MIJIN MATACCIYA 1-END

MIJIN MATACCIYA Page 1 to 10

Kamar daga sama tana tsaka da bincika handbag dinta domin ciro biro da kuma posting letter dinta taji an rungumeta ta baya juyawar da zatayi taga wani kyakkyawan yaro mai mutukar kyau da daukar hankali,

“Momy…. momy uncle yace min kin mutu…. Momy dama baki mutu ba? Kizo muje wurin daddy….”

Daure mata kai maganganun yaron sukayi wanda har saida ta sake kura masa ido ta kalleshi,farine sol yaron sanye cikin uniform dinshi tsaftacacce yasha stocking ga suma akanshi antaje masa ita tayi kyau gwanin burgewa,tana kokarin yi masa magana chioma taja hannunta sakamakon kiran da senior master yayi musu nan ta wuce office din senior master batare da ta kara bi ta kan yaronba,yana kokarin binta shi kuma principal yafito nan ya rakashi class da kanshi…………鉁嶏笍

*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎

 漏锔? *HASKE WRITERS ASSOCIATION.*

  _(Home of expert & perfect writers)_

*D’AND’ANO…..*

*MIJIN MATACCIYA…!*馃挒馃挒

  *_NA_*

*_UMMI A’ISHA_*

*Wattpad:-ummishatu*

亘爻賲 丕賱賱賴 丕賱乇丨賲賳 丕賱乇丨賷賲.

_*Har yanzu yan shidan haske masu dauke da fararen alqaluma na cigaba da kawo muku hazikan littattafai guda shida reras masu dumi da sanyi wadanda suka hadar da Gidan rina,hayatuddin,izzata,Da ciwo a zuciyata,tana k’asa tana dabo da kuma Burin zuciya ta,bugu da kari zaku samu wadannan dadadan labaran akan farashi mai sauki daidai da aljihunku naira 500 kacal,burin haske akoda yaushe shine ta saku dariya,maza garzaya ki nemi naki domin da abaka labari ai gara ka bayar,haske maganin duhu.*_

    *4*

     ~~~Koda tafito daga office din senior master bayan yagama accepting dinsu bata ga wannan yaron ba na dazu amma kuma maganganun yaron nata kai kawo acikin kwakwalwarta musamman ma maganar da yayi da yanda yazo ya riketa kamar dama can yasanta,

Da tunanin yaron da bata san ko waye ba tabar makarantar ta nufi zonal office domin taje tayi documentation zuwa gobe kuma sai ta nufi gida kanon dabo domin anbasu hutun sati biyu kowa yaje gida ya kintso sai yadawo da shirin zama,duk da bata son koyarwa kuma bata sha’awarta amma wannan kam tana jin zataji dadin aiki dasu domin makarantar ta azo agani ce kuma class biyu kacal aka bata wato JSS 2 da JSS 3 inda zata rinka koyar dasu darasin turanci dama abinda ta karanta kenan wato BSC English.

Aranar ta gama harhada kayanta domin da safe sammako take son yi zuwa gida bata son takai rana ahanya,mujahid kuwa kamar sun shekara basu ga juna ba yadda yabi ya rikice mata ya dameta da waya ba dare ba rana yana tambayar yaushe zata tafi idan babu dama shifa sai yazo da kanshi dan yaganta. Sassafe ta fita ta samu taxi yakaita tasha inda zata shiga motar kano kuma cikin nasara tana zuwa motar ta cika dama mutum daya ake jira babu bata lokaci suka dauki hanyar kanon dabo tumbin giwa.

***

  A guje yashiga cikin babban falon gidan yana kiran “Daddy…. Uncle….. Papa…”

“Kai Aryan menene haka kake gudu sai ka yanke jiki ka fadi ko?…”

“Umma Ina Daddy na?”

Dariya umma barira tayi ta mika hannu ta jawoshi jikinta,

“Banda abinka dan jikalle na ina zaka samu ganin babanka yanzu? Tun fa kafin ka tashi daga bacci yafita yace zaije waccan kasar arnan ni banma rike sunan garin ba,ai ko zai shigo gidan nan to ba yanzu ba…., Maza muje acire kaya ayi wanka azo aci abinci ayi shirin islamiyya malam yana nan zuwa”

Bata fuska yayi kamar zai saka kuka jin abinda umma barira tace,shi Daddyn sa yake son gani,shi yake son fadawa abinda yagani yau,da gudu ya shige dakinsa ya dauki kantamemiyar wayarshi ya zauna akan gado yana neman layin baban nashi amma bai samu ba ahaka umma barira tazo ta iskeshi nan ta karbe wayar ta ajiye asama sannan tajashi zuwa toilet tayi masa wanka ta shiryashi sai rakwarkwabe fuska yake yi irin baya so dinnan.

Misalin karfe 1 na dare ya shigo gidan tare da mukarrabansa, direct sashensa yashiga yayi wanka yasaka kayan baccinshi masu silbi riga da wando maroon colour,ga abinci nan akan table kala daban daban wanda duk aciki baya jin akwai wanda zai iya ci, da kanshi yashiga kitchen ya hada coffee sannan yafita ya nufi dakin Aryan,

A gefen gadon Aryan din ya zauna yana dan kurbar coffee din dake hannunshi yana yi yana nazarin d’akin,ga littattafai nan acan k’asa kan center carpet da alama home work yayi yagama kuma shine ba adebe littattafan ba yabarsu awurin,

Da kanshi ya tattarasu yasaka masa cikin school bag dinshi sannan yasake komawa gefenshi ya zauna tare da kunna yar karamar fitilar dake girke gefen gadon Aryan wato bedside lamp.

Cikin magagin bacci yaron yafarka ganin Khalil zaune kusa dashi yasashi kokarin tashi zaune,mayar dashi Khalil yayi ya kwantar tare da dan rungumoshi jikinsa cikin sanyin murya yana fadin,

“Koma kayi baccinka Aryan…., Nazo ne inganka dama,yi bacci kaji yaron kirki”

“Daddy naganta yau….. Kace min ta mutu ashe bata mutu ba Allah naganta”

Duk a tunanin Khalil magagin bacci ne yasa Aryan wadannan surutan na shirme shiyasa yayi gaggawar dakatar dashi ta hanyar fadin,

“Shhhhhh,Nace kayi bacci ko? Kar nasake jin bakinka awurin”

Maida idanuwanshi yayi ya rufe yana motsa baki alamun yana son yin magana amma babu damar yi,shafar kanshi Khalil yafara yi tun daga sumarshi har zuwa fuskarshi alamar so da kulawa mintuna kadan yasake komawa bacci,sai da yaga yayi nisa acikin baccin sannan yayi masa addu’a ya shafe masa jikinsa dashi sannan yakashe masa bed side lamp din da ya kunna yatashi ya fita bayan ya lullube shi ya rufe masa kofar dakin,

Bedroom ya wuce direct ya nemi wuri ya zauna saman kujerar dake can girke gefe daya da center table a gabanta,lumshe idanuwanshi yayi take tunanin da yasaba bijiro masa ya fara bijirowa kwakwalwarshi kamar koda yaushe wato tunanin matarshi Ramlat margayiya,

“Allah sarki Ramlat kin tafi kin barmu da kewarki da tunanin ki da kaunarki da kuma begenki da kishirwar ganinki….. Sai dai kash nasan bazan sake ganinki ba sai a darus salam,Allah ya jikanki,yaron mu ma da bai sanki ba kullum cikin mafarkinki da begenki yake….”

Daurewa yayi ya hadiye hawayen dake barazanar zubo masa,ahankali ya jingina da jikin kujerar ya kwanta sannan ya lumshe idanuwanshi yana tunani aranshi. Tsawon mintuna masu yawa ya dauka yana tunanin daga karshe dai ya tashi yashiga bathroom duk zufa ta jikeshi tamkar yana gaban wuta,ruwan sanyi ya sakarwa kansa bayan ya kunna na’urar dake bada ruwa. Ruwa yayita kwararawa kansa sai da yaji dan dama dama sannan yafito bayan ya daura alawala,

Wani kayan yasake sakawa sannan ya tsaya gaban mahaliccinsa kamar yanda yasaba akoda yaushe,sallah yayita yi har karfe 3 na dare tayi sai lokacin ya kwanta bacci amma kuma baccin ya gagreshi sai tunani dake ta addabar ruhinsa daga karshe dai yayi nasara baccin ya daukeshi bashi ya farka ba sai asubah. Bacci yasake komawa bayan yayi sallar asubah,yana cikin bacci yaji Aryan yana tashinsa,

“Daddy kace min mommy na ta mutu kuma jiya naganta a school….. Papa naga mommy jiya katashi kaji…”

Cike da bacci a idonshi ya bude idanuwansa yatashi zaune yana kallon Aryan wanda ke sanye cikin uniform din makaranta sai kamshin turaren silver boy yake yi  idanuwanshi sunsha kwalli baki, murmushi Khalil yayi sannan yajawoshi jikinsa ya rungume,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button