MIJIN MATACCIYA Page 11 to 20

Tunda Hanan taga wannan sakon nasa bacin ranta yasake nunkuwa zuciyarta har tafarfasa take yi dan bacin rai,wai ita zai cewa saboda ta rike masa yaro zai aureta,mai neman kuka ne aka jefeshi da kashin awaki nan tasoma kokarin mayar masa da reply dama haushinsa takeji saboda girman kansa da wulakancinsa dan ko sako ne sakonshi baya wuce layi biyu,
_Nima ai ba sonka nakeba kuma da kake maganar zaka aureni saboda in rike maka yaro to ni ba yar aiki bace kuma ba baiwa bace tun wuri ka nemi mai rike maka yaronka._
Wannan karon sakon nata ya bata masa rai fiye da wancan,wai wannan yarinyar dame take tak’ama da har take fada masa maganganu kanta tsaye ko tsoro bata ji kamar wata sa’arshi,dan kawai yace zai aureta sai aka fada mata sonta yake? Shi yanzu aduniya ai babu yarinyar da zata ja hankalinsa har ya sota,tsaki yayi ya ajiye wayar agefe yatashi ya shiga bathroom……………..鉁?
*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎
8/14/20, 10:07 AM – Ummi Tandama: 漏锔? *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
_(Home of expert & perfect writers)_
*D’AND’ANO….*
*MIJIN MATACCIYA…..*馃挒馃挒
*_NA_*
*_UMMI A’ISHA_*
*Wattpad-ummishatu*
*10*
***Kamar ya rabu da ita dan har ya shimfida Rug din salla yaji bazai iya kyaleta ba duk da yasan ko tantama baya yi a haihuwar kaji ya haifeta amma gara dai ya nuna mata ita ba kowan kowa bace agareshi. Sai bayan da yagama da ita sannan yaje ya tada kabbarar sallar da yayi haramar yi,
Har lokacin ita kam bata jin ta huce wani irin zafinsa take ji kamar taje har inda yake ta shakeshi saboda yashiga hakkinta da yawa,tana tsaka da sharar hawaye taji shigowar wani sakon wanda ko tantama batayi daga gareshi ne,yanzu kuma Allah ne kadai yasan irin bakar maganar da yaturo mata tunda ta lura shima dan zafin kaine bai da hakuri kamar ba babban mutum ba,
K’wafa tayi sannan cikin bacin rai tace “Ai wallahi idan tsoho baiji kunyar hawa jakiba to kuwa jaki bazai ji kunyar yin totso dashi har ya damfara shi da kasa ba,duk abinda zaka fada am too much ready in baka amsa daidai da maganar ka…”
Text massage din nashi ta bude nan ta soma karantawa afili,
_Ki dauki kanki bakida maraba da mai rainon yarona, sannan ina son infada miki akwai dokoki da sharruda masu yawa wadanda zan kafa miki akan yarona mutukar kika bisu zamu zauna lafiya amma karya doka daya daidai take da rugujewar dukkan dokokin da kika bi,idan har kina son aji kanmu dake to ki gwada saka kafa ki shure daya daga cikin dokokin._
Ranta idan yayi dubu to ya baci saboda wannan sakon da yaturo mata,ai kuwa wallahi sai dai ayi wacce za ayi amma ita ba yar raino bace,
Kiris dama take jira shiyasa ganin wannan sakon nasa yabata damar amayar da abinda ke nukurkusar zuciyarta,
Ko bayan da ta tura masa sakon ji take bata huce ba daga cin mutuncin da yayi mata gashi yana yin komai nasa isa isa iko iko,tasan dan girma kam ya girme mata nesa ba kusa ba to amma Menene zai rinka nuna mata gadara harda wani cewa a yar aiki ya dauketa kamar wata baiwar da yasaka kudi yasiyo a kasuwa zai tsaya yana fadin wai zai kafa mata dokoki da sharruda,
Sakon mujahid ne yashigo mata cikin wayarta adaidai wannan lokaci,ji tayi tausayinsu shida ita duk ya mamaye ilahirin zuciyarta baki daya saboda tasan yanda batayi bacci ba shi dinma gashi can kwance bai samu baccin ba duk kawai dan mutum daya,gaskiya saima Allah ya saka musu ita da mujahid,duk tsawon shekarun da suka dauka suna shirya yanda rayuwarsu zata kasance idan sunyi aure yau kwatsam rana daya wani tsohon banza can mai budurwar zuciya yazo ya rusa musu mafarkin su da suka dade suna yi,
Bude sakon tayi tana kuka kamar wata mai arahar hawaye,
_Dan Allah wify karki cigaba da wannan fushin dani,ki tsaya ki saurare ni,sanin kankine ina mutukar sonki kuma wallahi har na mutu da sonki dankare cikin zuciya ta zan koma ga mahaliccina,dan Allah ki daina fushi dani kijira kiga irin matakin da zan dauka._
Sai lokacin taji ta dan samu nutsuwa jin mujahid yace akwai abinda yake shiryawa, sauke ajiyar zuciya mai nauyin gaske tayi sannan tasoma kiran wayar mujahid din,ada kam ji take bata wani damu dashi ba amma ahalin yanzu tana jin soyayyar sa kamar idan babushi aduniya bazata iya rayuwa ba,ita kanta bata san yaushe wannan soyayyar ta shigeta ba sai yanzu, bata san yaushe tafara son mujahid har haka ba a iya saninta dai sai da aka fara turka turkar auren nan sannan wannan matsananciyar soyayyar tasoma tasiri agareta.
Bugu uku taji ya katse kiran sannan ya kirata,dauka tayi tai kasa da dasasshiyar muryarta wacce ke fita dakyar kamar wacce mura taci karfinta,
“Wify meyasa baki tsaya kinji uzuri na ba,meyasa kika dauki fushi dani har haka? Kema kin san ai ina sonki,u know how much you mean to me and i soo much loves you….”
“To ai dafarko dinne sai naga kamar baka damu da rabamun da za ayi ba shiyasa,naga kamar ni daya keta haukana you didn’t make any effort…”
“No wify,ba haka bane,gashi kina gani nakasa bacci…,akwai abinda nake shiryawa, kawai all what i want from you is ki kwantar da hankalinki ki daina damuwa kima daina nuna kwata kwata cewa kina cikin damuwa,nikuma ina can bayan fage ina shirya abinda nake shiryawa…”
Dan murmushi tayi mai dauke da jin dadi sannan cikin sanyin murya tace,
“Ok har naji relief wallahi,gobe insha Allah zan koma Abuja saboda ban dauki excuse ba nataho dama kawai nataho weekend ne fa”
“Babu matsala zamu hadu before kitafi,yanzu ki kwanta kiyi bacci kinga 2 ta kusa”
Sallama sukayi ta katse wayar tana jin farin ciki yana ziyartar birnin zuciyarta,haba har taji sanyi aranta.
***
Kamar kada ya bude sakon nata amma sai ya dake yabude aransa yana fadin “wannan yarinyar bata da kunya sam”
Yana budewa yaga tace,
_Girma dai ya fadi kasa wanwas masu budurwar zuciya._
Tsaki kawai yaja ya kashe wayarsa yayi kwanciyar sa bisa luntsumemen gadonshi mai azabar laushi,shi idan ta barshi da abinda ya dameshi ma ya isheshi bawai sai ta kara masa da tata matsalar ba domin shekara da shekaru acikin matsala da damuwa yake kawai yana daurewa ne amma acan kasan ransa babu kwanciyar hankali ko jin dadi atare dashi,
Bai kara bi ta kanta ba domin aganinsa ai ita ba sa’ar kace nace dinsa bace,nawa take da har zai zauna yana haka da ita? Ai ubanta shi shine abokin yinsa bawai itaba kuma duk ranar da ta kara yunkurin yimasa rashin kunya zai fada mata ubanta shine daidai shi bawai ita ba. Washe gari kamar yadda yasaba 9 yabar gida ya nufi kaduna saboda yana da wani muhimmin taro da zai halarta sannan kuma aranar yana son zuwa gombe zaije ya duba jikin hajiya haka kuma zai ga kayan aurenshi da aka gama hadawa cikin kwanaki kadan,
Wurin lokacin sallar la’asar yabar kaduna suka tasamma gombe wanda basu suka isa garin ba sai bayan magriba,
Saida suka fara yin salla a masallaci sannan yashiga cikin gidan,akwatuna ne gasu nan set biyu a falon hajiya Zaitun hadaddu dasu masu tsada kowanne damfare da kaya dan ko rufuwa ma basayi saboda tsabar cika,
Wuri yasamu ya zauna kansa babu hula suna gaisawa da hajiya wacce ke kishingide saman kujera.
“Mu’azzam dama kayanne nake son kazo ka gani kafin aje akai musu kasan abubuwan nakune duk cikin gaggawa kuka yisu kun debi lokacin auren kadan amma hakanma yayi daidai gara ayi ayi kawai…”