MIJIN MATACCIYA 1-END

MIJIN MATACCIYA Page 11 to 20

“Umma menene kuma na zuwa gida dan kawai yadawo,dan Allah karki tafi ki zauna muyi zamanmu”

“A’a wallahi ai idan naje can dinma ba dadewa zanyi ba,kwana biyu kurum zanyi indawo”

“To ai shikenan umma,bari naje nadawo”

Fita tayi nan suka yi kicibus da PA wai oga ne yaturoshi tafito yakaita unguwar, batace komai ba tabishi harabar gidan mai dauke da sassa daban daban gaskiya gidan nan katone ga haduwa da yayi securities kuwa abakin gate kamar gidan wani shugaban k’asa sai yau ta taba fitowa shiyasa ta kame a owners corner tana kallon unguwar tasu har suka je bright future ta karbi clearance form daga nan yakaita NYSC sectariate tayi thumbprint sannan ya maido da ita gida sai lokacin yake fada mata wai oga na can office yana jiransu da zarar yakoma zasu tafi unguwa ita dai bata ce komai ba ta bude kofa ta fita.

 Kamar yadda umma barira ta fada haka ta matsa sai ta tafi gida wai tayi kwana biyu kun san iyayenmu akwai kara da alkunya ita gani take zata shiga hakkinsu ta takura musu tunda amarci zasuyi,shi kansa Khalil din baya nan tunda yadawo daga Spain sau daya suka hadu sai driver yatura mata da mota yaje ya dauketa suka nufi gombe lokacin Aryan yatafi makaranta,

Koda yadawo daga makaranta baiga umma barira ba kuka yafara yi gidan shiru babu wanda yasan ma yanayi haka Hanan ta sauko ta sameshi kallonsa kadai tayi yaron yashiga taitayinsa jikinsa duk yafara rawa,da kansa ta turashi yaje ya cire uniform dinshi sannan ta tayi masa wanka,wani irin mugun tsoronta yaron yake ji domin baiga fuska ba ko abinci tana zuba masa ya dauka yafara ci duk yau babu wannan shagwabar da surutun da yasaba yiwa umma barira da kuwa ummance da sai sunyi daga da ita kafin ya yarda yaci abincin,

Gaba daya Aryan ya takura yazama marayan gaske kalar tausayi,malamin islamiyyarshi na zuwa yatafi yau babu game babu wasa babu kallon carton,sam Hanan bata wasa dashi,washe gari ita tatashi tayi masa shirin makaranta yatafi kuma babansa bai samu zuwa ganinsa ba ranar yadai kirashi awaya,

Cikin kwanaki biyu kacal Aryan yazama abun tausayi aranar da daddare misalin karfe 2 nadare Khalil yashiga gidan dawowarsa kenan daga gombe yaje ya dubo hajiyarsa,gani yayi Aryan duk ya sauya dan ko dazu awaya yayi mamakin yanda yaga yaron ya zama wani silent kamar bashi ba, Aryan ba irin yaran nanne masu kunci ba amma cikin yan kwanakin nan yafara zama haka shiyasa abin ke taba zuciyar Khalil,a lokacin bai tashe shi ba amma yadau alwashin sai ya tambayi yaron abinda ke damunshi,tashi yayi yafita yayi tafiyarsa tsohon gida.

Washe gari bayan antashi daga school office yasa aka kawo masa Aryan ba akaishi gida ba,

Tare ya zuba musu abincin da PA ya karbo musu daga gida saboda Aryan,daukar shi yayi yadora saman cinyarshi suna facing juna gani yayi da alama yauma Aryan yayi kuka,cikin damuwa ya dan girgizashi,

“Abba na meke damunka? Andukeka a makaranta ne?”

Girgiza kai Aryan yayi kamar zaiyi kuka dan har yafara murza ido da hannunshi,

“To meke damunka? Maza fada min,kaida na kawo maka mommy gida,ko baka farin ciki da zuwanta?”

Daga kai yayi alamun ehh tun daga nan Khalil yasa alamar tambaya jikinsa yabashi akwai wani abu dake faruwa……………鉁嶏笍

Share this

[ad_2]

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button