MIJIN MATACCIYA 1-END

MIJIN MATACCIYA Page 1 to 10

Daga Aryan tayi ta rungume suna dariya gaba dayansu yana sanye da dark blue din jeans da jar t shirt ta kamfanin polo sai jan takalmi shima na kamfanin polo,yanda yayi wannan shigar shima uban ita yayi sak jeans da t shirt duk irin na Aryan.

Bayan sun dawo sai da sukaje gombe suka gaida hajiya sannan suka juya aranar,ranar Monday Aryan suka koma school shi kuma Khalil yakoma office shikenan yazama busy kullum bashida hutu.

A bangaren Hanan itama ta shirya ta koma Abuja bayan hutu yakare nan kuma akaje aka fara koyar da dalibai babu kama hannun yaro duk sai ta zama busy itama saboda marking din script din dalibai kadai ya isheta shiyasa yanzu bata da lokaci sosai.

Shi kam Khalil Aryan ne ya bi duk ya dameshi da maganar mommy gashi baya samun lokaci sosai amma kullum yaron cikin maganarta yake daga karshe da yagaji sai yatura PA dinsa yace yaje ya binciko masa koma wacece wannan yarinyar da Aryan keta faman magana akanta kullum.

Cikin kwanaki biyu kacal nura yazowa da Khalil amsa lokacin Khalil din yadawo daga bauchi yana dan hutawa acikin falonsa,dan russunawa nura yayi sannan yace,

“Ranka yadade sunanta Sa’adatu mustapha mai jama’a taura,mahaifinta haifaffen garin taura ne,amma yanzu haka suna zaune acikin garin kano a unguwar sabon titi mandawari….”

Dan murmishi Khalil yayi yashafi sumar kanshi sannan yace,

“Ashema ‘yarmu ce,to ai ta kwana gidan sauki,nura kana iya tafiya, nagode”

“Nabarka lafiya yallabai” daga haka yajuya yafita, murmushi Khalil yasake yi akaro na biyu yana jin dadi har can cikin kasan ransa zaiyi surprising Aryan,zai kawo masa Mommy har gida ya ajiye masa ita yayita kallonta hakan ita kadaice mafita. Acikin satin yaje har gombe yasamu hajiya da Abban London da maganar ai kuwa zo kaga murna wurin iyayen nasa musamman ma hajiya da dama tafi kowa matsuwa da damuwar rashin auren nan nasa,washe gari Abba da kansa ba sako ba yashirya ya tafi kanon dabo neman aure,

Da dafarko shi mahaifin Hanan ma yayi zaton ko batan kai akayi amma da Abba yayi masa bayani sai ya fahimta yagane ba batan kai aka yiba,nan yace yabada auren hanan ai ko da ace akwai wani to zai iya hanashi yabawa Khalil bare ma babu,shi ai Khalil nasa ne atakaice dai Abba bai baro kano ba sai da ranar auren Khalil sannan abbanta yace Khalil din yasamu lokaci yaje su gana.

Yan hidimar k’asa kuwa ana can Abuja ana hidimtawa k’asa yanda ya kamata,kullum suna mak’ale da mujahid awaya dawowarta kuwa zuwansa biyu kullum cikin maganar tabari yatura gidansu yake amma ta murje idonta tace sam ita ba yanzu ba. Wata ranar alhamis sukayi waya da abbanta nan yake cemata,

“Uwar masu gida ki daure ki samu kizo acikin weekend dinnan domin inada muhimmiyar magana dake sannan kuma zamu samu bakuncin manyan mutane”

“To Abba insha Allah gobe dama nake son tahowa”

Tunani tai tayi aranta bayan sun gama waya da abba,to ko suwaye manyan bakin da zasuyi kuma oho,ko menene dalilin da yasa Abba yace taje gida oho,ko wacce muhimmiyar magana zasuyi da yace mata zasuyi duk Allah masani amma gaba daya hankalinta yatafi gida kawai so take ta ganta acikin garin kano,aranar taje tayi yar siyayyar kayan marmari domin yin tsaraba dama anyi musu alawee tun ranar Monday,washe gari tun 7 tafita taje tayi signing sannan ta tafi tasha ta hau mota cikin lokaci k’ank’ani mota ta cika fam suka kama hanya…….鉁嶏笍

_Game bukatar biyan kudin wannan book din zai turo naira 200 ta Account number dina 3112877210 Aisha Ibrahim first bank,sai atura shaidar biya ta wannan number din 07044644433 ko kuma atura MTN recharge card zuwa wannan number din 07044644433 sai atura shaidar biya ta the same number da aka tura katin nagode._

*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎

8/14/20, 10:06 AM – Ummi Tandama: 漏锔? *HASKE WRITERS ASSOCIATION.*

   _(Home of expert & perfect writers)_

*D’AND’ANO…..*

*MIJIN MATACCIYA…..*馃挒馃挒

  *_NA_*

*_UMMI A’ISHA_*

*Wattpad-ummishatu*

*Alqaluma shida daga k’ungiyar haske na nan suna cigaba da baje kolin tasu basirar,nemi naka kaima adama dakai cikin farashi mai rahusa.*

*7*

     ***Har motarsu ta isa kano tunani daban daban bai daina kai kawo acikin ranta ba,duk ta kasa samun nutsuwa sai tufkawa da warwarewa take ta faman yi tana son gano dalilin wannan kiran gaggawar da Abba keyi mata wanda abisa dukkan alamu akwai abinda ke faruwa ko kuma yake shirin faruwa.

Ita dai har motarsu tashiga kano ta sauka ta tare mai napep ta shiga zuwa gida zuciyarta bata daina yimata wasi wasi ba,alla alla takeyi taganta agida dan taga abinda ke faruwa shiyasa jiki a sanyaye ta shiga gidan bayan ta sallami mai napep din da ya sauketa,

Mamaye ce kadai tana kwaba fulawar da zatayi dan wanke a kofar kitchen abisa dukkan alamu shima yaya shamsu baya nan,ganin fuskar mamaye awashe sannan kuma asake alamun babu matsalar komai yasata ta danji sanyi acikin ranta,

Kayanta ta shigar cikin daki sannan ta dawo wurin mamaye suka fara gaisawa,

“Mutanen Abuja kinsha hanya kuma kun fito da wuri…”

“Ehh wallahi mamaye tun wurin 7 fa muka fito dan ni ko karyawa ma banyi ba”

“To ai akwai ruwan zafi a flask sai kije kihada shayi kisha”

“To bari insha abisa lalura amma shan shayi da rana ai sai ahankali”

Daga haka ta tashi tawuce falo ta hado tea ta dauko bread ta sake dawowa wurin mamaye. Sai la’asar sannan abbba yadawo lokacin suna zaune da mamaye da yaya shamsu suna hira,

Wurin Abba taje suka gaisa sannan suka dan taba hira kadan har zata tashi abba ya dakatar da ita,

“Uwar masu gida sai kuma kikaji kira ko?”

“Ehh Abba dama nima ina son inzo gidan inganku ai”

“To wani abokina ne kuma aminina ya nemi wata alfarma awurina wadda nikuma bazan iya kin yimasa itaba,ya bukaci inbashi aurenki nikuma bazan iya hanashi ba….”

Jin abinda Abba yace yasata zaro ido tare da jin firgici gamida gagarumar faduwar gaba,bata san lokacin da tace,

“Abba abokin ka?”

“Ehh uwar masu gida… abokina amma nasan insha Allah zaki sameshi kamar yadda kike so,zaki ji dadin kasancewar shi mijinki, matarsa ce ta mutu a lokacin haihuwa,dansu daya kacal wanda ta mutu ta bari….”

Kamar wacce aka zarewa laka ajikinta haka taji bata san lokacin da hawaye ya ziraro ta idanuwanta ba,

“Abba kuma shine da kansa yaganni yace yana sona?”

“Shine Hanan,shi yaganki anan Abuja,acan yake da zama minister ne,shine ministern yada labarai,matasa,raya al’adu da wasanni,yanemi da inbashi aurenki kuma na bashi nan da sati uku za adaura muku aure,sai kije kifara shirye shiryen da duk ya kamata…. Allah yayi miki albarka”

Bata iya cewa komai ba ta tashi tafita idanuwanta cike da hawaye tausayin kanta da kuma mujahid take yi,yanzu me zata cewa mujahid? Da wacce kalma zata dosheshi har tayi masa bayani? Da wacce kalma yadace tayi amfani wurin sanar dashi wannan bakin labari?

Daga mamaye har yaya shamsu babu wanda tayiwa magana tawuce daki taje ta kwanta tasoma shakar kuka,duk tsawon shekarun da suka dauka tare da mujahid bata taba jin sonshi ba sai yau da taji zata rasashi,wata zazzafar soyayyar shi take jin tana shigarta babu k’akk’autawa,

Tajima tana kuka kafin mamaye tashigo ta zauna gefenta tasoma bata baki,

“Hanan kiyi shiru wannan kukan baida wani amfani,kiyi shiru ki mika al’amuranki ga Allah ki nemi alkhairinsa da kuma albarka acikin aurenki….”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button