MIJIN MATACCIYA 1-END

MIJIN MATACCIYA Page 1 to 10

Tunda Abban London yasoma maganar bai kalleshi ba sai lokacin jin yace wai zai samu madadin Ramlat koma wacce tafita,tab ina ai shikam yasan bazai taba samun ko kwatankwacin rabinta ba shiyasa ma shida aure yanzu haihata haihata sai dai yaga anayi amma yagama aure aduniya idan yamutu yaje lahira sa hadu da Ramlat dinsa su cigaba da rayuwar aurensu a aljannah,

Har Abban London yagama nasiharsa yafita baima saniba kasancewar yafada kogin tunanin da yasaba. Ganin al’amarin nasa bamai sauki bane yasa hajiya Zaitun mahaifiyarshi sanya limamin dake jansu salla agidan yimasa taimako koda na addu’o’i ne dama kuma babu laifi nasihar Abban London ta dan shigeshi domin har ansamu ya fito daga dakin Zaid yaje wurin jaririnshi dan kimanin kwanaki biyar daukar jaririn yayi yai masa huduba yana fitar da kwalla,

“Menene sunanshi…?” Babbar yayarshi wato anty saudat ta bukata,

“Sulaiman Aryan…”

Daga haka yamika mata shi yatashi yafita,makabarta yasaka Zaid ya rakashi ya nuna masa kabarin Ramlat tun daga wannan lokaci kuma yasamu wurin zuwa sai yaje yasaka kabarin agaba yayita kuka har akayi sadakar bakwai gashi ba ci ba sha sai idan an takura masa hajiya tazo da kanta sannan zai yarda yasha ruwan tea amma rabon da yasakawa cikinsa abinci har yamanta.

Yauma saida yajima agaban kabarin yana rusar kuka kamar daga sama yaji andafashi ta baya cikin hawaye yajuya,wani mutum yagani tsaye dan dattijo dashi cikin taushin murya dattijon yace,

“Kayi hakuri bawan Allah….ka dauki k’addara wannan kukan da kake zuwa kullum kanayi ba mafita bace mafita guda daya ce itace addu’a….”

Gyada kanshi yayi ya goge hawayensa yana furta “nagode….nagode”

Juyawar da zaiyi yaga wayam babu dattijon nan babu alamarsa, addu’a yayiwa Ramlat sannan yamike yana fadin,

“Insha Allah zaki zama abar tunawa acikin zuciyata akoda yaushe Ramlat….bazan manta dakeba da yardar Allah, Allah yasa kina aljannah kina hutawa kin manta da wahalar rayuwar duniya….”

Motarshi yanufa yabude yashiga yanufi gida,duk mutane sun tattafi sai wadanda ba arasa ba wato na jiki jiki,yana yin parking masu tsaronsa dake zaune acan gefe suka mike suka nufoshi domin a yan kwanakin nan yahanasu binsa shi kadai yake zuwa kabarin Ramlat,

Falon hajiya Zaitun ya nufa amma sai karar jiniyar motocin gwamnati suka cika gidan da ma unguwar gaba daya hakan ya tabbatar masa da cewa mai girma gwamna ne yazo yimasa ta’aziya,

Fita yayi yaje ya taryeshi yashigar dashi zuwa dakin saukar baki nan yayi masa ta’aziya sannan ya bukaci ganin jaririn da marigayiyar tabari, Zaid ne ya dsukoshi yakawoshi wurin mai girma gwamna nan ya karbeshi yayi masa addu’a sannan yabada shi yayi musu sallama yatafi bayan ya ajiye kudi daruruwa. Cikin gida yashiga bayan tafiyar mai girma gwamna,zazzaune yasamu kowa afalo ana yin sallama da iyayen Ramlat wadanda zasu bar gombe ayau zasu nufi gida wato jos,da alama kuma dama shi kadai ake jira,

Zama yayi a kasa kusa ba Abban London wanda ke sanye cikin kayan gida amma na sarauta sai dai yau babu jibga jibgan rigunan nan da yasaba sawa shiyasa yafito a siririnsa,

“Ibrahim Allah yakara mana hakurin jure rashin Ramlat yakuma raya abinda tabari,mu zamuje mu tafi amma zamu tafi da jaririn sai mu kula dashi awurinmu…..” Alhaji Tamim maihaifin Ramlat yafada yana kallonshi,

“A’a Abba ina neman alfarmar ku kubar min yarona zan rikeshi awurina insha Allah kuma zan rinka kawo muku shi kuna ganinsa….”

“To shikenan hakanma babu aibu fatanmu dai Allah ya rayashi”

Kowa dake wurin da Amin ya amsa,

“To yanzu waye zai shayar dashi? Sai kabawa Humaida ko Lubnah tunda sune suke shayarwa….” Inji anty saudat,

Ai shi sai lokacin ma yatuna da batun shayarwa shi baida ra’ayin kowa ya shayar masa da yaronshi madara zai rinka bashi,

“A’a madara zai rinka sha…” Yafada atakaice sannan cikin sauri yasake kallon anty saudat,

“Da wata cikinsu ta shayar dashi?”

“Babu wadda ta shayar dashi madara ake bashi dama ana sone asanar dakai first sai wata cikinsu ta daukeshi”

“Basai andaukeshi ba abar min shi ni zan kula dashi”

“Kai ina ka taba jin namiji yakula da jariri? Kanada nonon da zaka bashi ne? Wadannan da akace kabawa wata cikinsu ba yan uwanka bane uwa daya uba daya ba?” Yakumbo mariya tafada cikin fada,shiru yayi baice komai ba amma shikam harga Allah bazai iya bawa wani rainon yaronshi ba shine zai kula da kayansa,

“Tunda kai ba mace bane tofa ya zama dole kabawa wata cikin yan uwanka ko yan uwan matarka akula da shi….” Yakumbo mariya tasake fada tana kallonsa,

Idonshi rau rau cikin rawar murya yace,

“Yakumbo kuyi hakuri karku rabani da Aryan bazan iya jurewa ba na rokeku da girman Allah kubar min shi…”

Yakumbo mariya ta bude baki kenan zata sake magana Abban London yayi gyaran murya yace,

“Ya isa haka tunda hakan yake so to muyi masa yadda yake so din ina ganin zaifi,Allah yaraya mana shi mudai shine fatanmu…..”

Gaba daya akan hakan aka tafi,aranar yaje babban store ya lodo duk wani abu wanda jariri ke bukata,madara kuwa yasiyota tafi gaban abinda tafi,umma barira k’anwar abbansu yadauka ta dawo family house dinsu gaba daya da zama tana tayashi kula da Aryan dayake ita din ahalin yanzu bata da aure kuma duk yaranta sun manyanta dama guda uku ne,shine da kansa ke yiwa Aryan wanka ya shiryashi yabashi abinci duk wani abu na kula da jariri ya iya ahalin yanzu kamar dama can yajima yanayi,indai kaga umma barira tayiwa Aryan wanka ko tsarki ko wani abu mai kamada haka to Khalil baya nan amma indai yana nan shine ke yimasa komai gaba daya rayuwarsa yanzu ta ta’allaka ne akan kula da Aryan ko aikinsa yar sama sama yake yimasa cikin haka har Aryan din yacika shekara daya nan kuma su yakumbo mariya suka sakashi agaba da maganar lallai lallai lokacin da zaiyi aure kuma yayi domin bazai yuyu yayita zama babu mace ba,duk lokacin da suka yi masa irin wannan maganar tayar masa da hankali sukeyi yayita kuka har takaishi da kwanciya a asibiti,daga karshe suka yanke shawarar hadashi aure da kanwar matarshi margiyaya mai suna zulaiha amma fafur yaki aminta wai shi bazai iya auren kanwar Ramlat ba yana jin kunyarta koda bata raye daga karshe dai sai hakura sukayi suka zubawa sarautar Allah Ido suka cigaba da rakashi da addu’a domin duk wadda aka samo masa akan za ahadasu aure baya yarda idan kuma ance yasamo da kansa sai yace shi baida wannan lokacin haka dai suka kyaleshi suna tayashi da addu’a.

***

BAYAN SHEKARA SHIDA………….鉁嶏笍

*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎

: 漏锔? *HASKE WRITERS ASSOCIATION.*

  _(Home of expert & perfect writers)_

*D’AND’ANO….*

*MIJIN MATACCIYA….*馃挒

 *_NA_*

*_UMMI A’ISHA_*

WATTPAD:-ummishatu

亘爻賲 丕賱賱賴 丕賱乇丨賲賳 丕賱乇丨賷賲.

     *3*

Washe gari

**

    ~~~Tunda yafara tafiya akan titi kowannensu yayi shiru babu wanda yayi magana har saida sukayi tafiya mai nisa sannan ya dan kalleta inda take zaune agefen kujerarshi hannunta rike da wayarta tana dubawa,

“Hanan…. Bakice komai ba fa kinyi shiru kin barni da nazari…..”

“Ai nayi magana mujahid kawai dai baka ji dadinta bane,nafada maka kayi hakuri ka jira nagama service dina sai ka turo iyayenka,to inma banda abinka kai da kayi hakurin shekara da shekaru ai bana tunanin hakurin shekara daya zai zame maka damuwa, wallahi insha Allah kamar yaune zamu yi aure……”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button