MIJIN MATACCIYA Page 1 to 10

*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎
8/14/20, 10:06 AM – Ummi Tandama: 漏锔? *HASKE WRITERS ASSOCIATION.*
_(Home of expert & perfect writers)_
*D’AND’ANO…..*
*MIJIN MATACCIYA….*馃挒馃挒
*_NA_*
*_UMMI A’ISHA_*
*Wattpad:-ummishatu*
亘爻賲 丕賱賱賴 丕賱乇丨賲賳 丕賱乇丨賷賲
*6*
~~~*R* anar hutu Khalil da kansa yakai Aryan makaranta saboda tunda suka tashi daga bacci yaga alamar da rigima Aryan din yatashi dan sai wani tutturo baki yake yi breakfast ma saida lallami yasamu yaci amma da umma barira tayi tayi dashi ya zauna yaci yaki ci daga k’arshe ta kira Khalil awaya,yana kwance yana bacci yaji karar wayar landline ta cika masa kunne wacce ke ajiye saman drawer din gadonshi,dole tasa yatashi ya daga wayar domin yasan daga cikin gidan ake kiransa ko securities ko wani daga cikin jama’ar dake cikin gidan addu’ar shi dai bata wuce Allah yasa ba baki yayi ba da sanyin safiyar nan domin ko wanka baiyi ba,
Muryar umma barira yaji tana cewa,
“Mu’azzam zo kaji da wannan kinibabben yaron naka dan ni bazan iya ba nayi lallashi har nagaji yaki jin lallashina tunda kai kaine ubansa kila zaiji naka…..”
Jin abinda umma barira tace yasashi yin murmushi mai dauke da sauti yasauka daga saman gadon yana kokarin zira silifas dinshi dake ajiye gaban gadon domin tana gama fadar abinda ta fada ta katse layin,
Gaban closet dinshi yaje ya tsaya yacire farar riga armless din dake jikinsa yasaka jallabiya kalar ruwan kasa sannan yafita,
A babban falo yasamesu suna drama umma barira nata tura masa soyayyen dankalin turawa wanda ya wadatu da kwai ga plantain shima agefe da wainar kwai sharba sharba amma yaki ci sannan ga tea dinshi nan a dan karamin cup dinshi,
Umma barira na ganin yashigo ta mike ta nufi cikin falon tabar dining room din tana fadin,
“Khalil wannan yaron naka dan jakar ubane ayita shan kansa amma yana sake botsarewa…..to nidai nayi nawa jeka kaima ka gwada taka sa’ar”
Murmushi Khalil yayi yana kallon Aryan wanda ke zaune saman dining yana ta turo baki,
“Ai ni dama tunda naga har yanzu bai shigo dakina ba nasan da walakin…. Bari naje na bashi abincin…..”
Daga haka yawuce wurin Aryan ya zauna akusa dashi sannan ya dagashi ya dora kan cinyarsa,
“Baba na yau kuma abinci ake yiwa yaji? Uhmmm? Yau fa za abaku hutu amma banga kana murna ba…. Kana da kiwar zuwa school Aryan,nifa when i was young kamarka banyi gardamar zuwa makaranta ba…”
“Papa ni bazan ci wannan ba…”
“To me zaka ci? Fada min maza adafa maka kaci ka tafi school ka karbo report card dinka”
“Noodles….”
“To ai mai saukine bari adafa maka within 5 minutes….”
Tashi yayi yafita ya kira kuku nan da nan kafin wani lokaci ya dafa noodles din mai kunshe da vegetables aciki da kifin gwangwani sannan ga soyayyen kwai akai,
Zama yayi yabashi abaki yaci ya koshi sannan yaje ya kaishi da kansa daga nan ya juyo gida domin kamar koda yaushe yauma yana da inda zaije.
Tunda yafita bai samu dawowa ba sai misalin karfe 10 saura na dare yayi mamaki sosai da yaga wai idon Aryan biyu a wannan lokacin baiyi bacci ba,yana ganinshi ya ruga da gudu ya rungumeshi yana rike da report card dinshi a hannu,daukarshi Khalil yayi yana karbar report card din,fuskarshi ce ta fadada da murmushi da fara’a har yakai bakinshi kan goshin Aryan yayi masa kiss,
“Yaron kirki this time around baka yarda suhail ya kwace maka first position din ba?? Kayi kokari,zan yi maka duk abinda kake so kaji…me kake so?”
Kwantar da kanshi yayi jikin kafadar uban sannan ahankali yace,
“Mommy…”
“To Aryan din Daddy…”
Tare dashi sabe a kafadarshi yawuce bedroom dinshi ya ajiye shi saman gado shi kuma ya fara kokarin rage kayan jikinsa.
Bayan yayi wanka yayi shirin bacci yana zaune saman Rug da Aryan kan cinyarsa yana bacci umma barira ta kira waya tana tambayar ko suna tare da Aryan domin ta shiga dakinsa bata ganshi ba kuma baya wurinta,niyyar tsokanarta yayi yace,
“Umma baya wurina ni nan ni kadai ne”
“To sai ku bazama nemansa domin nima baya tare dani”
“Umma kenan kin ganshi nan yana bacci,hira ma muke yi yayi bacci ya barni…”
“Aima yayi kokari da har kadawo ka sameshi ido biyu shida kafin 8 wani lokacin yayi bacci amma yau ya dan taba baccin rana wuni yayi yana bacci inajin shiyasa baiyi na daren da wuri ba”
“Ai nima nayi mamakin ganin idonshi biyu lokacin da na shigo”
“Ina ruwan mai gida”
Katse wayar yayi yana dariya shi bama dan yayiwa Aryan alkawari ba da ya turasu umarah shida umma barira,babu abinda zaice da ita sai godiya domin tana tsananin kaunar gudan jininsa ko ita ta haifeshi sai haka abinda hajiya mahaifiyar shi zatayi masa shi umma barira take yimasa duk tsawon lokacin nan da ta dauka tare dasu shekara da shekaru bazai iya cewa ga laifinta ba kullum cikin tattalinsu shida yaronsa take. Cikin dakinshi yakai Aryan suka kwana tare,bayan kwana biyu da yiwa su Aryan hutun makaranta Khalil yasa umma barira ta shirya kayanta da na Aryan shima ya shirya nasa suka nufi gombe domin shima ya dauki hutu a office,tun da suka je gomben ma bai zauna ba kullum cikin karbar baki yake da yawon gaishe da yan uwa da abokan arziki,duk wasu dangin hajiyarsu da dangin abbansu sai da yaje ya gaidasu tare da yimusu rabon masu gidan rana,kwanansu uku a gombe ya dauki Aryan suka tafi jos wurin iyayen Ramlat,shi a hotel ya sauka bayan yakai Aryan gidansu Ramlat sai dai kullum yana zuwa gidan domin ya duba Aryan,harga Allah yana jin dadin irin yanda ummi kanwar Ramlat ke kula da Aryan sannan duk itace ke wahala da tiriniyar kaishi gidajen yan uwa,har gobe iyayen Ramlat basu daina kwadayin sake hadashi aure da itaba amma shi bazai taba iya auren ta ba da ace zai iya to da ya aureta ko dan kulawar da take yi da dansa. Kwanansu biyu a garin jos daga can suka wuce Calabar babban birnin jahar cross river domin ya fahimci Aryan yana son yaje yaga yan uwanshi wato yaran Khalid cousin dinshi,kwanansu daya da yini daya adaren ranar suka tashi suka nufi babban birnin new york.
Kamar yadda yasaba duk lokacin da suka tafi hutu shida Aryan yakan samu lokaci sosai ya zauna tare da yaron suyi ta hira yana bashi labaru na ban dariya da nishadi da tatsoniyoyi kala daban daban hakan ba karamin sake kara musu shakuwa da sakin jiki da kusanci yake yi da yaron ba, sannan yakan ware musu lokaci a kullum su fita su zaga gari su je wuraren shakatawa da wurin wasannin yara domin debewa Aryan kewa banda shagunan sayar da kayayyaki da yake kaishi ya siyo masa duk abinda yake so. Wannan karon ma hakance ta faru a k’asar new york,duk inda yadace yakai Aryan yakaishi sannan sun samu lokaci sosai wurin kasancewa da juna,sunsha hotuna har sun gaji dama Khalil yakan tafi da yar karamar camera saboda daukar hotunan tarihi,
Satinsu uku sannan suka fara haramar dawowa,saida suka je babban kantin sayar da kaya dake cikin birnin Khalil ya jibgo masa kayan sawa da takalma dan hatta school bag dinshi da combos da sauran kayan sawarshi duk acan yasiyo masa,
Baiyi wata tsaraba mai yawa ba sai yan abubuwan da ba arasa ba ya sissiya daga nan suka nufo gida Nigeria,a Abuja suka sauka dama tun da Khalil yace gobe zasu dawo umma barira ta shirya ta tafi Abuja dan haka can suka tarar da ita,