MIJIN MATACCIYA Page 1 to 10

“Good morning lovely son….”
“Daddy naga mommy jiya a….”
“Mu fara gaisawa first sai ka fada min,ko baza ka gaida ni ba yau?”
“No Daddy zan gaida ka, Good morning”
“Morning my love,how was your night? Wa kace kagani jiya?”
“Uncle mommy na mana wadda kake nuna min a hoto har kace min ta mutu lokacin da za a haifeni…”
Dan jimm Khalil yayi yana nazarin maganar da Aryan yafada,lumshe idanuwanshi yayi ya shafi sumar Aryan,
“To naji Aryan…ai idan aka mutu ba a dawowa ita kuma mommy dinka ta mutu”
Bude baki Aryan yayi zai sake magana Khalil ya dakatar dashi sakamakon kaiwar da idonshi yayi kan agogon dake ajiye kan bed side drawer,karfe 7:40 agogon ya nuna,
“Aryan ya isa maza jeka ka tafi school kaga ka kusa makara”
Kiss yayi ma yaron a kumatu sannan ya saukar dashi daga kan gadon yana tambayar shi yaci abinci? Daga masa kai yayi alamar ehh,
“Me kaci?” Yasake tambayarshi yana son kawar da damuwar dake saman fuskar yaron,
“Potatoes smiley & egg muffin”
“Good boy,umma ta hada maka da chocolate ko?”
Kai ya daga masa,kumatunshi yaja sannan ya rakashi ya koma ya kwanta bayan ya rufe kofar d’akin nashi,wani baccin yake son yi amma yasan ba mai yuyuwa bane domin yau yanada commitments da yawa gashi yana son ya je gombe ayau yadawo duk da dama yasaba hakan, hakura da baccin yayi yatashi yayi wanka ya shirya cikin fararen kaya yafita dama already table ashirye yake amma iya ruwan tea kadai ya iya sha yafita yaje ya gaida umma barira daga nan yafita office,a office dinma babu abinda yaci duk da ankawo abinci conference room din nasu,bashi yabar office ba sai 6 na yamma wato dab da magriba,daga can wani uzurin yasake wucewa bai fito ba sai misalin karfe 8 da kusan rabi kai tsaye kuma gobe suka nufa.
Lokacin da yashiga family house dinsu a gombe tuni wasu ma har sunyi bacci agidan amma dai hajiya Zaitun wato mahaifiyar su bata kai ga yin baccin ba hakama sauran yanmatan gidan duk suna tare a falonta suna hira,
Zama yayi agefen yanmatan gidan wato mufida da zarah da Sarah wadanda duk yan riko ne hajiya ke rikesu amma ita Zaid ne dan autanta,
“Mufida ku kawo min abinci inci wallahi rabona da abinci har na manta…..”
Tashi suka yi dukansu suka fita ita kuma hajiya tasamu wuri ta zauna tana kallon d’an nata wanda aganinta yanzu duk ya lalace yaki yin kiba amma da ba haka yakeba,
“To ba dole kayita zama da yunwa ba mu’azzam tunda ka ki yin aure ka zabi yin rayuwa kai kadai babu mace… Yanzu da kana da aure yaushe matarka zata barka da yunwa wuni guda…”
Bai kai ga yin magana ba su mufida suka shigo kowaccensu rike da food flask,tuwon shinkafa suka kawo masa miyar taushe sai gasasshen nama da kunun aya mai sanyi wanda yaji kwakwa da madara da dabino sosai,saida yaran suka fita sannan ya kalli hajiya bayan yafara kwasar girkin dake gabansa,
“Wallahi hajiya ba rashin aure ne ke hanani cin abinci ba, lokacin cin abincin ne ma babu kwata kwata, rabona da gida fa tun karfe 8 nasafe ahakanma dan dai ina daurewa ne bana son yin nesa da Aryan amma da wallahi sai inyi kwana biyu banje gidanba…., Ni yanzu ma banida lokacin aurenne gaba daya”
“To koma dai yaya ne ai gara ace kana da matar akan ace babu Khalil,kai kaine babba kuma kana nema ka zama babban kwabo…… Ko tafiye tafiyen k’asashen wajen nan da kake yi acan kake aikata son ranka?”
Cak ya tsaya daga cin abincin da yake yi sannan cikin sanyin murya yace,
“Wallahi tallahi hajiya ni harkokin aikina ke fitar dani waje bawai wani abuba,haba hajiya ai ko dan Ramlat bazan iya aikata mummunan laifi kwatankwacin wannan ba…”
“Nima bance kana aikatawa ba amma dai yadace kayiwa kanka fada,mutum ya radi kansa tun kafin duniya ta radeshi, mutane suna ganin kana da kudi da komai na rayuwa amma baka da mata to gani zasuyi kamar wani abu kake aikatawa agefe…”
“Hajiya wallahi duk lokacin da kika yimin maganar auren nan jinina ne yake hawa saboda bana sonta…”
“Ai shikenan,to Lubnah ta haihu yau da safe ta samu yarta mace,sai ka samu lokaci kaje kayi mata barka”
“To insha Allah, Allah yaraya,zan dawo inyi mata barka idan nasamu lokaci, Ina zaid kuma”
“Ai yatafi Abuja tunda rana,baku hadu bane?”
“Bamu haduba ai rabona da gidan tun 8 nasafe”
Hira ya zauna suka sha da hajiya sosai kai idan ba sani kayi ba sai kace agarin zai kwana,karfe 1 da yan mintuna suka kama hanyar Abuja,
Lokacin da yashiga part dinsa a mutukar wahale yake ga gajiya ga kuma damuwar dake addabar mararsa,cire rigar jikinshi yayi yarage daga shi sai iya singilet da dogon wando,wayarshi ya dauka ya kira number nura PA,mintuna kadan sai ga nuran yashigo,
Cikin mawuyacin hali ya kalli nura, “Nura ina zaka samo min kanwa ko lemon tsami?”
“Ranka yadade kanwa kuma? A wannan daren? Ai yanzu babu inda za asamu kanwa acikin garin Abuja,dama dama lemon tsamin ma”
“Je kasamo min lemon tsamin”
Sake gyara kwanciyar shi yayi bayan nura yafita yana dafe da mararsa wacce ke murda masa wannan yana daya daga cikin dalilin da yasa baya son yaci abinci ya koshi domin duk ranar da ya koshi to sai ahankali…….鉁嶏笍
*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎
8/14/20, 10:06 AM – Ummi Tandama: 漏锔? *HASKE WRITERS ASSOCIATION.*
_(Home of expert & perfect writers)_
*D’AND’ANO….*
*MIJIN MATACCIYA….*馃挒馃挒
*_NA_*
*_UMMI A’ISHA_*
*Wattpad:-ummishatu*
亘爻賲 丕賱賱賴 丕賱乇丨賲賳 丕賱乇丨賷賲
*Alqaluma shida daga k’ungiyar haske na nan na cigaba da baje kolin basirarsu cikin farashi mai sauki daidai da aljihunku, akan naira dari biyar kacal zaku samu labarai guda shida cis wadanda suka hadar da Gidan rina, Hayatuddin, Izzata,Burin zuciya,Tana k’asa tana dabo,sai kuma Da ciwo a zuciyata,karku bari abaku labari,burin haske gamsar daku cikin nishadi da farin ciki.*
*5*
~~~*T* amkar zaiyi kuka haka ya zama kwakkwaran motsi yana neman ya gagareshi,yana baje saman Rug din dake shimfide tsakiyar falonshi yana shan sanyayyiyar iskar _air condition_ din da ta wadata falon da sanyi marar karfi wanda bazai cutar da jiki ba,
Juyi yake tayi shi kadai bayan ya tasa kansa da daya daga cikin pillows din dake kan kujerun falon sannan ga wani pillow din guda daya shima ya saka kasan kafafunshi,
Tsaki yaja yakuma karawa, yayi tsaki awurin yafi sau 30 saboda bacin rai,
“Mtswww shima nura yaje ya wani nemi wuri ya zauna kamar an aiki bawa garinsu…..mtsawww duk abinda mutum bazaiyi da kansa ba ai dama wahala gareshi dan sai abinda yagani kawai”
Juyi yayi yakoma kan damtsen hannunshi na dama dayan hannun kuma na kan mararsa,
Ahaka ya kwashe fiyeda mintuna 20 sai lokacin nura yabude kofa yashigo yana fadin,
“Tuba nake yallabai….wallahi ba asamo anan kusa bane amma dai gashi andace”
Tashi zaune yayi dakyar idonshi a lumshe ya karba kawai batare da yace ko uffan ba,
Har nura yajuya zai fita ya dakatar dashi ta hanyar fadin,
“Bani wuka a kitchen….”
“To yallabai” fita nura yayi yashiga kitchen yaje kan kitchen wire ya ciro daya daga cikin wukaken dake jere akai yakoma ya kai masa lokacin kuma yana jingine da jikin kujera sai faman ajiyar numfashi yake yi,
Karbar wukar yayi shi kuma nura yajuya yafita. Lemon tsamin ya yanyanka wurin guda uku take ya matse su abakinsa ya shanye yana mai yamutsa fuska saboda tsami,tamkar abin shiri cikin mintuna kadan yajishi garau ya dawo cikin nutsuwarsa, bedroom dinshi yawuce yaje yayi wanka yasa kayan bacci sannan ya fita zuwa dakin Aryan,shi kadai yasamu yana kwance yana bacci bayan ya gama game domin ga ga game dinnan na tayi ko kashewa baiyi ba, sannan ga text books dinshi nan suma bisa saman gadon,