MIJIN MATACCIYA Page 11 to 20

“Allah sarki shi faretin yake so? Ko harda shi a masu yi?”
“A’a gani kawai zaije yayi ai uban yahana shi yi da harda shi ake zaba sai uban yace bazai yiba kin san hutsu ne wani lokacin…”
“Ai kuwa dai naga alama” Ta fada acikin zuciyarta amma afili sai tace,
“To Allah yadawo dashi lafiya,bari naje inyi breakfast nima fitowata kenan”
Fita tayi ta hau kan dining domin karyawa,to ko mujahid yasake layi ne dan ko dazu sai da ta kirashi amma wayarshi akashe kamar koda yaushe,tsaki tayi taci gaba da cin abincinta tana jin duk zaman gidan har yafara isarta tun ba aje ko inaba,to zamane wuri daya kuma gashi babu abinda zakayi sai dai kaci kasha ka kwanta daga nan babu wani motsi da zaka yi,ita wallahi son fita ma take yi ta dan ga gari,
A kasalance ta koma sama ta kwanta a falonta wayarta ta dauka ta siyi data wai ko zata dan rage zafi domin ta gaji da zaman shirun nan wai ahakanma dan da su umma, group dinsu na WhatsApp ta duba wato Abuja Kopa kamar yadda sunan group din yake wai ashe anfara clearance tun jiya amma bata saniba kuma babu wanda yafada mata,dan tsaki tayi ta mike tana tunanin ko a ina kakinta ma yake oho dan bata san duniyar da yashiga ba,bata san ta inda yadace tafara nemanshi ba,
Bedroom tashiga tafara dubashi amma sai dakyar ta ganshi duk ya yi squeezing yanzu dole sai angogeshi,fita tayi wurin umma tana tambayar ta a ina zata samu ta dan goge kayanta? Nan umma ta karba tace idan PA yazo zata bashi sai yabawa mai wanki idan angoge za akawo mata, godiya ta yiwa umma sannan ta juya tasake komawa inda ta fito.
K’arfe 2 da kusan rabi na rana su Aryan suka shigo shida PA yana kan kafadar PA ya daukoshi kamar wani yaron goye,zuwa yayi ya haye kan umma barira bayan nura ya saukeshi shikuma yafita,
“Dan albarka andawo? Me ka kawo min?” Inji umma,
“Kayan dadi…”
Shigowar nura ta katse musu hirar da suke yi wanda ke rike da kaya niki niki na kwalam da makulashe cikin manya manyan ledoji masu dauke da tambarin ihsan confectionery,
Uniform din Hanan umma tabaiwa PA yabawa mai wanki ya wanke mata ya goge sai yahado da kayan Aryan ya kawo, nura na shirin fita Hanan ta sauko lokacin umma nata tiriniyar bubbude kayan da PA yashigo dasu,vanilla ice cream ne manya manya sai chocolate suma manya manya da sauran tarkacen kayan ciye ciye da su snacks,fada umma tafara yi tana cewa Aryan,
“Kai ja’iri ba babanka ya hanaka shan wadannan kayan sanyi da zakin ba? Shine shikuma nura ya biyewa son ranka yasiyo maka ko?”
“Umma Papa ne yace asiya min shima yakusa dawowa”
“Karya kake Khalil bazai ce asiya maka wannan kayan zakinba”
Ai jin umma ta ambaci Khalil sai yafara kuka wai danme zata fadi sunan babansa sai dai itama tace Daddy ko Papa,dariya umma tayi ta soma rarrashinsa tana cewa,
“To ai nikuma ba babana bane ba akanme zance masa baba?”
“Babanki ne…”
“To naji baba nane nima shikenan?”
Hanan kallonsu take yi kawai amma acan kasan ranta ji take yi kamar taje ta kwada masa mari saboda b’acin yaron da sangartarshi yayi yawa yanzu meye abin kuka anan daga magana dan anfadi sunan Khalil? Wallahi ba dan tana jin kunyar umma barira ba da sakashi zatayi agaba ta yita fadin sunan uban nashi inyaso yayi kukan jini. Wadannan kayan da yazo dasu su yasha yaki cin abinci umma sai kyaleshi tayi,malamin islamiyyarshi ma da yazo kin fita yayi nanma umman tayita binsa amma yaki harda yimasa barazanar zata fadawa abbansa amma abin mamaki da Khalil din yakira waya umma tana cemasa,
“Ka ganshi nan tunda yadawo daga wannan cindirin de din yaki dadi sai rigima yaketa yi yaki yaci abinci sannan ga malaminsa can yana jira shima yaki zuwa”
Murmushi Khalil din yayi yace da umma,
“Umma children’s day fa ake cewa,tunda baya son zuwa karatun yau akyaleshi gobe sai yaje nima insha Allah yau da tsakar dare zan dawo yanzu haka ma ina dan shisshirya kayana da nazo dasu ne”
“Ai kuwa Aryan yafada nazaci ko shirmensa ne,to Allah yadawo daku lafiya”
“Amin umma nagode, bawa Aryan din”
Duk abubuwan da ake yi Hanan dake can karamin falo tana jiyowa amma iya maganar umma kadai take ji, da alama dai shi yake bata yaronshi da kanshi ba umma ba dan umma na iya bakin kokarin ta akan Aryan. Tabe baki tayi aranta tana cewa sudai suka sani ita kam yar kallo ce.
***
Misalin karfe 3 nadare agogon Nigeria suka sauka afilin tashi da saukar jirage na Nmandi azikiwe international airport dake garin Abuja,kai tsaye tsohon gidanshi yawuce domin shi komai nasa yana can bai dauke ko tsinkenshi zuwa sabon gida ba kuma bai san ranar komawa ba tunda aganinsa mai zaije yayi agidan alhali ba Ramlat ce aciki ba,
Wanka kadai yayi da ruwan dumi sannan yazura farar jallabiya tas yafita yana rike da wani dan karamin akwatin adana zobe amma daga gani kasan yashaki kudi,
Kasancewar ya danci abinci acikin jirgi baya jin yunwa dan haka yashiga mota suka nufi sabon gidanshi dan bazai iya hakuri baiga Aryan ba har gari yawaye,
Nura na gaba yana yimasa jagora har cikin gidan,gidan yayi masa yadda yake so kuma anshirya shi yanda yabada umarni babu ta inda aka kuskure,dakin Aryan yabude yashiga ganinsa yayi yana kwance yana bacci amma ba kamar yadda ya saba ganinsa ba yau sai yaga yaron ya danyi masa wani iri,sumbatar goshinsa yayi da kumatunsa sannan yashafi kansa,akwatin zoben dake hannunsa yabude yaciro wani dan karamin zoben azurfa mai kyawun gaske dan har kana iya hango haskenshi acikin duhun tsabar shekin da yake yi,kama hannunshi na hagu yayi yasaka masa zoben wanda ke dauke da wani farin stone wanda yakara masa kyau da kwarjini,koda yaushe yana ta son yasiyo masa sakamakon wanda ke yatsan Aryan din tun yana jariri tuni yayi masa kadan yacire masa shi to bai samu wanda yayi masa bane sai wannan lokacin,
Tashi yayi ya dan zazzaga yaga yanda dakin Aryan din yake sannan yafita yaja masa kofar bayan ya lullube shi da bargonshi mai tsananin laushi,
Bai sake shiga ko inaba yafita yakoma mota suka bar gidan yanufi tsohon gidansa, kwanciya ya danyi ko zai dan samu bacci kafin asubah ta karasa domin da safe yana da tafiya zaije jihar katsina.
Da safe bayan yashirya yana kokarin saka farin takalminsa sau ciki sakon Hanan yashigo da kamar bazai bi takai ba sai kuma ya duba bayan yagama saka takalmin,
_Zanje clearance NYSC sectariat._
_Ok._
Yatura mata kawai yadauki hularshi yafita yanufi office.
***
Tunda taga reply dinshi taji ranta yabaci, karasa shiryawa tayi tasaka uniform dinta tafito sanye da milk colour din hijabi,
Bata samu kowa ba sai kayan breakfast jere saman table,taosted bread taci da ruwan tea sannan tashiga dakin umma barira wacce ke kwance bayan tagama shirya Aryan yatafi school gaisawa suka yi sannan tacewa umma zataje clearance tadawo ba jimawa zatayi ba,
“To sai kin dawo,ashe mai gidan shima yadawo daren jiya ko… Ai sai dazu Aryan ke nuna min zoben da yazo masa dashi kuma shine kamar gari bazai waye ba aka kasa hakurin bari sai yau… Tunda yadawo nima wajen gobe zanje ingano gida in danyi kwana biyu sai indawo”
Shiru Hanan tayi saboda ita bata san cewa wai minister yadawo ba au ashema yana garin take wani tura masa text massage,dan murmushi ta kakalo tayi sannan tace da umma,