MIJIN MATACCIYA Page 11 to 20

Shinkafar ta diba a plate tafara ci tana hadawa da gasasshen kifin,wato daga safe zuwa yanzu shine har aka kara zuba wasu abubuwan cikin show glass dinnan domin da safe iya dishes ne da ire irensu aciki amma yanzu harda kayan hada shayi irinsu madara, corn flakes, golden moon,da biskit kala kala wanda ake hadasu da tea asha,
Tana daf da gamawa taji karar kararrawa abakin kofar falon wato door bell,tana yunkurin tashi aka sake dannawa,mikewa tayi ta nufi bakin kofar dan ganin waye dukda babu hijabi ko mayafi ajikinta amma tasan kayan jikinta basu da matsala……………..鉁嶐煆?
*_Ummi A’isha_*馃憣馃徎
8/14/20, 10:07 AM – Ummi Tandama: *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.*
*15*
***Cikin nutsuwa take takawa har ta isa bakin kofar daidai lokacin aka sake dannawa, budewa tayi ta dan ja baya,umma barira ce da nura PA yana dauke da Aryan a kafadarshi da alama ma Aryan dinne ke ta faman daddanna door bell din,
Kasancewar ita ba saninsu tayiba yasa ta dan saki fuska tana yimusu sannu da zuwa, Aryan kuwa sauka yayi daga hannun PA ya ruga jikinta ya rungume ta, bata da zabin da yawuce itama ta rungumeshi din amma bawai dan son ranta ba,
Kaya aka rinka shigowa dashi wanda yake mallakin su umma bariran da Aryan,sai lokacin ta fahimci ko suwaye domin dama taji Zaid yana waya yana fadar cewa zasu dawo gidan da zarar sun kammala shirya kayansu nan suka sake sabuwar gaisuwa da umma barira ta tsugunna har kasa ta gaida umman,
Suna zaune a falo PA nata shigarwa da umma kayanta cikin daya daga cikin bedroom din dake kasa bayan angama kaiwa Aryan nasa dake sama,
Sosai take ankare da yaron wato Aryan wanda yayi dare dare kan cinyar umma barira sai game din Angry run yake ta faman yi awata waya hadaddiya wacce bata da masaniyar ko ta waye,
“Umma kema akai miki kayanki upstairs…..” Taji Aryan din yafada yana turo baki alamun shagwaba,
“A’a Aryan ni ina kasa yaushe zan hau sama intakura muku”
Jin abinda tace yayi wurgi da wayar yasoma rigima shi ala dole itama umma sai ta hau sama,wani irin haushin yaron Hanan keji gaba daya anbi anbata yaro an sangartashi dan kawai uwarshi ta mutu? Yaro sai tabarar tsiya duk anbarshi babu gwaba?
Dan karamin tsaki taja tana kallonsu umma nata kokarin rarrashinsa amma yana ta botsarewa,cigaba tayi da kallon dramar tasu amma fa yaron akwai masifar kyau ko tantama batayi tasan mahaifiyar shi ya iyo dan wallahi kamar dan larabawa yake ko turawa,
Dakyar umma ta rarrasheshi ya hakura ita dai Hanan haushi ne ya hanata magana domin dama haushinsa take ji tunda ta sanadiyyar shi ne ubansa yaje ya aurota har da su kafa mata dokoki akansa. Har lokacin sallar magriba yayi suna babban falon kasa zaune lokaci zuwa lokaci suna dan taba hira shikuma Aryan na kwance yayi pillow da cinyar umma yanata game dinshi,ganin lokacin salla na neman wucewa yasa umma barira fadin,
“To kai sulaimanu dagani inje daki inyi salla karka karasa min k’afar”
Mikewa umma tayi domin shiga daki shikuma Aryan yana cewa,
“Ni bazan bikiba mommy zanbi”
“Ehh kuje umma ta gaida Aysha” umma tafada tana wucewa daki,ita kam Hanan bata kulashi ba da taga zai biyota ma harara ta zabga masa jikinsa yana rawa yabi bayan umma yafasa binta,sama ta hau tana ta faman mita,
“Haka kawai kunbi duk kun bata yaro kamar shi kadaine maraya mtswwww nidai wallahi bazanyi tolerating wannan nonsense dinba”
Bedroom dinta ta shiga tayi alwala tafito aranta tana cewa idan uban naka yaji haushi ya sallame ni inbar muku gidanku sai yaci gaba da lallaba ka yana tattalinka. Aryan kuwa da kuka yashiga dakin umma wacce ke kan rug din salla tana yi,shi tunda yafado duniya bai san wani abu waishi takura ko kiyayya ba,kowa cikin nuna masa so yake da kauna ko harara bai santa ba sai yau da yaga Hanan tayi masa shiyasa tun daga lokacin yafara jin tsoronta,saida umma ta idar da salla sannan tasoma rarrashinsa daga karshe taci nasara bayan tace masa suje tabashi tuwo yaci dama akwai shi da son tuwo yana mutukar kaunar tuwo yaron yafi sonshi fiyeda komai adangin cima,
Saida umma ta sake masa kayan jikinsa daga jeans da t shirt zuwa riga armless da gajeren wando sannan suka fita,akasa suka zauna bayan umma ta zubo tuwon nan tafara bashi abaki yana ci tana hada masa da ruwa amma shi hankalinsa gaba daya yana kan wayar dake hannunshi,ahaka Hanan ta sauko ta samesu tana sanye da babban hijabi hannunta rike da casbaha tana ja ahankali,zama tayi akan kujera tana kallonsu kamar tasamu tv domin sai umma ta dan rarrashesa sannan yake yarda yana karbar tuwon,
Kamar a mafarki kuma sai taga yana murna yana dariya yana fadin,
“Papa….. Daddy”
“Yes son how you? Me kaka cine haka?” Khalil yafada wanda ke kwance kan gado yana kallon Aryan da umma agefenshi ta video call din da yakira,
“Daddy tuwo umma take bani…. Kuma da dad’i”
Dariya Khalil yayi yana kallon fuskar Aryan Sosai,
“Boy meyasa kayi kuka? Waye ya taba min kai?”
Kafin Aryan yayi magana umma tayi karaf tace, “Rigimar tashi ce kawai ta motsa kasan halin mutumin idan yan rikicin suna kusa,muma ai gamu asabon wuri Masha Allah wallahi wuri yayi kyau mu’azzam Allah yasanya albarka”
Duk abubuwan da akeyi Hanan na saman kujera tana kallo amma ita bata jiyo maganar Khalil din tunda ba akusa take ba. Sunfi mintuna talatin suna wannan wayar dan har Hanan ta ci abinci tagama tawuce sama tabarsu har lokacin Aryan yanata hira da Abban nashi, lallai Allah kadai yasan irin son da wannan mutumin ke yiwa Aryan gaba daya parlors din gidan hotunan yaronne akakkafe wanda sam da bata lura dasu ba kun san ance hankali shine gani ita dai dakinta ta koma tayi sallar ishah tayi wanka tayi shirin bacci tabi lafiyar gado.
Washe gari kasancewar da akwai makaranta kafin ma tafito tuni har anshirya Aryan antafi kaishi shiyasa lokacin da ta fito iya umma kadai ta tarar tana karyawa,gaisheta tayi sannan itama tawuce kan table tana ta mamakin wai su ma’aikatan gidan nan ba aganinsu ne sai dai kawai kafito ka tarar da aiki angama? Dan hatta shara dasu mopping duk anyi ansaka turaren kamsasa daki sai faman tashi yake,bayan tagama takoma wurin umma anan ma take tambayar ta ma’aikatan gidan nan umma tafara bata labari ai su da asubah suke aikinsu suyi su gama,sun jima tare da umma suna shan hira wanda hakan ba karamin debe mata kewa yayi ba,suna tare Khalil yakira umma suka gaisa cikin fara’a umma ke cemasa mutumin ai yatafi makaranta sai anjima za aje adaukoshi,tana jin lokacin da umman ke cemasa amarya fa ko abata waya? Sai yace a’a itama zai kirata ita kuwa Hanan tasan ba kiran nata zaiyi ba shiyasa da umma ta fada mata acikin zuciyarta tace yarike kiransa itama ba nema take yiba. Sun jima tare da umma suna hira daga daren jiya izuwa yau kadai taji ta saki jiki da matar kuma har sabo yashiga tsakaninsu kamar dama can sun dade tare,wurin azahar ta koma sama tayi wanka tayi salla ta dan kwanta ita fa gaba daya ta kosa hutunta yakare ta koma school saboda bazata iya wannan kwanciyar ba ace mutum babu abinda zaiyi sai dai yaci ya kwanta? Tunda fa tazo gidan nan babu abinda take yi daga gyaran d’akinta sai gyaran falo da toilet shikenan aikin sai kwanciya alhali ita bata saba wannan rayuwar ba,ita tasaba ta wuni tana aiki tana kujiba kujiba takai can ta kawo nan amma yanzu wani lokaci yazo mata wanda bata duk wadannan abubuwan.