MIJIN MATACCIYA Page 1 to 10

Sai da ya kintsa masa komai sannan yayi masa kiss a kumatu yafita. Bedroom dinshi ya shiga ya kwanta bayan yayi shafa’i da wutri domin yau kam bacci yakeji da gaske bada wasa ba saboda jiya bai samu bacci ba yanda ya kamata kuma yau da safe ma haka,duk da gobe babu aiki ana yin public holiday amma shi yana da tarin ayyuka wanda dole sai ya fita yaje ya gabatar dasu, pic din Ramlat ya kalla sannan ya kwata ya lumshe idanuwansa bayan yayi addu’ar bacci.
Washe gari da safe asubanci yayi yafita daga gidan tun kafin mutanen gidan su tashi, shiyasa lokacin da Aryan ya tashi kuka yafara yi bayan yaje bedroom din Khalil bai ganshi ba shi ina Daddynshi? Sai da Zaid yafito yayi masa wayo sannan ya hakura daga karshe Zaid din ya daukeshi suka fita tunda yau babu makaranta.
Duk da Khalil ya fadawa Aryan cewa ya daina maganar yaga mommynshi a makaranta ba ita bace ita ta rasu bai hakura ba kullum cikin maganar yake kuma idan yaje makaranta yakan duba gaban staff room wai ko zai ganta, kullum sai yaduba wurin amma bai sake ganinta ba, Khalil kuwa har yagaji da maganar nan gashi da zarar Aryan yayi masa maganar sai yaji damuwar sa da raunin dake cikin zuciyarsa sun dawo sabo fill. Yau ma da suke zaune a falonshi shida Aryan da Zaid Aryan yana game a wayarshi sai yasaka pause yajuya ya kalli Khalil wanda ke magana da zaid yana cewa,
“Ai Zaid mutane ne kadai ke ganin kamar muna jin dadi amma wallahi azahirin gaskiya wahala muke sha,sam fa mutum baida hutu sannan baida lokacin kansa kana gani kai kanka tunda kazo bamu haduba bamu zauna dakai ba sai yau…. Kai ai wannan rayuwa tana da wahala”
“Daddy….. Mommy”
Jin abinda Aryan yafada yasashi juyawa ya kalleshi shi wallahi yasoma gajiya da wannan maganar mommy din domin bata masa rai ma take yi,
“Daddy zamuje da mommy new york?”
“Ban saniba,ba nafada maka idan kagama exams dinka zan kai ka can ba? Kamin shiru da bakinka”
Shiru yayi ya kama bakinshi kamar yadda Khalil yasaba sashi idan ya hanashi surutu sai yasashi ya kama bakinshi.
***
A bangaren Hanan kuwa cike da farin ciki da murna ta isa gida tana ta dokin ganin mutanen gida kamar irin ta shekara dinnan bata gansu ba domin dama ita bata saba yin tafiya taje wani wurin tayi kwanaki ba shiyasa wannan dan sati uku zuwa hudun da tayi take ganin kamar watanni ne tayi batare da taga yan gida ba.
Tun aranar mujahid yazo domin shima cike yake da dokin ganinta,
Kamar yadda ta kawowa kowa dake gidan tsarabar turare shima mujahid haka ta kawo masa turaren secret man,
Tallafe kumatunsa yayi yana kallonsa saboda azahirin gaskiya tayi bala’in kyau domin da alama weather din garin Abuja ta karbi fatar jikinta tayi wani luwai luwai sai sheki take yi tana kyalli,
“Wai yallabai menene ka tisani agaba kana kallona kamar yau kafara ganina?”
Murmushi mujahid yayi sannan ya janye idanuwanshi daga kanta ya mayar kan sitiyarin motarshi,
“Wallahi kinyi kyau ba karya,gaskiya Abuja ta karbeki,ko can zamu zauna ne?”
Yar dariya tayi sannan ta shafi fuskarta,
“Wai haka ma su yaya shamsu suka ce,wai nayi kyau kamar bani ba yar dukununun fatata duk ta haska tayi kyau ashe da gaske ne….”
“Allah dagaske ne kinyi kyau amarya ta kamar irin kin fara cin amarci dinnan…”
“Uhmmm zaka fara ko,kai a kullum baka da magana sai ta aure”
“To bashi ne araina ba? Ai dole intayi miki maganarsa ko zaki ji tausayina ki bani dama”
“To nidai yanzu gobe kazo ka kaini gidan anty salaha inje mu gaisa inbata labarin Abuja”
“Duk yanda kikace haka za ayi da girman kujerarki….”
Cikin sati biyun da tayi a kano ta harhada kayanta jimilla gaba daya wadanda zata tafi dasu sannan ta sissiya wadanda take da bukata,ranar da zata tafi yaya shamsu ne da mujahid suka kaita basu suka baro garin abuja ba sai magriba yayinda ita kuma ta zauna zaman shirya kayanta a daya daga cikin dakunan dake cikin quarters din makarantar domin yanzu tabar Lodge hukumar makarantar bright future tabasu masauki a quarters din malamai wanda ke dauke da komai na more rayuwa,
Wallahi sosai abun ya burgeta kuma yayi mata dadi haba zatayi service a dadi komai yana zuwar mata cikin sauki duk ma dai da term din yakare domin exams za afara to amma yazama dole su kasance suna kusa.
Washe gari ashraf ne ya tadata daga bacci wai zaizo yaganta kafin yabar Abuja,tana fitowa daga wanka yakaraso kaya kadai tasa tafita ta sameshi waje yana jiranta,suna tsaye dashi suna hira motar Khalil tashiga cikin makarantar inda zasu ajiye Aryan sannan yawuce kaduna shida nura PA,duk da ba akusa suke ba ahakan Aryan ya hangota,kama hannun Khalil yayi yace,
“Papa kalli mommy can….”
Khalil bai kulashi ba ya saka hannu cikin aljihunsa ya ciro wayarshi ya soma latse latse har suka ajiye Aryan bai kulashi ba sai babbata rai Aryan din ketayi,
Tun daga ranar walwalar Aryan ta ragu ahaka har suka fara exams ita kuwa Hanan bama sosai take shiga cikin makarantar ba saboda jarabawa akeyi aikin da ake basu kadanne ba wani aiki sukeyi sosai ba amma dai suna yin nasu daidai gwargado,ana yin hutu ta tattara nata inata ta nufi gida kanon dabo.
***
Tunda aka gama exams Aryan ke faman yiwa Khalil rigima akan maganar mommynshi, Aryan irin yaran nanne da basa mantuwa kai sai ma ka manta da abu shi bai manta ba,
Rarrashinsa Khalil yafara yi yana cemasa,
“Kamanta da maganar mommy dinnan kaji yaron kirki,ana yimuku hutu zan kaika Jos kaga yan uwan mommynka sannan zan kaika gombe wurin hajiya ai zakaje ko? Daga nan zan daukeka mu tafi new york inda zaka kare hutunka gaba daya acan,kullum zamu rinka zuwa central park kana shan ice cream….”
Makale kafada Aryan yayi yana turo baki,
“Ni wurin mommy nake so…”
“Kai….. Shut up…..ba na hanaka wannan maganar ba? Get out of here ko in bugeka,marar jin magana”
Tsawar da Khalil yayi masa ce ta razanashi yafita da gudu yaje ya zauna a falo yana kuka abunka da yaran hutu wadanda basu saba ba take temperature din jikinsa ta sauya kansa yafara ciwo shikenan sai numfashi sama sama,
Shi kuma uban na can dakinshi yagama shiryawa zai fita zai tafi kano ta’aziyar baban wani classmate dinshi,duk atunaninshi Aryan na wurin umma barira,har zai fita ta kofar side dinshi sai yafasa domin bai yiwa umma barira sallama ba,
Ta babban falo yabi acan ya hango Aryan sheme saman carpet yana wani irin abu kamar mai iska,kansa yaje ya dagashi duk hankalinsa atashe,baima tsaya ya saurari fitowar umma barira ba yanufi waje dashi,
Asibiti suka kaishi nan aka fara bashi taimakon gaggawa,shidai a iya saninshi Aryan lafiyayyen yarone bashi da wata lalura sai dai ko boyayyiya wacce bata bayyana ba,
Abinda likita yafada masa ne yayi mutukar girgizashi wai zuciyar Aryan yar mitsitsiya ce sannan dole aguji bacin ran shi adaina hanashi abinda yake so,to ai dama Khalil a iya saninshi abinda Aryan yakeso yake masa dan shi ko fada bai yarda wani yayiwa yaronsa ba,
Aranar da daddare aka sallamesu,tunda suka koma gida yaketa nan nan da Aryan ranar ma tare suka kwana,da zarar yayi masa maganar mommy kuwa sai yace ehh zai nemo masa ita duk inda take,abun har mamaki yabashi saboda irin yanda yaga yaron yanata murna yana farin ciki,shima farin cikin yaji ya samu kansa aciki domin farin cikin Aryan shine nasa, Aryan ya cancanci dukkan soyayyar da ta dace daga gareshi domin yarasa mahaifiyar shi a lokacin da yake tsananin buk’atarta baiji dumin jikinta ba haka kuma bai sha ruwan madarar dake fita daga jikinta ba shiyasa yanzu dole ya zame masa uwa kuma uba dole yasamar masa da dukkan farin cikin da yake buk’ata koda kuwa hakan zaisa shi yarasa nasa farin cikin……鉁嶏笍