MIJIN MATACCIYA 1-END

MIJIN MATACCIYA Page 11 to 20

K’arfe 2 na rana tasake sauka k’asa lokacin tuni har Aryan yadawo daga makaranta PA yaje ya daukoshi yana zaune a falo daga shi sai gajeren wando duk uniform din nashi da takalmi da school bag duk ya zubarsu anan, harararshi tayi bayan ta zauna nan yashiga taitayinshi yadaina abinda ta sameshi yana yi wato baza kayan wasanshi irin fruits din roba dinnan na wasan yara harda su wuka wacce ake yanyankawa to su ta iskeshi yana barbazawa duk yana neman hargitsa falon,kalar tausayi yayi ya rakube jikin kujera yana wasa da wayarshi,

Jin motsi a dining area yasata waiwayawa nan taga kuku yana shirya abinci dama tunda ta sauko take jin kamshi ya cika falon,yau dai taga ma’aikacin gidan guda daya, muryar kukun tajiyo yana gaidata nan ta amsa cikin harshen turanci domin bai iya hausa ba sunanshi John,tana ji yanata jan Aryan da wasa amma baiyi magana ba Aryan din bayan kuma surutu ne da yaron kamar aku,

Tana can tana faman kallon yanda john ke shirya table cikin kwarewa da sanin makamar aiki Khalil yakira Aryan kuri yayi yana kallon yaron saboda sam babu fara’a atare dashi fuskarshi kamar zaiyi kuka tambayar shi yafara yi wai waye ya tabashi? Ko yunwa yake ji? Yaci abinci? Ina umma barira? 

Duk wadannan tambayoyin babu wanda ya amsa sai murza ido da yake ta faman yi yana son yin kuka,kasa da murya Khalil yayi yace,

“To albishirinka lovely son…. Gobe zata zama rana ta musamman agareka…. Ai kasan babu school gobe ko? Gobe zanyi surprising dinka da wani abu,maza jeka ka kaiwa umma wayar..”

Tashi Aryan yayi da gudu yana murna yahau sama nan Hanan tabishi da kallo, dakinshi dake sama yashiga wanda sam Hanan bata ma san dashi ba can ya iske umma tagama gyara masa dakin tana karasa shirya masa kayansa cikin drawer,wayar yabata yana ta murna,

Bayan umma tagaisa da Khalil cikin damuwa Khalil din yace mata, “Umma ni kwana biyun nan haka haka nake ganin yaron nan babu walwala kamar yana cikin damuwa ko baida lafiya ne?”

“A’a lafiyar shi kalau wallahi kuma babu abinda ke damunshi kai dai ka saki ranka ka kwantar da hankalinka wuri daya”

Bazaiyi musu da umma ba shiyasa yayi shiru amma ko jiya fa da yaga yaron da daddare saida jikinsa yabashi cewa kuka yayi yau kuma gashi yaganshi yazama wani soo silent kamar wanda aka takure wuri daya, sallama sukayi umma ta mikawa Aryan wayar suka ci gaba da magana da tsohonshi Khalil sai janshi yake da hira tun bai sake ba har yasake yafara nuna masa dakinshi da umma tagama gyara masa yana ta murna yana cewa Khalil dakinshi na yanzu yafi na tsohon gida kyau ahaka Hanan ta shigo ta samesu saboda taji shirun yayi yawa kuma agabanta Aryan ya iyo sama da gudu shine da taji shiru tabiyo bayanshi, kasancewar yabar kofar dakin abude shiyasa tagane inda ya shiga,koda ta shigo cikin dakin sakin baki tayi kawai ta tsaya cak tana kallon ikon Allah domin abinda idanuwanta suka gane mata yayi bala’in bata mamaki…………………鉁嶏笍

*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎

8/14/20, 10:08 AM – Ummi Tandama: *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.*

*16*

      ***Sakin baki kawai Hanan tayi tana kallon irin uwar dukiyar da aka narkar wurin shiryawa Aryan dakinsa,dakin ya hadu ne yasha furnitures masu tsada da burgewa irin yanda ake shirya dakunan yara akasar turai ko India,

Wani dan karamin gado ne hadadde pink & purple colour da drawers dinsa sai mirrior wanda aka daurashi a jikin bango gashi gaba daya bangon dakin an zaneshi da zanen su butterfly da sauran zane na daukar hankalin yara da kaloli daban daban har da wurin karatunshi acan gefe ansaka table da yar karamar kujera kai dakin dai yagama haduwa karshe,

Tsabar mamaki kasa magana tayi sai faman bin ko ina na cikin dakin take yi da kallo yayinda ita kuma umma barira ke kokarin karasa shirya masa takalmansa saman shoe rack,

“Masha Allah Aryan wannan dakin naka na yanzu yafi na tsohon gida kyau ko?” Umma ta tambayeshi cikin tsokana,yana rike da wayarshi yaturo baki,

“Uhm uhmm ni nafi son wancan”

“To basai kaje ka koma ba dan nema,ni katashi ma inshiryaka maza malamin islamiyya zaizo yanzu kar yazo baka shirya ba…”

Ita dai hanan wuri tasamu ta zauna tana kallon wannan ikon Allah yaro karami amma dan daurewa karya kugu shine harda wani dakinsa kuma dakin ma ba ashiryashi da wasa ba dagaske aka shiryashi domin anci mutuncin naira dagaske ba kadan ba. Agabanta umma ta buda drawer din kayan shi domin ciro masa kayan da zata saka masa,kayane iya ganinka wani kayanma wannan sai yafi shekara bai maimaita shi ba saboda tsabar yawansu dan hatta uniform din makarantarshi gashi nan yafi set goma,gaskiya yaron nan dan gata ne na ajin karshe ubanshi naji dashi kuma yana nuna masa tsantsar so shi ko tunanin gaba ma bayayi?

Tabe baki tayi ta tashi tafita bayan ta fadawa umma dama sawun Aryan din tabiyo da taji shiru bai koma ba, k’asa ta sauka ta hau kan table domin cin abinci, spaghetti and cheese bagels taga ni sai egusi soup and eba ga kuma jalop rice with jerk chicken salad, sannan ga goat meat pepe soup,

Eba din ta zuba da miyar egusi tasoma ci tana yi tana hadawa da juice mai sanyi,gefe daya kuma tana mamakin yadda akayi wannan kukun ya iya girki har haka sai kace yaje catering school dan ko mace bazata nuna masa kwarewa wurin girki ba,tun kafin ta kalli wurin tasan sun sauko domin tana jiyo karadinsa da karar takalminsa, gaskiya umma barira na da hakuri dan wannan Aryan din dan rigima ne,

Su dinma kan dining din suka hau umma nata rigima dashi akan sai yaci abinci saboda baya son cin abinci dan wani lokacin ma lunch box dinshi yanda yatafi dashi school haka zai dawo dashi bai ko buda ba,

Tana jin umma nata lallaminsa har aka samu yaci eba ta hada masa da karamin juice na kwali sannan yafita domin tuni malaminsa yazo yana can yana jiransa. Ita dai tana son tayiwa umma barira magana akan Aryan amma kuma bata san ta inda yadace tafara ba domin irin wannan wani lokacin kai zakayi magana da zuciya daya kuma gaskiya zaka fada amma sai aga kamar da biyu ka fada saboda ba kai ka haifi yaroba shiyasa ma kawai taja bakinta tayi shiru suka yi wata hirar ba wannan ba,

Suna zaune cikin falo bayan sun gama cin abinci nura PA yashigo dauke da kayan wasan Aryan wanda yabaro a tsohon gida wai Aryan dinne yace akawo masa kayansa shine fa akaje aka debosu cikin mota Hilux guda ahakan ma ba duka ya debo ba yabar wasu acan,

Daki guda taga anbude anan k’asa kusa da na umma barira ciki nura keta kai kayan ashe dama akwai wasu aciki kiriga guda sababbi babu abinda babu,motoci ne,babur,jirgi,bindiga,duk na roba gasu nan jingim kamar dakin wasan yara,ganin haka sai ta kara shan jinin jikinta akan lamarin daga karshe ma tashi tayi takoma sama bata san lokacin da aka gama shigowa da kayanba. 

Washe gari bayan tafito da safe misalin karfe 11 iya umma kadai tasamu kishingide cikin d’akinta tana jan charbi,shiga tayi suka gaisa sannan umman ta kara da cewa,

“Nima yanzun nan nashigo ai mutumin na raka yashiga mota babanshi ya iyo waya tunda asuba wai ashirya shi za akaishi wurin faretin yara yana son gani wai yau babu makaranta ranar yarace….”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button