MIJIN MATACCIYA Page 1 to 10

Shiru Khalil yayi yana dan sake jingina sosai cikin kujera, so yake idan yagama da Dr yaje yaga Aryan saboda yau throughout bai ganshi ba,yadai ganshi da safe kafin yafita lokacin ko ma tashi daga bacci baiyi ba kasancewar yau asubanci yayi.
Wurin karfe 12 saura sakon minister yashigo wayar Hanan dama har lokacin bata yi bacci ba,tana dubawa taga ok,ranta yayi mutukar baci,inbanda rashin mutunta dan adam Menene zai ce mata wani ok,
Tsaki tayi tasake tura masa da wani text din,
Bai kulata ba sai da Dr yatafi shima PA yatafi, bedroom din Aryan yaje ya dubashi sannan yakoma part dinshi yawuce bedroom ya kwanta domin Dr yace yadan samu bacci akalla na awanni shida. Massage din da yaji yashigo tun dazu ya duba,
“Again?” Yafada ganin Hanan ce ta sake turo masa da reply,
Budewa yayi ya tsurawa sakon nata ido cikin nutsuwa,
” _Ni dai ancuceni anrabani da wanda nake so saboda kawai budurwar zuciya,angirma ma ba za a hakura ba,yadai dace idan angirma asan angirma._”
Afili ya karanta sakon kamar yana karantawa wani,wai shine mai budurwar zuciya, murmushi yayi saboda shi abinma dariya yaso bashi,sai dai gaskiya turancinta ya burgeshi saboda duk sakonnin tana turosu ne da harshen turanci da alama dai ta kware a fannin,
Bai cemata komai ba ya ajiye wayar tashi saman bedside drawer sannan yakashe bedside lamp din dake gefen gadonshi ya lumshe idanuwanshi saboda son bin umarnin Dr,yana son ya dan samu bacci kamar yadda Dr yace……鉁嶏笍
_Ga mai bukatar siyan littafin mijin matacciya zai tura naira 200 ta account dina 3112877210 Aisha Ibrahim first bank sai atura shaidar biya ta 07044644433,ko kuma recharge card na MTN ta wannan number din 07044644433 sannan sai atura shaidar biya ta number da aka turawa._
*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎
8/14/20, 10:07 AM – Ummi Tandama: 漏锔? *HASKE WRITERS ASSOCIATION.*
_(Home of expert & perfect writers)_
*D’AND’ANO…..*
Share this
[ad_2]