwar waya kirar kamfanin Samsung mai mutukar kyau da daukar hankali harda sim card aciki,
Tabe baki tayi cike da jin haushi tace,
“Tsabar ya rainawa mutane hankali da wayo shine shi baizo ba saboda yafi karfin yazo sai aikowa yayi,kuma ko waye yace masa bani da arzikin waya da har zai siyo ya bayar akawo min…. Saboda ga yar talakawa ko” kwafa tayi da karfin gaske sannan ta bude envelope din tana tsaki,
Kudi tagani bugun Abuja sababbi fil yan dubu dubu wanda bazata iya kiyasta adadinsu ba sannan kuma ga dan karamin card nan ajiki anrubuta,
_Ibrahim Sulaiman I._
Sai phone number dinshi a k’asa, maganar PA ce ta fado mata inda yake cemata,
“Akwai number dinshi ajiki yace idan kina da bukatar magana dashi ko wani abu mai kama da haka sai ki kirashi….”
Ita bazata kirashi ba amma dole ce zata sa tayi hakan ko dan tunatar dashi kuskuren da yake neman tafkawa dan kawai yana da kudi,saboda kawai yana da dama shine zaiyi amfani da karfin mulkinsa wurin musgunawa wasu,
Number wayar tashi ta kwafa tasoma kira domin so take ta fada masa maganar da zata bakanta masa rai watakila ma idan yaji haushi yace yafasa tunda bata da kunya,
Saida ta kira wayar sau hudu amma bata shiga sai dai ta danyi wata yar kara sai ta yanke,tsaki taja ta harhada kan kayan ta mayar dasu cikin leda tana kokarin tashi tajiyo karar shigowar text massage,
Kamar bazata duba ba sai kuma ta dauka tana dubawa,
_Am Little busy now,text me please._
Shine abinda taga anturo da wata special number mai dauke da 33333, tunani tafara yi to waye kuma wannan? Zuwa can tagane minister ne,kai duk yanda akayi shine tunda ita dai yau bata kira kowa ba sai shi,kai shi dinne ma,
Saida ta duba number tasake dubawa sannan ta mayar masa da reply,
_Ya kamata dai idan angirma asan angirma,duk zawarawan duniyar nan da rikakkun yanmata ka rasa wacce zakace kana so sai ni,nidai ka cuceni kuma kasani kawai zanyi zaman biyayya ne bawai dan ina soba saboda ni inada wanda nake so,idan kuma dan kana da kudine to ni kudinka baya gaba na._
Shine abinda ta rubuta ta tura masa amma shiru babu amsa har tagaji ta daina ma tsammanin zai turo mata da reply, “kaji irin wulakancin nasu ai” tafada aranta kafin ta tashi taje tashiga wanka,har tagama komai nata ta shirya ta kwanta mutumin nan baibi ko ta kanta ba,har tagama yanke tsammanin zai kulata domin 11 tawuce.
***
Lokacin da Hanan ta kirashi yana cikin meeting da yan uwansa ministoci,shi a ka’idar wayarshi idan ka kira asalin layinshi bazai shigaba sai dai idan text massage kayi masa to wannan zai shiga har yagani amma idan kira kayi to bazai shigaba amma dai zai ga kiran a dayan layinshi da akayi forwarding kiran zuwa can,to idan yasanka zai kiraka ta special line dinshi idan kuma bai sanka ba shikenan sai yakyale,itama Hanan dalilin da yasa ya san itace shine abbanta yatura masa number din tunda jimawa tun bayan lokacin da yabashi aurenta da yakirashi domin yimasa godiya yatura masa number dinta wai ko zai kirata shi kuma baice a’a ba amma aganinshi me zai kirata yace mata? Shi baida bukatar number dinta saboda baida case da ita,
To yau yana tsaka da meeting yaga kiranta shine yayi mata text, lokacin da ta dawo masa da reply ma shi ko budawa baiyi ba saboda lokacin har yasake shiga wani meeting din da masu bada shawara ta musamman akan harkokin wasanni da matasa gashi yan jarida suna waje sunyi cincirindo suna son ganawa dashi dangane da wani rade radi dake ta faman kaiwa da kawowa acikin gari na cewa wai gwamnatin tarayya zata sauke wasu masu ruwa da tsaki a harkar gwamnati har su dari daya,
Gaba daya bai samu kansa ba sai wurin misalin karfe 11 sai a lokacin yabar office bayan yagama ganawa da yan jarida yanufi gida,
Agajiye yake mutuka sannan ga ciwon baya dake dan damunsa da kuma ciwon kirji shiyasa tun kafin yakarasa gida yasa nura yakira masa likitansa wato Dr Al’amin,
Duk jikinsa jinsa yake babu karfi ga rashin cin abinci,yana komawa gida yayi wanka yasa jallabiya da gajeren wando aciki,a dan karamin falon shakatawarshi ya zauna ya hada coffee mai zafi yasha yana gama sha yaji amai na kokarin fito masa, bathroom din dake cikin falon yashiga yayi aman sannan yadawo falon ya zauna daidai lokacin da PA yashigo yana sanar dashi zuwan Dr cemasa yayi yashigo sannan ya dan kishingida jikin kujerar da yake kai,
Sai da Dr yagama dubashi sannan ya daure masa hannunshi da wata yar roba yana duba jijiya saboda anan ne zai dan yimasa allura sannan zai kara masa wani dan karamin ruwa leda daya,
Sai lokacin ya dauki wayarshi yasoma duba sakon da aka tutturo masa nafi yawa friends ne da masu neman taimako ahaka har yazo kan na Hanan,ganin abinda tace abin yaso ya bata masa rai,wai yara kanana sai su zagi mutum dan kawai maganar aure ta hadasu, yanzu ita wannan yarinyar ko ahanya ta ganshi ta isa ta fada masa wannan maganar ba dan maganar aure ta shiga tsakani ba?
_Ok_ shine abinda yatura mata kawai,yaci gaba da karbar ruwan dake shiga jikinsa wanda Dr ke kara masa,ajiye wayar yayi agefe ransa adan bace,
“Ranka yadade wallahi stress ne kawai ba wani abuba, sannan kuma yallabai maganar nan tawa dai kamar koda yaushe,dole fa sai ansamu abokiyar debe kewa….. Saboda agaskiya kana bukatar mace ko dan lafiyarka”