MIJIN MATACCIYA 1-END

MIJIN MATACCIYA Page 1 to 10

Dan sassauta gudun da yake yi yayi sannan ya kalleta cikin sanyin jiki,

“Wallahi ni gani nakeyi kamar baza muyi auren nan ba hanan shiyasa kika ga duk hankali na yatashi…..”

“Hmm kajika da wata magana kuma…. Dan Allah kadaina wannan maganar”

“Shikenan nadaina”

Da wannan maganar yana ta faman nanata ta suka isa unguwar kurna gidan anty salaha wato babbar yayar su Hanan,saida Hanan ta shigar da mujahid suka gaisa sannan yayi musu sallama yatafi amma da yamma zai sake dawowa ya dauki Hanan. Agidan anty salaha dinma dai maganar guda daya ce shine ta tafiya service wuni sukayi suna wannan hirar har lokacin tafiyar Hanan yayi nan ta kira mujahid yazo ya dauke ta anty salaha nata fadan wai karfi da yaji ta maida mujahid driver dariya Hanan tayi tace wai ai dama namiji bawan matane idan bai kyautata mata ba tunda yana sonta har sai yaushe?,haka dai suka karasa gida cikin farin ciki da kaunar juna bayan mujahid ya dan yimata siyayya ahanya. Acikin yan kwanakin Hanan tagama hada komai nata da take bukata kullum cikin lissafi take su shamsu na tayata ai kuwa aranar da akayi posting ta duba dash board dinta nan taga ankaita Abuja tsalle ta daka sannan ta dire tana fadin “yes” murna kamar zata taka rawa nan ta soma kiran yan ajinsu wadanda suke mutunci tana tambayar inda aka kaisu sai dai fin rabi duk sunansu bai samu fitowa ba yanzu sai zuwa batch na gaba wadanda sunan nasu kuma yafito duk wasu garuruwan aka turasu ita kadai aka tura Abuja sai ko wasu yan department din wadanda bama lallai ta sansu ba. Aranar da za ashiga camp din aranar ta shirya ta tafi,da tare da shamsu zasu tafi zai rakata amma ganin Abuja ne yasa aka barta ta tafi ita daya shamsu sai tsokanarta yake yi yana cemata gaskiya ba karamar sa’a tayiba domin Abuja special posting ake turawa can ba kowa ake kaiwa ba amma fi tura yaran manya wurin,ita dai yau baki har kunne zata tafi camp,wata dirkekiyar trolley ta tafi da ita wadda ta hade gaba daya kayanta aciki amma sauran abubuwan bukata kamarsu bokitin wanka da makamantansu tace sai taje can zata sissiya,har tasha shamsu ya rakata yasata a motar Abuja direct sannan yatafi, mujahid kuwa daga can inda yake wato jahar yobe yakirata awaya yafi sau 30 acewarsa shi da yasan cewa ita daya zata tafi da baiyi tafiyar nanba da yajira yarakata, murmushi tayi tace masa babu matsala insha Allah zata kular masa da kanta.

***

  Tunda yadawo daga makaranta ya hakimce akan kujera yana ta faman buga tv game dinshi umma barira tayi kiransa har ta gaji yaki tashi suje tayi masa wanka tabashi abinci yaci,

D’an turo baki yayi lokacin da umma bariran ta shigo takai hannu ta kashe game din da yake yi,

“Ka tashi muje kaci abinci nace ko,ga David can tun d’azu yagama hada abinci amma inata kiranka kayi kunnen uwar shegu…..”

Shure shure yafara yi zaiyi kuka ganin ta kashe masa game dinsa,zama tayi akusa dashi sannan cikin fara’a tace,

“Yawwa yaron babanshi,maza tashi muje kaci abincin kafin abbanka yadawo yakaika unguwar ko?”

Daga kai yayi yana dariya,

“Umma Daddy ai zai siya min doki ko?”

“Ehh zai siya maka duk wanda kake so”

Makalkaleta yayi ta daukeshi suka fita zuwa dining area wanda ke hade da kitchen dinsu,kan kujera ya haye umma barira ta zuba masa abinci tabashi abaki sannan ta daukeshi zuwa dakinshi tayi masa wanka bayan ta shiryashi ne Khalil yakira waya nan suka lalace wurin hira shida Aryan tamkar sun shekara basu ga juna ba sai surutu Aryan din keyi masa shi kuma yana biyeshi dakyar umma barira ta sa Khalil ya katse wayar shi kuma dan rigimar tata nan ya kwanta yafara bacci.

***

 Tunda tagama registration tasaka white take faman daukar hotuna wadanda tayisu sunfi guda 50 wani ita daya wani kuma itada sabbin kawayen da tayi wato Khadija da hajara,tun lokacin da tafara hotunan take ta turawa shamsu da mujahid, kayan kam ba karamin karbarta suka yi ba dan duk inda ta gifta sai kaji ana cewa “yarinya mai kyau”, dan hijabin dake jikinta iya kafadarta ne baida girma sosai sai farar t shirt ta kamfanin Polo da farin wando wanda ya tsaya iya kwaurinta tasaka farar safa da farin combos sannan ga yar karamar jaka daure a kugunta. Ba kadan ba tayi mutukar kyau wanda har ita da kanta ta shaida hakan.

Tun shigarta camp bata taba karbar abincin da ake rabawa aciki ba maami market take shiga ita da su khadija suje suci abinda suke so su biya kudi,gashi ta samu wani guy ya makale mata wai shi Ashraf wanda ko ba afada mata ba tasan dan masu ido da kwalli ne kai kusan ma yaran dake camp din duk yayan masu fada aji ne dan sai yanzu take gasgata maganar da yaya shamsu yafada mata cewar special posting ake turawa camp din Abuja,

Tana son ta shiga parade domin yana burgeta amma Ashraf ya hana ta sai hakura tayi,haka zai jata zuwa maami market yayita kashe mata kudi itada friends dinta,gaskiya taji dadin zaman camp dinnan da tayi domin tayi shi ne cikin walwala da jin dadi babu abinda take yi sai dai taci abinci ko wankin kayanta biya take yi awanke mata baya ga cin abinci babu abinda take yi koda yaushe tana clinic ita da Ashraf suna hirar duniya, ranar da akayi canival day kuwa aranar tasan Ashraf ya danganci sarauta domin shigar yayan sarauta yayi,ita kam kayanta na hausawa ta saka ita da kawayenta atamfa dinkin riga da skirt harda mayafi ranar ma sunsha hotona kamar babu gobe. Saida suka yi sabo da mutane sosai acikin satin ukun da sukayi a camp,ranar talata suka fita inda aka tutturasu duk guraben da yakamata,abin haushi duk cikinsu kowa inda aka turashi daban amma duk da haka sun yanke hukuncin cewa zasu zauna awuri daya ita da su Khadija wato a corpers lodge din da aka tanada musamman dan yan kano,

Haushi kamar ya kasheta lokacin da taga wai makaranta aka turata su kuma su hajara duk ministries aka kaisu, Ashraf kuwa mutuminta yana babbar fada domin shi dama sai da ya zabi inda yake so sannan ya gayawa babanshi kuma can din aka kaishi,

Su hajara nata tsokanarta suna kiranta da malama ta shirya ta nufi makarantar domin yin report,tun acikin taxi take faman mita acikin ranta domin gaskiya Abuja akwai tsadar rayuwa yanzu daga inda mai taxi ya daukota zuwa makarantar da zai kaita yace sai tabashi dari bakwai wai da dan nisa ita dai duk abinnan yafara damunta gaskiya ba zata iya wannan tsadar rayuwar ba idan taga babu haza itama redeploy zata yi. Lokacin da taje makarantar yar kauye ta zama domin bata taba ganin hadaddiyar makaranta makamanciyar wannan ba a tarihin rayuwarta, makarantar ta hadu ta tsaru fiye da hasashen mai karatu,gata tana da girman gaske gashi ta kawatu ta ko ina kamar a k’asar turai gaskiya wannan makarantar ko shakka babu zata yi tsada domin taci kudinta,

Tana tafe tana sake yaba kyawu da tsarin makarantar acikin zuciyarta,a k’asa take tafiya saboda mai taxi din da ya kawota tun daga gate suka rabu,taji dadin ganin wasu mutum biyu sanye da kayan hidimar k’asa irin nata domin itanma sanye take da uniform dinta riga mai tambarin NYSC da wandonta sai farin hijabi marar girma yayinda ta daura rigar jacket din a kugunta sannan tasha farar safa da farin takalmi wato dai ta zama fully kitted gwadas da ita gwanin ban sha’awa dan kayan sun sake fito da ita sosai. Su ukune kacal yan hidimar k’asar da makarantar ta nema da kanta aturo mata su saboda tana da bukatarsu kamar yadda aka saba,suna zaune itada sauran corpers din su uku suna dan tattauna rayuwar camp wanda ke da alhakin karbarsu yafito daga office din principal yana basu hakuri akan bata musu lokacin da ya danyi,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button